Tarihi
“A Cikin Hannun Damanka Akwai Jiyejiyen Daɗi Har Abada”
Lois Didur ce ta ba da labarin
Sau nawa ne ka taɓa cewa, ‘Da ma na sani, da ban yi wannan zaɓin ba’? Amma, bayan shekara 50 da na yi a hidima ta cikakken lokaci, ba zan iya tunawa da wani sakamako marar kyau da na samu don kasancewa a hannun dama na Jehobah ba. Bari na bayyana.
AN HAIFE ni a shekara ta 1939 kuma na yi girma a karkarar Saskatchewan, a ƙasar Kanada. Ina da ’yan’uwa mata huɗu da ƙane guda. Rayuwa tana da daɗi sosai a wannan gonar. Akwai wata rana da Shaidun Jehobah suka zo wa mahaifina wa’azi, sai na tambaye su ko Allah yana da suna. Suka nuna mana sunan nan Jehobah a littafin Zabura 83:18. Hakan ya sa na nemi ƙarin bayani game da Allah da kuma Kalmarsa.
A wannan zamanin, makarantu ba su da ƙananan azuzuwa, amma babban ɗaki guda ne. Kuma yara suna kasancewa a cikin wannan babban ɗakin daga aji ɗaya na firamare zuwa aji uku a sakandare. Suna hawan doki ko kuma su taka a ƙas na tsawon miloli da yawa zuwa makaranta. Malaman makarantar suna zama a gidan iyayen waɗannan yaran kuma su ne suke kula da su. Akwai wata shekara da iyaye na suka ɗauki hakkin kula da sabon malaminmu mai suna, John Didur.
Ban sani ba cewa shi ma yana son Kalmar Allah sosai ba. Akwai wata rana da nake goyon bayan mulkin kama karya da gurguzanci wanda mahaifi na yake ciki a lokacin. Sai John ya ce: “Babu kowanne ɗan Adam da yake da ikon ya mulki wani ɗan Adam. Allah ne kaɗai yake da wannan ikon.” Hakan ya sa muka tattauna abubuwa da yawa.
Da yake an haifi John a shekara ta 1931, an ba shi labari game da wahalar da ake sha a lokacin yaƙi. Sa’ad da aka soma Yaƙi a Ƙasar Koriya a shekara ta 1950, ya tambayi limamai dalilin da ya sa suke saka hannu a yaƙin. Dukansu suka ce ya dace Kiristoci su yi yaƙi. Daga baya, ya yi wa Shaidun Jehobah wannan tambayar. Suka nuna masa shawarar da ke Nassi na kada a yi yaƙi da Kiristoci na ƙarni na farko suka bi. John ya yi baftisma a shekara ta 1955. Ni ma na yi hakan a shekara ta 1956. Dukanmu mun san cewa muna son mu bauta wa Jehobah da dukan ranmu. (Zab. 37:3, 4) Ni da John mun yi aure a watan Yuli na shekara ta 1957.
Tun da yake mun yi aure a watan Yuli, ranar tuna aurenmu takan faɗa a watan da muke taron gunduma. Muna farin cikin kasancewa tare da dubban mutanen da suke daraja aure. Taron gunduma na ƙasashe na farko da muka halarta shi ne wanda aka yi a shekara ta 1958. Mu biyar muna shiga mota zuwa birnin New York daga Saskatchewan. Mun yi tuƙi na tsawon mako guda kuma muna yin barci daddare a cikin tanti. Mun yi mamaki sosai sa’ad da wani ɗan’uwa da muka haɗu da shi a birnin Bethlehem, da ke Pennsylvania, ya gayyace mu mu zauna dare ɗaya tare da iyalinsa. Wannan kirkin da ya yi mana ya sa muna isa birnin New York tsab-tsab. Wannan taron gunduma da mutane da yawa suka halarta ya sa mu ga muhimmancin bauta wa Jehobah. Kamar yadda marubucin zabura ya ce, “a cikin hannun damanka akwai jiyejiyen daɗi har abada.”—Zab. 16:11.
