Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/15 p. 3-p. 5 par. 4
  • Shin Ka Ga Tabbaci Cewa Allah Yana Ja-gora Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shin Ka Ga Tabbaci Cewa Allah Yana Ja-gora Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sun Manta da Tabbacin
  • Ka Ga Tabbacin Ja-gorar Allah a Yau
  • Ka Bi Ja-gorar Allah
  • Ku Ci-gaba da Bin Ja-gorancin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Bi Umurnin Allah A Dukan Abu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Kada Ka Mance da Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Sani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/15 p. 3-p. 5 par. 4

Shin Ka Ga Tabbaci Cewa Allah Yana Ja-gora Kuwa?

ISRA’ILAWA da kuma Masarawa ba su taɓa ganin irin wannan abu a dā ba. Yayin da Isra’ilawa suke Fitowa daga ƙasar Masar, umudi na girgije yana tafiya kusa da su kuma ya ci gaba da kasancewa tare da su. Da daddare yana zama umudi na wuta. Hakan yana da ban al’ajabi! Amma daga ina ya fito? Mene ne manufarsa? Kuma mene ne za mu iya koya daga yadda Isra’ilawa suka ɗauki “umudi na wuta da na girgije” bayan shekaru 3,500 na wannan aukuwar?—Fit. 14:24.

Kalmar Allah ta gaya mana tushe da kuma manufar umudin, ta ce: “Ubangiji yana tafe gabansu da rana cikin umudi na girgije, domin ya yi masu ja gaba cikin tafarki; da dare kuma cikin umudi na wuta, domin a ba su haske; su yi tafiya dare da rana.” (Fit. 13:21, 22) Jehobah ya yi amfani da umudi na girgije da na wuta don ya fito da mutanensa daga ƙasar Masar da kuma daga cikin jeji. Za su kasance a shirye don su bi shi. Sa’ad da rundunar ƙasar Masar suke son su kai wa mutanen Allah hari, umudin ya shiga tsakanin rukuni biyun don ya kāre Isra’ilawa. (Fit. 14:19, 20) Bin ja-gorar umudin ne kaɗai za ta sa Isra’ilawa su kai Ƙasar Alkawari ko da yake umudin bai nuna hanyar da ta fi kyau na zuwa wurin ba.

Umudin ya tabbatar wa mutanen Allah cewa Jehobah yana tare da su. Yana wakiltar Jehobah, kuma a wasu lokatai ya yi magana daga cikin umudin. (Lit. Lis. 14:14; Zab. 99:7) Bugu da ƙari, girgijen ya nuna cewa Musa ne Jehobah ya naɗa don ya ja-goranci al’ummar. (Fit. 33:9) Hakazalika, lokaci na ƙarshe da aka ambata cewa girgijen ya bayyana ya tabbatar mana cewa Jehobah ya naɗa Joshua a matsayin wanda zai ɗauki matsayin Musa. (K. Sha 31:14, 15) Hakika, sakamako mai kyau na Fitowar zai dangana idan Isra’ilawa suka tabbata cewa Allah yana musu ja-gora kuma suka bi hakan.

Sun Manta da Tabbacin

Babu shakka Isra’ilawa sun yi mamaki sa’ad da suka fara ganin wannan umudin. Abin baƙin ciki, wannan mu’ujizar da suke gani a koyaushe bai burge Isra’ilawa har su ci gaba da kasancewa da tabbaci ga Jehobah ba. Sun ƙalubalanci yadda Allah yake musu ja-gora sau da yawa. Sa’ad da rundunar ƙasar Masar suka bi su, ba su dogara ga ikon ceto na Jehobah ba. Maimakon haka, sun zargi bawan Allah Musa cewa yana son ya je ya kashe su. (Fit. 14:10-12) Bayan an cece su a Jar Teku, sun yi gunaguni game da Musa da Haruna da kuma Jehobah domin sun ɗauka cewa suna rashin abinci da ruwa. (Fit. 15:22-24; 16:1-3; 17:1-3, 7) Kuma wasu makonni bayan hakan, sun matsa wa Haruna ya yi musu maraƙi na zinariya. Ka yi tunanin wannan! A wani sashe na sansaninsu, Isra’ilawa sun ga umudin na girgije da na wuta, wannan tabbaci ne mai girma na Wanda ya fito da su daga ƙasar Masar, kuma ba su yi nisa ba daga wurin sa’ad da suka soma bauta wa gunki marar rai, suna cewa: “Wannan Allahnka ne wanda ya fishe ka daga cikin Masar.” Lallai wannan “aikin cakuna” ne sosai!—Fit. 32:4; Neh. 9:18.

