Yanzu Lokaci Ne Na Ɗaukan Mataki
“Har yaushe za ku yi ɗingishi a kan wannan imani da wancan?”—1 SARAKUNA 18:21.
1. Me ya sa zamaninmu ya bambanta ƙwarai da na dā?
KA GASKATA cewa Jehobah ne Allah makaɗaici na gaskiya? Ka gaskata cewa annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki na nuni ga lokacinmu na “kwanaki na ƙarshe” na mugun zamanin Shaiɗan? (2 Timothawus 3:1) Idan haka ne, za ka yarda cewa yanzu ne ake bukatar a ɗauki mataki. Rayukan mutane ba su taɓa kasancewa cikin haɗari kamar yanzu ba.
2. Menene ya faru da masarautar ƙabilu goma ta Isra’ila a lokacin sarautar Sarki Ahab?
2 A ƙarni na goma K.Z., al’ummar Isra’ila tana bukatar tsai da shawara mai muhimmanci. Wanene za su bauta wa? Sarki Ahab ya ɗaukaka bautar Ba’al a tsakanin ƙabilu goma na Isra’ila, domin rinjayar matarsa arniya Yezebel. Ba’al allahn ni’ima ne wanda ya kamata ya yi tanadin ruwa da amfanin gona. Mutane da yawa masu bauta wa Ba’al wataƙila sun yi masa alamar sumba da hannunsu ko kuma sun durƙusa wa wani gunkin allahnsu. Don Ba’al ya albarkaci shuke-shukensu da dabbobinsu, masu bautarsa suna ayyuka na lalata da kuma karuwanci a haikali. Suna da al’adar tsattsaga jikinsu don jini ya zuba.—1 Sarakuna 18:28.
3. Yaya bautar Ba’al ta shafi mutanen Allah?
3 Isra’ilawa, 7,000 ne suka ƙi su sa hannu a wannan bautar gumaka, ta lalata da kuma mugunta. (1 Sarakuna 19:18) Sun manne wa dangantakarsu ta alkawari da Jehobah Allah da aminci, kuma an tsananta musu domin wannan. Alal misali, Sarauniya Yezebel ta kashe annabawan Jehobah da yawa. (1 Sarakuna 18:4, 13) Domin wannan yanayi, yawancin Isra’ilawa suna haɗin addini, wato, suna ƙoƙari su faranta wa Jehobah da kuma Ba’al rai. Amma Ba’isra’ile ya yi ridda idan ya bar Jehobah ya bauta wa allahn ƙarya. Jehobah ya yi alkawari zai albarkaci Isra’ilawa idan sun ƙaunace shi kuma suka yi biyayya ga umurninsa. Amma, ya yi musu kashedi cewa idan sun ƙi su yi masa “sujada” zai halaka su.—Kubawar Shari’a 5:6-10; 28:15, 63.
4. Menene Yesu da mabiyansa suka annabta zai faru tsakanin Kiristoci, kuma yaya hakan ya cika?
4 Irin wannan yanayi ya kasance a Kiristendam a yau. Waɗanda suke zuwa coci suna da’awa su Kiristoci ne, amma ranakun hutunsu, halinsu, da imaninsu sun saɓa wa koyarwar Littafi Mai Tsarki. Kamar Yezebel, limaman Kiristendam ne suke zuga a tsananta wa Shaidun Jehobah. Tarihin Limaman Kiristendam na goyon bayan yaƙe-yaƙe ne, da haka suna da hannu a mutuwar miliyoyin mutanen cocinsu. Littafi Mai Tsarki ya ce irin wannan goyon baya da addini suke ba wa gwamnati ta duniya fasikanci ne na ruhaniya. (Ru’ya ta Yohanna 18:2, 3) Ƙari ga haka, Kiristendam suna na’am da fasikanci na zahiri, har tsakanin limamai. Yesu Kristi da mabiyansa sun annabta cewa za a yi wannan ridda mai tsanani. (Matta 13:36-43; Ayukan Manzanni 20:29, 30; 2 Bitrus 2:1, 2) Menene zai zama ƙarshen mabiyan Kiristendam fiye da biliyan ɗaya? Wane hakki ne masu bauta na gaskiya na Jehobah suke da shi ga waɗannan da wasu da addinin ƙarya ya yaudare su? Za mu sami amsar waɗannan tambayoyi ta wajen bincika aukuwa na musamman da ya sa aka “tumɓuke Ba’al daga cikin Isra’ila.”—2 Sarakuna 10:28.