HIDIMAR MAJAGABA
Bayan shekara ɗaya, wato, a shekara ta 1959, muka soma hidima ta cikakken lokaci kuma muna zama a wani gidan da aka yi da bodin tirela a tudun Saskatchewan. Za ka iya hangen nesa daga tudun, kuma duk wuraren, yankin da muke wa’azi ne.
Wata rana an aika mana wasiƙa da ta sa mu farin ciki sosai. Na gaggauta zuwa inda maigidana yake gyaran motar tarakta. A cikin wasiƙar, an ce mu zama majagaba na musamman a garin Red Lake, a lardin Ontario. Da yake ba mu san wurin ba, sai muka duba taswirarmu.
Wannan wurin ya yi dabam da wannan gonar da muke zama. A yanzu za mu zauna a cikin babban daji mai ƙananan garurrukan da aka gina kusa a wurin da ake haƙa zinari. A rana ta farko da muke neman masauki, wata ƙaramar yarinya ta ji muna tattaunawa da maƙwabcinsu. Sai ta koma gida a guje ta gaya wa mahaifiyarta, kuma ta amince mu kwana a gidanta daddaren. Gadon yana cikin ɗakin da ake zuba shara a dā. Washegari muka samu gidan mai ɗakuna biyu da aka gina da katako. Gidan bai da ruwan famfo da kayan ɗaki, sai dai wani ƙaramin wuri na ɗumama ɗaki. Muka sayo wasu kayan gwanjo kuma mun gamsu da hakan.
Nisan ikilisiya daga inda muke zama mil 130 ne. Mutane da yawa da suke aiki a wannan wurin haƙa zinari sun fito ne daga ƙasar Turai, kuma sun ce mu kawo musu Littafi Mai Tsarki a nasu yare. Ba da daɗewa ba, muna nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane 30. A cikin watanni shida, aka kafa wata ƙaramar ikilisiya.
Mijin wata mata da muke nazari da ita ya kira firist ya zo ya hana matarsa nazarin. Sa’ad da firist ɗin ya zo, ya ce mu riƙa koya wa mutane game da Allah-Uku-Cikin-Ɗaya da kuma sauransu. Matar ta fito da Littafi Mai Tsarki na Katolika, kuma ta ce ya nuna mata ayoyin da dukan abubuwan da yake faɗa suke. Ya wurgar da Littafi Mai Tsarkin a kan teburi, kuma ya ce ba ya bukatar ya bayyana mata kome. Sa’ad da yake fita daga gidan, ya faɗa da yaren ƙasar Ukraine cewa a kore mu daga gidan kuma kada a sake barinmu mu dawo. Bai san cewa John yana jin yaren ƙasar Ukraine ba.
Ba da daɗewa ba bayan hakan, muka bar birnin Red Lake domin ana son a koya wa maigidana aikin masu kula masu ziyara. Kusan shekara guda bayan wannan lokacin, maigidana ya ba da jawabin baftisma a wani taron gunduma, kuma maigidan wannan matar da na yi nazari da ita yana cikin waɗanda suka yi baftisma a ranar. Abin da ya faru tsakanin su da wannan firist ya sa ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki.
MUN SHAGALA A HIDIMAR KULA DA DA’IRA
Sa’ad da muke hidimar kula da da’ira, mun samu gatan kasancewa tare da iyalai dabam-dabam. Mun zama abokan waɗanda suka kula da mu. Akwai wata rana a lokacin dari da muka sauka a wani gidan bene da ba shi da wurin ɗumama ɗaki. Muna jin sa’ad da wannan ’yar’uwa tsohuwa take shigo cikin ɗakinmu da sassafe don ta kunna mana rasho. Ba da daɗewa ba, sai ta shigo da baho da kuma ruwan zafi domin mu yi wanka da shi. Na koyi halaye masu kyau daga wajenta.
Hidimar kula da kuma ziyara ta taimaka mini na kusaci Jehobah. Akwai wata ’yar’uwa da take zama ita kaɗai a wani yanki a Alberta da ake haƙan ma’adinai da ke Arewancin ƙasar Kanada. Yaya ƙungiyar Jehobah take ɗaukan wannan ’yar’uwar? Muna hawan jirgin sama zuwa wurin bayan kowanne wata shida, don mu yi taro tare da ita da kuma wa’azi daidai yadda ake yi da babban ikilisiya. Wannan ya nuna yadda Jehobah yake kula da kowanne tumakinsa.