Tawayen da Isra’ilawa suka yi ya nuna cewa sun rena ja-gorar Jehobah sosai. Amma matsalarsu ita ce cewa ba su fahimci yadda Jehobah yake musu ja-gora ba kuma ba su bi ja-gorarsa ba. Sun ga umudin, amma sun mance cewa yana wakiltar ja-gorar Jehobah. Ko da yake ayyukansu sun “cakuni Mai-tsarki na Isra’ila,” Jehobah cikin jin ƙai ya ci gaba da yi musu ja-gora ta wurin umudin har Isra’ila ta kai Ƙasar Alkawari.—Zab. 78:40-42, 52-54; Neh. 9:19.

Ka Ga Tabbacin Ja-gorar Allah a Yau

Hakazalika, a yau, Jehobah bai taɓa ƙyale mutanensa ba tare da yi musu ja-gora ba. Kamar yadda bai bukaci Isra’ilawa su nemi hanyarsu ba, ba a gaya mana a yau ba cewa mu nemi hanyar da ke bishe zuwa sabuwar duniya da aka yi mana alkawarinta ba. Yesu Kristi ne aka naɗa a matsayin Shugaban ikilisiya. (Mat. 23:10; Afis. 5:23) Ya ba da wasu iko ga bawan nan mai aminci, wanda ya ƙunshi rukunin shafaffun Kiristoci masu aminci. Wannan rukunin yana naɗa masu kula a cikin ikilisiyar Kirista.—Mat. 24:45-47; Tit. 1:5-9.

Ta yaya za mu san rukunin wannan bawan mai aminci ko kuma wakilin bawa? Ka lura da yadda Yesu da kansa ya kwatanta shi: “Wanene fa wakili mai-aminci, mai-azanci, wanda ubangijinsa za ya sanya shi bisa iyalin gidansa, domin shi raba musu abincinsu a lotonsa? Wannan bawa mai-albarka ne wanda ubangijinsa, sa’anda ya zo, za ya iske shi yana yin hakanan.”—Luk 12:42, 43.

Saboda haka, rukunin wakilin nan “mai-aminci” ne da bai taɓa cin amana ko kuma yin watsi da Jehobah da Yesu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ko kuma mutanen Allah ba. Da yake rukuni “mai-azanci” ne, wannan wakilin yana nuna sanin ya kamata a ja-gorar aiki mai muhimmanci na wa’azin “bishara kuwa ta mulki” da kuma “almajirtarda dukan al’ummai.” (Mat. 24:14; 28:19, 20) Rukunin wakilin nan yana biyayya wajen rarraba abinci na ruhaniya mai kyau “a lotonsa” wanda ke gina jiki. Ana ganin alamar cewa Jehobah ya amince da rukunin bawan a yadda yake yi wa mutanensa albarka ta wajen sa adadin mutanensa su ƙaru da yadda yake ja-gorance su su tsai da shawarwari masu muhimmanci da yadda yake sa su fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai da yadda yake kāre su don kada magabtansu su halaka su da kuma yadda yake ba su kwanciyar hankali.—Isha. 54:17; Filib. 4:7.

Ka Bi Ja-gorar Allah

Ta yaya za mu nuna cewa muna godiya ga ja-gorar Allah? Manzo Bulus ya ce: “Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabanninku, ku sarayar da kanku gare su.” (Ibran. 13:17) Yin hakan ba zai kasance da sauƙi ba a ko da yaushe. Alal misali: A ce kai Ba’isra’ila ne a zamanin Musa. Kuma ka daɗe kana tafiya, sai umudin ya tsaya. Har tsawon wane lokaci ne zai kasance a wurin? Kwana ɗaya ne? Mako guda ne? Watanni da yawa ne? Kana mamaki, ‘Ya kamata na kwance dukan kayayyaki na ne?’ Wataƙila za ka fara kwance kayayyakin da suka fi amfani. Duk da haka, bayan ’yan kwanaki, ka gaji da neman kaya sai ka soma kwance kome. Amma, sa’ad da ka kusan ƙarasawa, sai ka ga umudin ya tashi, kuma sai ka soma tattara kayan kuma! Hakan ba zai kasance da sauƙi ba ko kuma da sukuni. Duk da haka, Isra’ilawa suna bukata su ‘yi tafiya” nan da nan.’—Lit. Lis. 9:17-22.

