Abin Da Ke Ciki
15 Ga Nuwamba, 2011
Na Nazari
TALIFOFIN NAZARI NA MAKONNIN:
26 ga Disamba, 2011–1 ga Janairu, 2012
“Kada Ka Jingina ga Naka Fahimi”
SHAFI NA 6
WAƘOƘI: 133, 23
2-8 ga Janairu, 2012
Ka Yi Tafiya Bisa ga Ruhu, kuma Za Ka Samu Rai da Salama
SHAFI NA 10
WAƘOƘI: 83, 120
9-15 ga Janairu, 2012
SHAFI NA 16
WAƘOƘI: 40, 85
16-22 ga Janairu, 2012
Ku Taimaki Maza Su Samu Ci Gaba a Ruhaniya
SHAFI NA 24
WAƘOƘI: 123, 95
23-29 ga Janairu, 2012
Ku Koyar da ’Yan’uwa Maza Su Yi Burin Aikin Kula
SHAFI NA 28
WAƘOƘI: 45, 10
Manufar Talifofin Nazari
TALIFIN NAZARI NA 1 SHAFUFFUKA NA 6-10
Shin kana amfana sosai daga tanadin yin addu’a da Allah ya yi mana? Ka koya yadda Addu’a za ta iya taimaka mana mu fuskanci mawuyacin yanayi da tsai da shawara mai muhimmanci da kuma jimre da gwaje-gwaje.
TALIFIN NAZARI NA 2 SHAFUFFUKA NA 10-14
Manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci da ke Roma abin da ya kamata su mai da wa hankali domin su samu rai da salama. Ka koya yadda za ka iya amfana daga gargaɗin da ya ba su.
TALIFIN NAZARI NA 3 SHAFUFFUKA NA 16-20
Kamar yadda aka nuna a wannan talifin, amintattun bayin Jehobah na dā sun yi rayuwa a matsayin “baƙi.” Mabiyan farko na Yesu ma hakan. Amma Kiristoci na gaskiya a yau fa? Ka koya abin da yake nufi mu zauna a matsayin baƙi a wannan muguwar duniya.
TALIFOFIN NAZARI NA 4, 5 SHAFUFFUKA NA 24-32
Ana bukatar maza da za su iya yin ja-gora a abubuwa na ruhaniya. Yesu ya taimaki maza da yawa su karɓi bishara kuma su cancanci samun gata. Idan mun nazarta hanyoyin da ya yi hakan, za mu iya koya yadda za mu iya taimaka wa maza da muka haɗu da su a hidima da kuma yadda za mu iya taimaka wa maza da suka yi baftisma a cikin ikilisiya su samu gata a ƙungiyar Jehobah.
A FITOWAR NAN
3 Jehu Ya Tallafa wa Bauta ta Gaskiya da Ƙwazo
15 “Na Naƙasa Yanzu amma Ba Har Abada Ba!”
22 Kana Farin Ciki da Gatar Yin “Alheri”?