Jehu Ya Tallafa Wa Bauta Ta Gaskiya Da Ƙwazo
JEHU ya tallafa wa bauta ta gaskiya. Don ya idar da wannan hakkin, yana da ƙwazo da yin abu babu ɓata lokaci da nacewa da himma da kuma gaba gaɗi. Jehu ya nuna halaye da ya kamata mu yi koyi da su.
An ba Jehu wani aiki sa’ad da al’ummar Isra’ila take cikin mugun yanayi. Al’ummar tana ƙarƙashin mugun tasiri na Jezebel, gwauruwar Ahab da kuma mahaifiyar Jehoram, sarki da ke sarauta a lokacin. Ta ƙarfafa mutanen su bauta wa Baal maimakon bauta wa Jehobah, ta kashe annabawan Allah da kuma rinjayi mutane da ‘karuwancinta’ da kuma ‘maitar’ ta. (2 Sar. 9:22; 1 Sar. 18:4, 13) Jehobah ya ba da doka a halakar da dukan gidan Ahab haɗe da Jehoram da kuma Jezebel. Jehu ne aka sa ya yi ja-gora a wannan aikin.
Nassosin ya ce Jehu ya kasance tare da sarakunan yaƙi sa’ad da Isra’ilawa suke yaƙi da Suriyawa a Ramoth-gilead. Jehu yana da makami mai girma, wataƙila shi ne kwamanda ɗin sojojin Isra’ila. Annabi Elisha ya aiki ɗaya cikin ’ya’yan annabawa ya naɗa Jehu a matsayin sarki a ɓoye kuma ya umurce shi ya kashe kowanne namiji na gidan Ahab ’yan ridda.—2 Sar. 8:28; 9:1-10.
Sa’ad da abokan aikin Jehu suka tambaye shi dalilin wannan ziyarar, Jehu ya yi jinkirin ba da amsar. Amma sa’ad da aka matsa masa, sai ya faɗi gaskiyar sai kuma shi da abokansa suka soma ƙulla wa Jehoram. (2 Ki. 9:11-14) Wataƙila sojojin suna gaba da Ahab da kuma Jezebel. Duk da haka, Jehu ya yi tunani sosai a kan hanyar da ta fi dacewa da zai yi aikin da aka ba shi.
Kafin a naɗa Jehu, an ji wa Sarki Jehoram rauni a yaƙi kuma ya gudu zuwa birnin Jezreel yana sa rai zai warke. Jehu ya san cewa idan zai yi nasara, bai kamata batun nan ya kai Jezreel ba. Jehu ya ce, “Kada kowa shi tsira shi fita birni domin shi bada labari cikin Jezreel.” (2 Sar. 9:14, 15) Wataƙila ya yi tsammanin cewa waɗanda suke goyon bayan Jehoram za su yi faɗa da shi. Jehu yana son ya tabbata cewa faɗa bai taso ba.
SUKUWA DA HAUKA!
Don ya sa su mamaki, Jehu ya yi hanzarin yin sukuwa da karusar daga Ramoth-gilead zuwa Jezreel da ke da nisan mil arba’in da biyar. Da ya kusan inda yake zuwa, wani mai tsaro a kan hasumiya ya hango “rundunar Jehu tafe.” (2 Sar. 9:17) Wataƙila, Jehu ya je da runduna mai yawa don ya tabbata ya zartar da aikin da aka ba shi.
Da ya lura cewa Jehu mai gaba gaɗi yana kan ɗaya cikin karusar, mai tsaron ya ce: “Yana sukuwa da hauka.” (2 Sar. 9:20) Ko da yake wataƙila haka ne Jehu yake sukuwa, amma a wannan lokacin yana sukuwa da hauka don ya cim ma wannan aikin.
Bayan ya ƙi ya ce kome ga mutane biyu da aka aika wajensa, Jehu ya haɗu da Sarki Jehoram da abokinsa Ahaziah, sarkin Yahuda, kowannensu yana kan karusarsa. Sai Jehoram ya yi tambaya, “Lafiya, Jehu?” Shi ma ya amsa ya ce: “Ina fa lafiya, muddar karuwancin uwarka Jezebel da maitatta suna da yawa haka?” Don amsar ya firgita Jehoram, sai ya juya zai gudu. Amma Jehu ya fi shi gudu! Jehu fa ya ja bakansa, ya ɗirka wa Jehoram sai ta sha zarar zuciyarsa, sai sarkin ya kuwa fāɗi cikin karusarsa ya mutu. Ko da yake Ahaziya ya gudu, amma daga baya Jehu ya kama shi kuma ya sa a kashe shi.—2 Sar. 9:22-24, 27.