Muna rubuta wasiƙa wa ’yan’uwa da yawa da muka zauna tare da su. Hakan ya sa na tuna da kyauta na farko da maigidana ya ba ni. Wannan wani akwati ne cike takarda. Muna jin daɗin rubuta wa abokanmu wasiƙu da waɗannan takardun. Har yanzu, ina daraja wannan akwatin.
Sa’ad da muke hidimar kula da da’ira a birnin Toronto, wani ɗan’uwa ya kira mu daga Bethel da ke ƙasar Kanada, kuma ya ce ko za mu so mu yi hidima a Bethel. Kuma yana son mu ba shi amsa washegari. Kuma washegari, muka amince da gayyatar.
HIDIMA A BETHEL
Kowanne canjin da muka samu a hidimarmu ya nuna mana ɓangarori dabam-dabam na jiyejiyen da ake samu daga hannun damar Jehobah. Hakan ya ci gaba sa’ad da muka ƙaura zuwa Bethel a shekara ta 1977. Yin cuɗanya da wasu Kiristoci shafaffu ya ba mu zarafin ganin halayensu dabam-dabam da kuma yadda suke daraja Kalmar Allah sosai.
Mun ji daɗin sabuwar hidimarmu a Bethel. Alal misali, mun soma saka tufafinmu a cikin kabat maimakon a cikin akwatin da muke tafiye-tafiye da shi. Kuma muna ikilisiya ɗaya maimakon dabam-dabam kowanne mako. Ban da aikin da nake yi, zagayawa da baƙi a Bethel yana sa ni farin ciki sosai. Ina bayyana musu irin aikin da ake yi a Bethel, na ji kalamansu kuma ina amsa tambayoyinsu.
A shekara ta 1997, aka gayyaci John ya halarci Makarantar Koyar da Kwamitocin Reshe a Patterson, birnin New York. Bayan hakan, aka tambaye mu ko za mu so mu ƙaura zuwa ƙasar Ukraine. An ƙarfafa mu mu yi tunani da kuma addu’a a kan batun sosai. Da yamma muka amince cewa za mu je wurin.
AN TURA MU ZUWA ƘASAR UKRAINE
Mun halarci taron ƙasashe a birnin St. Petersburg, a ƙasar Rasha, a shekara ta 1992 da kuma a birnin Kiev a ƙasar Ukraine, a shekara ta 1993. Hakan ya sa mu ƙaunaci ’yan’uwanmu da ke Gabashin Turai sosai. Masaukin da a ka ba mu a birnin Lviv, a ƙasar Ukraine yana kan hawa ta biyu a wani tsohon bene. Tagar ɗakin ya fuskanci wani lambu da ake kiwon kaji. Hakan ya sa mu ji kamar muna gonarmu ta dā a lardin Sasketchewan. Mu goma sha biyu ne muke zama a gidan. Muna hawan mota da sassafe zuwa aiki a Bethel.
Yaya muka ji game da yin hidima a ƙasar Ukraine? Kasancewa tare da ’yan’uwa da yawa da suka fuskanci gwaje-gwaje da hani, kuma suka kasance cikin fursuna ya sa mu tawali’u sosai. Amma duk da haka, suna da bangaskiya sosai. Sa’ad da muka ƙarfafa su, suna cewa, “Mun yi hakan ne saboda Jehobah.” Ba su taɓa jin cewa Jehobah ya ƙyale su ba. Har wa yau, idan ka yi wa wani godiya domin alherin da ya yi, zai ce maka, “Mun gode wa Jehobah.” Kuma hakan yana nuna cewa Jehobah ne yake tanadar da dukan abubuwa masu kyau.
’Yan’uwa da yawa suna takawa zuwa tarurruka a ƙasar Ukraine, kuma hakan yana ba su zarafin tattaunawa da kuma ƙarfafa juna. Suna takawa na tsawon sa’a ɗaya ko fiye da hakan. Akwai ikilisiyoyi fiye da 50 a birnin Lviv, kuma 21 a cikinsu suna halartar taro a wani babban Majami’ar Mulki. Ganin ’yan’uwa da yawa a ranar Lahadi suna zuwa tarurruka daga safiya zuwa yamma yana da ban sha’awa.
Ba da daɗewa ba, muka saki jiki da ’yan’uwan, da yake suna da sauƙin hali kuma suna a shirye su kula da mutane. Ko da yake ba na jin yarensu sosai, amma suna haƙuri da ni. Yadda suke yi mini magana da yanayin fuskarsu ya nuna hakan.
Abin da ya faru a taron ƙasashe da aka yi a birnin Kiev, a shekara ta 2003 ya nuna cewa ’yan’uwanmu sun amince da juna sosai. Sa’ad da muka sauka daga wata tashar jirgin ƙasa da ke ƙarƙashin ƙasa, muka ga wata ƙaramar yarinya ta taho wurinmu, ta ce, “Ina neman kakata, ban san inda take ba.” Yarinyar ta ga bajonmu, kuma ta san cewa mu Shaidun Jehobah ne. Tana da hankali sosai kuma ba ta yi kuka ba. Wata matar mai kula da da’ira da take tare da mu ta kai yarinyar Sashen Matattarin Tsintuwa da ke wurin taron gundumar. Ba da daɗewa ba yarinyar ta gan kakarta. Yadda yarinyar ta amince da mu ya taɓa zuciya ta sosai ko da yake akwai mutane da yawa a wannan wurin.
Sa’ad da aka keɓe sabon ofishin reshenmu a ƙasar Ukraine a watan Mayu ta shekara ta 2001, ’yan’uwa daga ƙasashe da yawa sun zo bikin keɓewar. Bayan an ba da jawabi na musamman a filin wasa a safiyar Lahadi, ’yan’uwa maza da mata da yawan gaske suka yi zagayar buɗe ido a sabon Bethel ɗin. Wannan abu mai ban al’ajabi ne sosai. Ganin waɗannan ’yan’uwan da suke da hankali ya ƙarfafa ni sosai. Hakan ya sa na ga muhimmancin bauta wa Allah.
YANAYINMU YA CANJA NAN DA NAN
Abin baƙin ciki, a shekara ta 2004, maigidana John ya soma ciwon daji. Mun je ƙasar Kanada don jinya. Magani na farko da aka ba shi ya yi masa yawa har ya yi makonni a asibiti. Amma mun gode Allah cewa ya sake farfaɗowa. Ko da yake da ƙyar yake magana, amma yadda yake kallon mutanen da suka ziyarce shi ya nuna cewa yana godiya sosai.
Amma a wannan shekarar, ya rasu sanadiyyar ciwon. Na yi kewarsa sosai. Ni da maigidana mun yi farin ciki sosai a bautar Jehobah tare. Amma yanzu, mene ne zan yi? Na koma ƙasar Ukraine. Na yi farin ciki sosai saboda ƙaunar da iyalin Bethel da kuma ikilisiyar suka nuna mini.
Ba mu taɓa yin da-na-sani saboda zaɓin da muka yi ba. Rayuwa ce mai gamsarwa sosai. Kuma muna da nagargarun abokai. Har ila, na san cewa akwai abubuwa da yawa da zan iya koya daga alherin Jehobah. Na ƙuduri aniya cewa zan ci gaba da bauta wa Jehobah har abada domin a gaske ‘akwai jiyejiyen daɗi a cikin hannun damar Jehobah.’
[Bayanin da ke shafi na 6]
“Ba mu taɓa yin da-na-sani saboda zaɓin da muka yi ba”
[Hoto a shafi na 3]
Ranar da ni da John muka yi aure
[Hoto a shafi na 4]
Sa’ad da nake hidimar majagaba na musamman a garin Red Lake, a lardin Ontario
[Hoto a shafi na 5]
Tare da John a ƙasar Ukraine a shekara ta 2002