Ƙaunar Allah ga Mutanensa Masu Tawaye
5. Ta yaya Jehobah ya nuna ya damu da mutanensa masu tawaye?
5 Jehobah Allah ba ya jin daɗin yi wa waɗanda suka yi masa rashin aminci horo. Da yake shi Uba ne mai ƙauna, yana son mugaye su tuba su koma gare shi. (Ezekiel 18:32; 2 Bitrus 3:9) Don ya ba da tabbacin wannan, Jehobah ya yi amfani da annabawa masu yawa a kwanakin Ahab da Yezebel don ya yi wa mutanensa kashedi game da sakamakon bautar Ba’al. Iliya yana ɗaya daga cikin irin waɗannan annabawan. Bayan fari mai ɓarna da aka annabta ya faru, Iliya ya gaya wa Sarki Ahab ya tara Isra’ilawa da annabawan Ba’al a kan Dutsen Karmel.—1 Sarakuna 18:1, 19.
6, 7. (a) Ta yaya Iliya ya fallasa dalilin da ya sa Isra’ila ta yi ridda? (b) Menene annabawan Ba’al suka yi? (c) Menene Iliya ya yi?
6 An yi taron a wurin bagadin Jehobah da aka “rushe,” wataƙila don a faranta wa Yezebel rai. (1 Sarakuna 18:30) Abin baƙin ciki, Isra’ilawa da suka halarci taron ba su tabbata ba ko Jehobah ne ko kuwa Ba’al ne zai iya kawo ruwan sama da suke matuƙar bukata. Annabawa 450 ne suka wakilci Ba’al, amma Iliya ne kawai annabi da ya wakilci Jehobah. Don ya faɗi ainihin matsalarsu, Iliya ya tambayi mutanen: “Har yaushe za ku yi ɗingishi a kan wannan imani da wancan?” Har a kalmomi masu sauƙi, ya gabatar musu da matsalar: “Idan Ubangiji shi ne Allah, ku bi shi; amma idan Baal ne, sai ku bi shi.” Don ya motsa Isra’ilawa waɗanda suka kasa tsai da shawarar su bauta wa Jehobah shi kaɗai, Iliya ya ce a yi gwaji da zai nuna Allah na gaskiya. Za a yanka bijimai biyu don hadaya, ɗaya don Jehobah ɗayan kuma don Ba’al. Allah na gaskiya zai ƙona nasa. Annabawan Ba’al suka shirya hadayarsu, suka yi sa’o’i da yawa suna roƙo: “Ya Baal, ka ji mu!” Sa’ad da Iliya ya soma yi musu ba’a, suka tsastsaga jikinsu har jini yana ta zuba, suka yi ta ihu. Amma ba amsa.—1 Sarakuna 18:21, 26-29.
7 Lokacin Iliya ya yi ya yi nasa. Da farko ya gyara bagadin Jehobah kuma ya saka naman bijimin a kai. Bayan haka, sai ya ce a kwara tuluna huɗu na ruwa a kan hadayar. Haka aka yi sau uku har ruwa ya malale bagaden ya cika wuriyar. Sai Iliya ya yi addu’a: “Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da na Ishaku, da na Isra’ila, bari ya zama sananne yau kai ne Allah cikin Isra’ila, ni kuma bawanka ne, na yi wannan duka kuma bisa ga cewarka. Ka ji ni, ya Ubangiji, ka ji ni, domin wannan jama’a su sani, kai, Ubangiji, Allah ne, ka juyadda zukatansu kuma.”—1 Sarakuna 18:30-37.
