Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 3/15 pp. 7-9
  • Wace Irin Shawara Ce Kake Ba Mutane?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wace Irin Shawara Ce Kake Ba Mutane?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za Mu Nemi Shawara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Yadda Za Mu Ba Da Shawara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Wani Sabon Kayan Bincike
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 3/15 pp. 7-9

Wace Irin Shawara Ce Kake Ba Mutane?

Wani ya taɓa neman shawara daga wurin ka? Alal misali, wani ya taɓa maka tambayoyi kamar su: ‘Mene ne zan yi? Shin ya kamata na halarci wannan taron? Ko na zaɓi wannan sana’ar? Ko kuma na yi zawarci da wannan mutumin domin a nan gaba mu yi aure?’

Mutane masu kan gado za su iya neman shawara daga wurinka. Kuma waɗannan suna iya zama shawarwarin da za su shafi dangantakarsu da abokai ko iyalai ko kuma Jehobah. Shin za ka yi amfani da Littafi Mai Tsari don ba da shawara ko kuma za ka faɗi ra’ayinka? Yaya kake taimaka wa mutane su tsai da shawara mai kyau? Ko da batun mai muhimmanci ne sosai ko a’a, littafin Misalai 15:28 ya ce: “Zuciyar mai-adalci ta kan yi tunanin abin da za ta amsa.” Ka yi la’akari da yadda waɗannan ƙa’idodi biyar na Littafi Mai Tsarki za su taimaka maka sa’ad da kake ba da shawara.

1 Ka Fahimci Yanayin da Kyau.

“Wanda ya mayar da magana tun ba ya ji ba, wauta ce gareshi da kunya.”—MIS. 18:13.

Domin ka ba da shawara mai kyau, ya wajaba mu fahimci yanayin da kuma ra’ayin wanda yake neman shawarar. Alal misali: Idan wani ya kira ka ta wayar selula ya ce ka kwatanta masa gidanka, waɗanne tambayoyi ne za ka yi masa domin ka san yadda za ka taimaka masa? Shin za ka yi masa kwatance ba tare da ka fara tambayarsa inda yake ba? Hakika, ba za ka yi haka ba. Hakazalika, ba da ja-gora mai kyau yana bukatar sanin yanayin mutumin da kuma abin da yake tunani. Shin da akwai wasu abubuwa game da yanayinsa da zai iya shafi amsar da za mu ba da? Idan ba mu fahimci yanayin ba sosai, za mu iya ba da shawarar da za ta daɗa rikitar da wanda yake neman shawarar.—Luk 6:39.

Ka Tambaye Shi ko Ya Yi Bincike. Zai kuma dace mu yi wa wanda yake neman shawarar waɗannan tambayoyin: “Waɗanne shawarwarin Littafi Mai Tsarki ne kake tsammani za su taimake ka?” “Mene ne abubuwa masu kyau da kuma marasa kyau game da zaɓin da kake son ka yi?” “Wanne bincike ne ka riga ka yi?” “Waɗanne shawarwari ne dattawan ikilisiya da iyayenka da kuma wanda yake nazarin Littafi Mai Tsarki da kai suka ba ka?”

Amsoshi ga waɗannan tambayoyin za su taimaka maka ka san irin binciken da ya riga ya yi ko kuma shawarar da mutane suka ba shi. Kuma za mu sani ko yana so ne mu faɗa masa abin da yake son ya ji ne kawai.—2 Tim. 4:3.

2 Ka Guji Ba Da Amsa da Garaje.

“Bari kowane mutum ya yi hanzarin ji, ya yi jinkirin yin magana.”—YAƘ. 1:19.

A wasu lokatai, muna iya yin tunani cewa ba da amsa da sauri zai kasance da amfani. Amma shin hakan yana da kyau, musamman idan muna tattauna batun da ba mu yi bincike a kai sosai ba? Misalai 29:20 ya ce: “Ka ga mutum mai-garajen magana? A fi sa zuciya ga wawa da shi.”

Ka tabbata cewa amsar da za ka ba da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ka tambayi kanka, ‘Shin tunani da kuma “ruhun duniya” sun shafi yadda nake tunani?’ (1 Kor. 2:12, 13) Sa’ad da Yesu ya ce zai sha azaba kuma ya mutu, manzo Bitrus ya shawarce shi: “Allah shi sawwaƙa maka, Ubangiji: wannan ba za ya same ka ba daɗai.” Wanne darasi ne za mu iya koya daga yadda Bitrus ya aikata? Hakan ya nuna cewa idan ba mu mai da hankali ba, za mu iya ba da shawarar da ba ta ‘Allah ba ce, amma na mutane.’ (Mat. 16:21-23) Yana da kyau mu yi tunani sosai kafin mu ba da shawara. Ya dace mu tuna cewa hikimar Allah ta fi na ’yan Adam.—Ayu. 38:1-4; Mis. 11:2.

3 Ka Kasance da Tawali’u Wajen Yin Amfani da Kalmar Allah.

“Ba na yin komi domin kaina ba, amma ina faɗin waɗannan magana yadda Uba ya koya mani.”—YOH. 8:28.

Shin za ka ce, “Da ni ne kai, da na yi kaza da kaza”? Ko da tambayar tana da sauƙi, zai yi kyau ka bi misalin Yesu na tawali’u da kuma filako. Yesu ya fi kowanne ɗan Adam hikima da kuma basira, amma duk da haka, ya ce: “Gama ban yi magana bisa kaina ba; amma Uba . . . shi ne ya ba ni umurni, abin da zan faɗi, da magana da zan yi kuma.” (Yoh. 12:49, 50) Koyarwa da kuma shawarar da Yesu ya ba da sun jitu da nufin Allah.