Sarauniya Jezebel ce wata a cikin gidan Ahab da za a kashe. Ya dace da Jehu ya kira ta “la’antaciyar macen nan.” Yayin da Jehu yake sukuwa zuwa cikin Jezreal, sai ya gan ta tana leƙowa ta taga. Ban da ɓata lokaci, Jehu ya ba ma’aikatan fada umurni su jefo Jezebel daga taga. Sai ya sa dawakai su tattaka wannan wadda ta ɓata dukan Isra’ila. Bayan hakan, Jehu ya halaka mutane da yawa a gidan mugun nan Ahab.—2 Sar. 9:30-34; 10:1-14.
Ko da yake nuna ƙarfi ba shi da kyau, ya kamata mu fahimci cewa a wannan zamanin, Jehobah ya yi amfani da bayinsa don ya zartar da hukuncinsa. Nassosi ya ce: “Wannan tafiya da Ahaziah ya yi zuwa wurin Jehoram ta zama hallakarsa bisa ga ƙadarar Allah: gama sa’anda ya zo, ya tafi tare da Jehoram garin yaƙi da Jehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya zuba masa mai, ya naɗa shi sarki, domin shi hallaka gidan Ahab.” (2 Laba. 22:7) Yayin da Jehu ya ba da umurni a jefar da jikin Jehoram daga cikin karusarsa, ya fahimci cewa ya cika alkawarin da Jehobah ya yi na rama wa kisan da Ahab ya yi wa Naboth. Bugu da ƙari, an umurci Jehu ya “ɗauki fansar jinin bayin [Allah]” da Jezebel ta zubar.—2 Sar. 9:7, 25, 26; 1 Sar. 21:17-19.
A yau, babu bawan Jehobah da zai yi yaƙi na zahiri da magabtan bauta ta gaskiya. “Ɗaukan fansa nawa ne,” in ji Allah. (Ibran. 10:30) Amma don a kāre ikilisiya daga mutane da za su ɓata ta, ya kamata dattawan Kirista su aikata da irin gaba gaɗi da Jehu yake da shi. (1 Kor. 5:9-13) Kuma dukan waɗanda suke cikin ikilisiya suna bukatar su ƙuduri aniya su guji cuɗanya da waɗanda aka yi wa yankan zumunci.—2 Yoh. 9-11.
JEHU YANA DA KISHI SABODA JEHOBAH
Mun san dalilin da ya sa Jehu ya cika aikinsa ta wurin abin da ya gaya wa Jehonadab mai aminci daga baya: “Ka zo tare da ni, ka ga kishina domin Ubangiji.” Jehonadab ya yi na’am da gayyar kuma ya shiga cikin karusar Jehu, kuma suka yi sukuwa zuwa Samariya. Jehu ya aikata da dabara a wurin “da nufin ya hallaka masu-yin sujada ga Baal.”—2 Sar. 10:15-17, 19.
Jehu ya sanar cewa yana son ya yi “babbar hadaya” ga Baal. (2 Sar. 10:18, 19) Wani masani ya ce, “Jehu ya yi amfani da kissa.” Ko da yake kalmar da aka yi amfani da ita a nan “tana nufin ‘hadaya,’ an kuma yi amfani da ita ga ‘halakar’ ’yan ridda.” Domin Jehu yana son dukan masu bauta wa Baal su halarci wannan taron, ya tara dukansu a gidan Baal kuma ya sa suka saka tufafin da ya ware su dabam. “Bayan da aka gama bada hadayar ƙonawa,” Jehu ya sa mutane 80 masu takobi su karkashe masu bauta wa Baal. Sai ya rushe gidan Baal kuma ya mai da shi salga, don kada a yi bauta a ciki.—2 Sar. 10:20-27.
A gaskiya, Jehu ya zubar da jini da yawa. Duk da haka, Nassosi ya nuna shi a matsayin jarumi da ya ’yantar da Isra’ila daga zaluncin Jezebel da iyalinta. Idan wani sarkin Isra’ila zai yi nasara a yin hakan, zai zama mutum mai gaba gaɗi da aniya da kuma himma. “Aiki ne mai wuya kuma ya yi shi da kyau,” in ji wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki. “Wataƙila yin sanyi-sanyi zai sa a kasa kawar da bautar Baal daga Isra’ila.”
Babu shakka, ka ga cewa ya kamata Kiristoci a yau su nuna wasu halaye na Jehu a wasu yanayi da suke fuskanta. Alal misali, yaya ya kamata mu aikata idan aka jarabce mu mu yi wani abu da Jehobah ba ya so? Ya kamata mu ƙi yin abin nan da nan da gaba gaɗi da kuma himma. Idan ya zo ga batun bautarmu, dole ne mu yi kishi saboda Jehobah.
KA KULA KA YI TAFIYA BISA DOKAR JEHOBAH
Ƙarshen wannan labarin ya zama abin kashedi a gare mu. Jehu ‘ba ya rabu da ’yan maruƙa na zinariya da ke cikin Bethel da Dan ba.’ (2 Sar. 10:29) Ta yaya zai yiwu wanda yake da himma don bauta ta gaskiya zai yi kamar ya amince da gumaka?
Mai yiwuwa Jehu ya gaskata cewa idan masarautan Isra’ila suna son su samu ’yanci daga Yahuda, ana bukatar a raba addini na masarautan biyu. Saboda haka, kamar sarakunan da suka mulki Isra’ila a dā, ya yi ƙoƙari ya raba su ta wajen gabatar da bautar maraƙi. Amma wannan ya nuna rashin imani ga Jehobah, wanda ya naɗa shi a matsayin sarki.
Jehobah ya yaba wa Jehu domin ya ‘hukunta da kyau abin da Allah ya nufa.’ Duk da haka, Jehu “ba ya kula ya yi tafiya bisa ga shari’ar Ubangiji, Allah na Isra’ila, da dukan zuciyatasa” ba. (2 Sar. 10:30, 31) Idan ka yi la’akari da abin da Jehu ya yi da farko, kana iya yin mamaki da kuma baƙin ciki. Duk da haka, ya koya mana darasi. Bai kamata mu ɗauki dangantakarmu da Jehobah da wasa ba. Muna bukatar mu kasance da aminci ga Allah a kowacce rana ta wajen yin nazari da kuma bimbini a kan Kalmarsa da kuma yin addu’a ga Ubanmu na samaniya da dukan zuciyarmu. Saboda haka, bari mu mai da hankali sosai mu ci gaba da yin tafiya bisa dokar Jehobah da dukan zuciyarmu.—1 Kor. 10:12.
[Akwati a shafi na 4]
Jehu a Littattafan Tarihi
Sau da yawa masu sūka sun yi musun ko mutanen da aka ambata a cikin Nassosi sun wanzu da gaske. Shin da akwai tabbaci daga wani wuri ban da Littafi Mai Tsarki cewa Jehu ya wanzu?
Aƙalla takardu guda uku na Assuriya ta dā sun ambata sunan wannan sarkin Isra’ila. Ɗaya cikin waɗannan ya yi da’awar nuna Jehu, ko kuma wataƙila ɗaya cikin wakilansa yana rusuna a gaban Sarkin ƙasar Assuriya, Shalmaneser na uku, yana miƙa masa kyauta. Abin da aka rubuta a cikin zanen ya ce: “Na karɓi kyautar, azurfa da zinariya da saplu-bowl, wato, kwanon zinariya da tulun ado na zinariya da kofin tambulan na zinariya da bokiti na zinariya da gwangwani da sandar sarki, (da) kayayyakin katako daga Jehu, Ɗan Omri.” Jehu ba “ɗan Omri” ba ne, amma an yi amfani da wannan furucin don a nuna sarakunan Isra’ila da suka bi bayansa, wataƙila domin Omri sananne ne kuma shi ne ya gina Samariya, babban birnin Isra’ila.
Ba za a iya tabbatar da da’awar da sarkin Assuriya ya yi cewa Jehu ya ba shi kyauta ba. Amma, ya ambata Jehu sau uku, a kan rubutun da ke kan mutum-mutumi na sarki Shalmaneser da kuma rubutaccen tarihi na sarautar Assuriya. Wannan bincike ya tabbatar cewa Jehu da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki ya wanzu da gaske.