8. Ta yaya Allah ya aikata ga addu’ar Iliya, kuma menene annabin ya yi?
8 Allah na gaskiya ya amsa ta wajen sa wuta daga sama ta faɗo ta cinye hadayar da bagadin. Wannan wutar ta ƙona ruwan da ke cikin wuriyar kewaye da bagadin! Ka yi tunanin yadda wannan ya shafi Isra’ilawan. “Suka fāɗi bisa fuskarsu: suka ce, Ubangiji, shi ne Allah; Ubangiji shi ne Allah.” Iliya ya ƙara ɗaukan mataki, ya ba wa Isra’ilawa umurni: “Ku damƙe annabawan Baal; kada wani ya tsira.” Sai aka kashe dukan annabawan Ba’al guda 450 a Dutsen Karmel.—1 Sarakuna 18:38-40.
9. Ta yaya har ila aka gwada masu bauta ta gaskiya?
9 A wannan rana ta musamman, Jehobah ya sa aka yi ruwa a ƙasar bayan shekara uku da rabi! (Yaƙub 5:17, 18) Ka yi tunanin magana da Isra’ilawa suke yi sa’ad da suke komawa gida; Jehobah ya nuna shi ne Allah na gaskiya. Amma masu bauta wa Ba’al ba su ba da gari ba. Yezebel ta ci gaba da tsananta wa bayin Jehobah. (1 Sarakuna 19:1, 2; 21:11-16) Da haka an sake gwada amincin mutanen Allah. Shin za su riƙa bauta wa Jehobah shi kaɗai sa’ad da lokacinsa na hukunta masu bauta wa Ba’al ya kai?
Ka Ɗauki Mataki Yanzu
10. (a) A wannan zamanin, menene Kiristoci shafaffu suke yi? (b) Menene yake nufi a yi biyayya da umurni da ke Ru’ya ta Yohanna 18:4?
10 A wannan zamanin, Kiristoci shafaffu sun yi aiki kamar na Iliya. Ta maganar baki da kuma littattafai, sun gargaɗi mutane na dukan al’ummai ciki da waje na Kiristendam game da haɗarin bin addinin ƙarya. Saboda haka, mutane da yawa sun ɗauki mataki sun daina tarayya da addinan ƙarya. Suka keɓe rayukansu ga Jehobah kuma suka zama almajiran Yesu Kristi da suka yi baftisma. Hakika, sun yi biyayya ga roƙon Allah na gaggawa game da addinin ƙarya: “Ku fito daga cikinta, ya al’ummata, domin kada ku yi tarayya da zunubanta, kada ku sha rabon annobanta.”—Ru’ya ta Yohanna 18:4.
11. Menene ake bukata don a sami amincewar Jehobah?
11 Ko da yake mutane da yawa suna son saƙon Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah suke yaɗawa, har ila ba su da tabbacin abin da ya kamata su yi. Wasu cikin waɗannan wani lokaci suna zuwa taron Kirista kamar su, kiyaye Jibin Maraice na Ubangiji ko wasu sashe na taron gunduma. Muna ariritar irin waɗannan su yi la’akari da kalmomin Iliya: “Har yaushe za ku yi ɗingishi a kan wannan imani da wancan?” (1 Sarakuna 18:21) Maimakon su ɓata lokaci, suna bukatar su ɗauki mataki yanzu kuma su yi ƙoƙari su zama masu bauta wa Jehobah da suka keɓe kansu, kuma su yi baftisma. Begensu na rai madawwami yana cikin haɗari!—2 Tassalunikawa 1:6-9.
12. Cikin wane irin mugun yanayi ne wasu Kiristoci da suka yi baftisma suka faɗa, kuma me ya kamata su yi?
12 Abin baƙin ciki, wasu Kiristoci da suka yi baftisma ba sa fita wa’azi a kai a kai ko kuma sun zama marasa ƙwazo a bautarsu. (Ibraniyawa 10:23-25; 13:15, 16) Wasu ba sa himma kuma domin suna tsoron tsanantawa, suna alhinin biyan bukatar rayuwa, suna ƙoƙarin zama masu arziki, ko kuma suna biɗan annashuwa na kansu. Yesu ya yi kashedi cewa waɗannan abubuwa za su sarƙe wasu cikin mabiyansa, ya sa su yi tuntuɓe, kuma ya zame musu tarko. (Matta 10:28-33; 13:20-22; Luka 12:22-31; 21:34-36) Maimakon yin “ɗingishi a kan wannan imani da wancan” ya kamata irin waɗannan su ‘yi himma su tuba’ ta wajen ɗaukan mataki yanzu su keɓe kansu ga Allah.—Ru’ya ta Yohanna 3:15-19.
Ƙarshen Addinin Ƙarya Farat Ɗaya
13. Ka kwatanta yanayin da ke Isra’ila sa’ad da aka naɗa Yehu sarki.
13 Abin da ya faru a Isra’ila kusan shekara 18 bayan da aka warware batun Allahntaka a Dutsen Karmel ne dalilin da ya sa yake da gaggawa ’yan adam su ɗauki mataki yanzu. Ranar hukuncin Jehobah a kan bautar Ba’al ya zo farat ɗaya a lokacin hidimar Elisha, magajin Iliya. Yehoram, ɗan sarkin Ahab ne ke sarautar Isra’ila kuma Yezebel har ila tana da rai, ita ce mamar sarkin. Elisha ya aiki bawansa a ɓoye ya naɗa Yehu shugaban sojojin Isra’ila, ya zama sabon sarki. A lokacin Yehu yana gabas da Urdun a Ramoth-gilead, yana ja-gorar yaƙi da ake yi da magabtan Isra’la. Sarki Yehoram yana Yezreyel a kwarin da ke kusa da Magiddo, yana samun sauƙi daga ciwo da ya ji a yaƙi.—2 Sarakuna 8:29–9:4.
14, 15. Wane aiki ne aka ce Yehu ya yi, kuma yaya ya aikata shi?
14 Ga abin da Jehobah ya umurci Yehu ya yi: “Za ka bugi gidan ubanɗakinka Ahab, domin in ɗauki fansar jinin bayina annabawa, da jinin dukan bayin Ubangiji a wurin Jezebel. Gama dukan gidan Ahab za su hallaka, . . . karnuka za su ci Jezebel cikin yankin Jezreel, ba kuwa mai-bizne ta.”—2 Sarakuna 9:7-10.
15 Yehu mai aikata abu nan da nan ne. Babu ɓata lokaci, ya shiga cikin karusarsa ya nufi Yezreyel cikin hanzari. Wani mai tsaro a Yezreyel da ya san yadda Yehu yake sukuwa, ya gaya wa Sarki Yehoram, Yehoram kuma ya hau kan karusarsa ya tafi ya sadu da Yehu shugaban sojojinsa. Sa’ad da suka sadu, Yehoram ya yi tambaya: “Lafiya, Jehu?” Yehu ya amsa: “Ina fa lafiya, muddar karuwancin uwarka Jezebel da maitatta suna dayawa haka?” Kafin Sarki Yehoram ya gudu, Yehu ya ja bakansa kuma ya ɗirka wa Yehoram kibiya a zuciyarsa.—2 Sarakuna 9:20-24.
16. (a) Wane yanayi ne ma’aikatan Yezebel suka fuskanta farat ɗaya? (b) Ta yaya kalmomin Jehobah game da Yezebel suka cika?
16 Babu ɓata lokaci, Yehu ya yi sukuwa da karusarsa zuwa birnin. Da ta leƙa ta taga, Yezebel da ta sha kwalliya ta yi wa Yehu barazana. Yehu ya yi banza da ita, ya yi kira a tallafa masa: “Wa ke wajena? Wa?” Fadawan Yezebel suka aikata babu ɓata lokaci. Fadawa biyu ko uku suka leƙa ta taga. Nan da nan, aka gwada amincinsu. Yehu ya ba su umurni su “jefo ta ƙasa.” Fadawan suka jefar da Yezebel ta faɗi a kan titi, a nan dawakan Yehu da karusa suka tattake ta. Da haka mai ɗaukaka bautar Ba’al a Isra’ila ta zo ƙarshenta. Kafin a binne ta, karnuka suka cinye ta, kamar yadda aka annabta.—2 Sarakuna 9:30-37.