Alal misali, littafin Luka 22:49 ya faɗa cewa almajiran Yesu sun nemi shawara ko ya dace su yi faɗa sa’ad da ake son a kama Yesu. Ɗaya cikin almajiran ya yi amfani da takobinsa don ya kāre Yesu. Ka lura cewa littafin Matta 26:52-54 ya faɗa cewa ko a cikin wannan yanayin, Yesu ya bayyana wa almajiran dokar Jehobah. Yesu ya san da ƙa’idodin da ke littafin Farawa 9:6 da annabce-annabcen da ke Zabura 22 da kuma Ishaya sura 53. Kuma wannan ya taimaka masa ya ba da shawarar da ta ceci rayuka kuma ta sa Jehobah farin ciki.

4 Ka Yi Amfani da Littattafai.

“Wanene fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima wanda ubangijinsa ya sanya shi bisa iyalin gidansa, domin shi ba su abincinsu a lotonsa?” —MAT. 24:45.

Yesu ya naɗa amintattun rukunin bawa da suke tanadar mana da littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki. Kafin ka ba wani shawara a kan wani batu mai muhimmanci, zai dace ka yi bincike sosai daga littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki.

Za mu iya samun bayanai da yawa ta wajen bincika littafin nan Watch Tower Publications Index da Watchtower Library.a Zai dace mu yi amfani da waɗannan littattafan. Akwai bayanai da kuma talifofi da yawa da za su taimaki mutumin da ke neman shawara. Shin za ka iya taimaka wa wani ya yi bincike da waɗannan littattafan don ya tsai da shawara mai kyau? Kamar yadda taswira za ta iya taimaka wa mutum ya san wurin da yake nema, hakan ma waɗannan littattafan za su iya taimaka wa mutum ya tsai da shawara da za ta taimaka masa ya samu rai madawwami.

Dattawa da yawa sun nuna wa ’yan’uwa yadda ake amfani da Watch Tower Publications Index da kuma Watchtower Library. Kuma hakan yana taimaka wa masu shela sa’ad da suke nazari, kuma yana taimaka musu su yi amfani da nassi sa’ad da suke tsai da shawara. Sun koya yin bimbini da kuma dogara ga littattafan da Jehobah yake tanadarwa don magance matsalolinmu da kuma gudanar da rayuwa ta yau da kullum. Ta hakan, suna ‘watsa hankulansu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.’—Ibran. 5:14.

5 Kada Ka Tsai da wa Mutane Shawara.

“Kowane mutum za ya ɗauki kayan kansa.”—GAL. 6:5.

Jehobah ya ba kowannenmu hakkin tsai da shawara ko zai bi ƙa’idodin nassi ko a’a. (K. Sha 30:19, 20) Akwai ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da yawa da suka yi magana game da wasu yanayi, kuma wanda yake neman shawara ne zai zaɓa wanda zai bi. Idan wani yana neman shawara daga wurinmu, zai dace mu tambayi kanmu, ‘Shin ina da ikon ba da amsa ga wannan tambayar?’ Akwai wasu batutuwa da ya kamata mu ce ya tambayi dattawa, kuma idan shi yaro ne ko matashi, zai dace mu ce ya tambayi iyayensa.

[Hasiya]

a Za a iya samun Watchtower Library a faifain CD-ROM a harsuna 39. Akwai Watch Tower Publications Index ma a harsuna 45.

[Akwati/​Hoto a shafi na 8]

Bincike Don Bauta ta Iyali

Za ka iya yin amfani da ranar Bauta ta Iyalinku da yamma don yin bincike a kan tambayar da wani ya yi maka kwanan nan. Waɗanne talifofi da kuma ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne za ka iya amfani da su don ka amsa tambayar mutumin? Alal misali, wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa zai iya tambayarka game da wata da yake son ya soma zawarci da ita don a nan gaba su yi aure. Sa’ad da kake yin amfani da Watch Tower Publications Index ko Watchtower Library, ka duba jigon nan “Dating” ko “Marriage,” wato, “Fita zance” ko “Aure.” Sai kuma ka duba kan maganan da ka amsa tambayar da mutumin yake yi. Kan maganan nan “See also” zai iya taimaka maka domin za su iya nuna maka ƙarin abubuwa game da binciken da kake yi.

[Akwati a shafi na 9]

Muna godiya sosai don tanadi da Jehobah ya yi mana ta ƙungiyarsa, domin muna iya samu da kuma ba da shawara mafi kyau. Littafin Mai-Wa’azi 12:11 ya ce: “Kalmomi masu-hikima kamar ƙaimi su ke; zantattukan da a ke tattarawa kuma kamar kafaffun ƙusoshi ne, daga bakin makiyayi ɗaya su ke fitowa.” Kamar “ƙaimi,” wato, sandar da ake korar dabbobi da ita, shawara da aka ba mu kai tsaye da kuma cikin ƙauna tana taimaka mana kada mu bijire. Kuma kamar yadda ake amfani da “ƙusoshi” don a gina gidaje masu ƙarfi, shawara mai kyau tana taimaka mana mu samu sakamako mai kyau. Masu hikima suna farin ciki don bin “zantattukan da a ke tattarawa,” ko kuma shawara mai kyau daga bakin “makiyayi ɗaya,” wato, Jehobah.

Ya kamata mu yi koyi da Makiyayinmu, Jehobah, sa’ad da muke ba da shawara. Muna farin cikin sauraron waɗanda suke neman shawara daga wurinmu, kuma muna taimaka musu iyakar gwargwadonmu. Idan mun yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke ba da shawara, hakan zai amfane mutane kuma zai taimaka musu su samu rai na har abada.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba