Tambayoyi Daga Masu Karatu
Mene ne ya kamata na yi idan ina da tambaya game da wani abin da na karanta cikin Littafi Mai Tsarki ko kuma idan ina bukatar shawara game da matsalar da nake da ita?
Misalai 2:1-5 ta aririci kowanenmu ya ‘biɗi’ hikima da kuma fahimi kamar muna neman “ɓoyayyun dukiya.” Wannan yana nufin cewa ya kamata mu yi ƙoƙari sosai mu yi bincike a kan tambayoyinmu game da Littafi Mai Tsarki da kuma yi maganin matsalolin da muke da su. Ta yaya za mu iya yin hakan?
Littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education shafuffuka na 33 zuwa 38, ya bayyana “Yadda Za a Yi Bincike” ta wajen yin amfani da kayayyakin da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya yi tanadinsu. (Mat. 24:45) Shafi na 36 ya bayyana yadda za a yi amfani da littafin nan Watch Tower Publications Index, wanda an raba kowanne littafin zuwa jigon nassi da kuma fihirisar nassin. Yana sa ya yiwu a yi bincike ta wajen neman muhimman kalamai ko kuma ayoyin Littafi Mai Tsarki, kuma za ka samu jerin littattafai da za ka yi bincike a ciki. Ka yi haƙuri wajen neman ainihin amsa ko kuma bayani da kake bukata. Ka tuna cewa kana neman “ɓoyayyun dukiya,” wanda ke bukatar lokaci da kuma ƙoƙari sosai.
Hakika, da akwai wasu batutuwa da nassosi da littattafanmu ba su yi magana a kansu ba. Kuma ko idan mun yi magana a kan wata ayar Littafi Mai Tsarki, wataƙila ba mu tattauna ainihin amsar da kake so ba. Har ila, wasu labaran Littafi Mai Tsarki suna sa a yi tambayoyi don ba dukan abin da ya faru ba ne aka rubuta a cikin Nassosi ba. Saboda haka, ba za mu iya samun amsoshi ga dukan tambayoyin da muke da su nan da nan ba. A irin wannan yanayin, ya kamata mu guji ƙaga abubuwan da ba za a iya ba da amsarsu ba, idan ba haka ba za mu sa kanmu cikin yin musun da ke ‘jawo muhawwara, da ba su aika wakilcin Allah wanda ke cikin bangaskiya ba.’ (1 Tim. 1:4; 2 Tim. 2:23; Tit. 3:9) Ofishin reshe ko kuma Hedkwatarmu ta duniya ba su da ikon bincika da kuma amsa irin waɗannan tambayoyin da ba a tattauna a littattafanmu ba. Ya kamata mu gamsu cewa Littafi Mai Tsarki ya ba da isashen bayani da zai yi mana ja-gora a rayuwa kuma ya cire wasu bayanai don mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi ga Mawallafinsa.—Ka duba littafin nan Ka Kusaci Jehovah, shafuffuka na 185 zuwa 187.
Idan ka yi iya ƙoƙarinka ka bincika wani batu da ya shafe ka amma har ila ba ka sami amsar da kake bukata kuma fa? Za ka iya tambayar wani ɗan’uwa da ya manyanta, wataƙila ɗaya cikin dattawan ikilisiyarku. Sun san Littafi Mai Tsarki kuma suna da basira a hanyar rayuwar Kirista. Taimakonsu zai dace sosai idan kana bukatar shawara game da matsala da kake da ita ko kuma shawara da kake son ka tsai da, domin sun san ka da kuma yanayinka don suna kusa da kai. Kuma kada ka manta ka yi addu’a ga Jehobah musamman game da damuwarka kuma ka gaya masa ya ja-gorance ka ta wurin ruhunsa mai tsarki, “gama Ubangiji yana bada hikima . . . da fahimi.”—Mis. 2:6; Luk 11:13.