17. Hukuncin Allah a kan Yezebel ya kamata ya ƙarfafa bangaskiyarmu a kan wane aukuwa na nan gaba?
17 Hakanan ma, karuwa ta alama mai suna “Babila Babba” za to zo ƙarshenta na ban mamaki. Karuwan tana wakiltan addinan ƙarya na duniyar Shaiɗan, waɗanda suka samo tushensu daga birnin Babila na dā. Bayan ƙarshen addinin ƙarya, Jehobah Allah zai mai da hankalinsa ga dukan mutane da suke sashe na duniyar Shaiɗan. Za a halaka waɗannan, sai a sami sabuwar duniya ta adalci.—Ru’ya ta Yohanna 17:3-6; 19:19-21; 21:1-4.
18. Bayan mutuwar Yezebel, menene ya faru da masu bauta wa Ba’al a Isra’ila?
18 Bayan mutuwar Yezebel, Sarki Yehu bai ɓata lokaci ba wajen kashe dukan zuriyar Ahab da masu goyon bayansa na musamman. (2 Sarakuna 10:11) Amma Isra’ilawa da yawa masu bauta wa Ba’al sun rage a ƙasar. Game da waɗannan, Yehu ya aikata don ya nuna ‘kishinsa domin Ubangiji.’ (2 Sarakuna 10:16) Yehu ya yi kamar shi ma yana bauta wa Ba’al, sai ya shirya babban biki a haikalin Ba’al da Ahab ya gina a Samariya. Duka masu bauta wa Ba’al a Isra’ila sun halarci bikin. Da yake an kama su cikin haikalin, mutanen Yehu suka kashe su duka. Littafi Mai Tsarki ya kammala labarin da kalmomin nan: “Da hakanan Yehu ya tumɓuke Baal daga cikin Isra’ila, ya halaka.”—2 Sarakuna 10:18-28.
19. Wane bege mai girma yake jiran “taro mai-girma” na masu bauta wa Jehobah cikin aminci?
19 An kawar da bautar Ba’al daga Isra’ila. Babu shakka, addinan ƙarya na wannan duniya za su zo ƙarshensu, da ban mamaki kuwa. A gefen wa za ka kasance a wannan babbar rana ta hukunci? Ka tsai da shawara yanzu, za ka iya samun gata a haɗa ka cikin “taro mai-girma” na waɗanda suka tsira wa “babban tsananin.” Sa’annan za ka iya tuna dā da farin ciki kuma ka yabi Allah don ya zartar da hukunci a kan “babbar karuwa, wadda ta ɓāta duniya da fasikancinta.” Da kai da sauran masu bauta ta gaskiya, za ku yarda da kalmomi masu ban sha’awa da mala’iku a sama suka rera: “Hallelujah: gama Ubangiji Allahnmu, Mai-iko duka, yana mulki.”—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10, 14; 19:1, 2, 6.
Tambayoyi don Bimbini
• Ta yaya Isra’ila ta dā suka kasance da alhakin bautar Ba’al?
• Wace ridda mai girma ne Littafi Mai Tsarki ya annabta, kuma yaya wannan annabci ya cika?
• Ta yaya Yehu ya kawar da bautar Ba’al?
• Menene dole mu yi don mu tsira wa ranar hukunci na Allah?
[Taswira a shafi na 17]
Socoh
Aphek
Helkath
Jokneam
Megiddo
Taanach
Dothan
SAMARIYA
En-dor
Shunem
Ophrah
Yezreyel
Ibleam (Gath-rimmon)
Tirzah
Beth-shemesh
Beth-shan (Beth-shan)
Jabesh-gilead
Abel-meholah
Gidan Arbel
Ramoth-gilead
[Mountain Peaks]
Dutsen Kamel
Dutsen Tabor
Moreh
Dutsen Gilboa
[Bodies of water]
Bahar Rum
Tekun Galili
[River]
Kogin Urdun
[Spring and well]
Rijiyar Harod
[Inda aka Dauko]
Based on maps copyrighted by Pictorial Archive (Near Eastern History) Est. and Survey of Israel
[Hoto a shafi na 18]
Yin wa’azin Mulki a kai a kai da kuma halartan taron Kirista ayyuka ne masu muhimmanci a bauta ta gaskiya
[Hoto a shafi na 20]
Kamar Yehu, duka waɗanda suke son su tsira wa ranar Jehobah dole su aikata