Yaya muke aikatawa sa’ad da muka samu umurni daga wurin Allah? Muna ƙoƙari mu yi amfani da shi ‘nan da nan’ ne? Ko kuwa muna ci gaba da yin abubuwa yadda muka saba yin su ne? Shin mun san da sababbin umurnin da aka ba da yanzu game da, gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida, yin wa’azi ga mutane da suke wani yare, saka hannu a bauta ta iyali a kai a kai, ba da haɗin kai ga Kwamitin Hulɗa da Asibitoci da kuma nuna hali mai kyau a tarurrukan gunduma? Muna kuma nuna cewa muna daraja ja-gorar Allah ta wurin amincewa da gargaɗi. Sa’ad da muke bukatar mu tsai da shawarwari masu muhimmanci, bai dace mu dogara ga hikimarmu ba amma mu dogara ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa don ja-gora. Kamar yadda yaro yake neman kāriyar iyayensa sa’ad da ake hadari, muna neman kāriya daga ƙungiyar Jehobah sa’ad da muke fuskantar matsalolin wannan duniya masu kama da hadari.

Hakika, waɗanda suke ja-gora a sashen ƙungiyar Allah na duniya ajizai ne kamar Musa na zamanin dā. Duk da haka, umudin ya ba da tabbacin cewa Allah ne ya naɗa Musa kuma yana da amincewar Allah. Ka kuma lura cewa, ba kowanne Ba’isra’ila ba ne zai yanke shawara a kan lokacin da za a soma tafiya ba. Maimakon hakan, mutanen sun aikata bisa “umurnin Ubangiji da ya yi wa Musa.” (Lit. Lis. 9:23) Da hakan, Musa ne Allah yake amfani da shi don ya ba da alama su soma tafiya.

A yau, rukunin wakilin Jehobah suna ba da alama a duk lokacin da ake bukatar canji. Ta yaya wakilin yake yin hakan? Ta wurin talifofin Hasumiyar Tsaro da Hidimarmu Ta Mulki da sababbin littattafai da kuma jawabai da ake ba da a manyan tarurruka da taron gunduma. Ana kuma ba da umurni ga ikilisiyoyi ta wurin masu kula masu ziyara ko kuma ta wurin wasiƙu ko kuma koyarwa da ake wa ’yan’uwa da suke da hakkoki a cikin ikilisiya.

Shin ka gane tabbacin cewa Allah yana ja-gora kuwa? A wannan kwanaki na ƙarshe, Jehobah yana yin amfani da ƙungiyarsa don ya ja-gorance mutanensa, ta muguwar duniyar Shaiɗan da ke kama da “jeji” mai haɗari sosai. Muna more haɗin kai da ƙauna da kwanciyar hankali a sakamakon hakan.

Sa’ad da Isra’ilawa suka isa Ƙasar Alkawari, Joshua ya ce: “Ku kuma kun sani cikin zukatanku duka da cikin rayukanku duka, babu wani abu ɗaya ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku.” (Josh. 23:14) Babu shakka, mutanen Allah za su isa sabuwar duniya da aka yi musu alkawarinta. Amma dai, ko za mu kasance a wurin ya dangana ga kasancewa a shirye mu bi ja-gorar Allah cikin tawali’u. Saboda haka, bari dukanmu mu ci gaba da ganin tabbaci cewa Jehobah yana ja-gora!

[Hotuna da ke shari na 5]

Ana mana ja-gora a yau ta ƙungiyar Jehobah

Littattafai da aka fito da su a taron gunduma

Makarantu na Tsarin Allah

Koyarwa a tarurruka don hidima

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba