Kada Ka Mance da Jehobah
WASU Isra’ilawa sun yi hakan a dā. Amma, ga yawancinsu wannan ne lokaci na farko kuma na ƙarshe da za su haye kogi kuma jikinsu bai jiƙe ba. Jehobah ya sa ruwayen Kogin Urdun ya daina gudu. A dogon layin jerin gwano, miliyoyin Isra’ilawa sun haye kogin zuwa Ƙasar Alkawari. Kamar kakanninsu shekaru 40 da suka shige a Jan Teku, mai yiwuwa mutane da yawa da suka haye Urdun sun yi tunani, ‘Ban zan taɓa manta abin da Jehobah ya yi a nan ba.’—Josh. 3:13-17.
Amma, Jehobah ya san cewa wasu Isra’ilawa za su “manta da ayukansa” da wuri. (Zab. 106:13) Saboda haka, ya ba Joshua, shugaban Isra’ila umurni cewa ya ɗauki duwatsu goma sha biyu daga tsakiyar kogin kuma ya ajiye su a masaukinsu na farko. Joshua ya bayyana: “Waɗannan duwatsu kuwa za su zama matuni ga ’ya’yan Isra’ila.” (Josh. 4:1-8) Waɗannan tarin duwatsu za su tuna wa al’ummar ayyukan Jehobah masu girma kuma su fahimci muhimmancin da ya sa ya kamata su ci gaba da bauta masa da aminci.
Wannan labarin yana da muhimmanci ne ga mutanen Allah a yau? E. Bai kamata mu ma mu manta da Jehobah ba, kuma dole ne mu ci gaba da bauta masa da aminci. Za a iya amfani da gargaɗin da aka ba Isra’ilawa ga bayin Jehobah a yau. Yi la’akari da kalmomin Musa: “Ka yi lura kada ka manta da Ubangiji Allahnka, da ba za ka kiyaye dokokinsa da shari’unsa, da farillansa.” (K. Sha 8:11) Hakan ya nuna cewa mance Jehobah zai sa mutum ya yi rashin biyayya ga Allah. Hakan yake a yau ma. Sa’ad da yake rubuta wa Kiristoci, manzo Bulus ya yi gargaɗi don irin “wannan misalin kangara” da Isra’ilawa suka nuna a cikin jeji.—Ibran. 4:8-11.
Bari mu yi la’akari da wasu abubuwa da suka faru a tarihin Isra’ila da suka nuna cewa bai kamata mu mance da Allah ba. Ƙari ga haka, misalin rayuwar mazan Isra’ilawa biyu masu aminci zai taimake mu mu bauta wa Jehobah da jimiri da kuma godiya.
Dalilan Tunawa da Jehobah
A dukan shekarun da Isra’ilawa suka yi a ƙasar Masar, Jehobah bai taɓa mancewa da su ba. Ya “tuna da alkawarinsa da Ibrahim, da Ishaƙu da Yaƙub.” (Fit. 2:23, 24) Abin da ya yi don ya ’yantar da su daga bauta abu ne da bai kamata su mance ba.
Jehobah ya bugi ƙasar Masar da annoba tara. Firistocin Fir’auna masu yin sihiri ba su da ƙarfin hana annobar. Duk da haka, Fir’auna ya raina Jehobah, ya ƙi ya ƙyale Isra’ilawa su tafi. (Fit. 7:14–10:29) Amma, sakamakon annoba na goma ya tilasta wa wannan sarki mai fahariya ya yi biyayya ga Allah. (Fit. 11:1-10; 12:12) Tare da Musa a matsayin shugaba, al’ummar Isra’ila da taron mutane da yawa, wataƙila wajen mutane miliyan uku ne suka bar ƙasar Masar. (Fit. 12:37, 38) Ba su daɗe da tafiya ba da Fir’auna ya canja zuciyarsa. Ya ba da umurni ga rundunar karusarsa da mahayansu, wato, runduna mafi ƙarfi a duniya a wannan lokacin, su sake kamo bayinsa na dā. Yayin nan kuma, Jehobah ya gaya wa Musa ya kai Isra’ilawa zuwa wani ƙaramin wuri tsakanin Jar Teku da tudun duwatsu, wurin da kamar ba za su tsira ba da ake kira Pihahiroth.—Fit. 14:1-9.
Fir’auna yana ganin cewa Isra’ilawa sun shiga cikin tarko, kuma rundunarsa suna gab da kai musu hari. Amma Jehobah ya ja Masarawa da baya ta wajen kafa umudi na gajimare da umudi na wuta tsakaninsu da Isra’ilawa. Sai Allah ya raba Jar Teku, ya buɗe wa ruwan tekun hanyar zubowa wataƙila har tsawon kafa hamsin a kowane gefe. Isra’ilawa suka soma haye tekun a busashiyar ƙasa. Ba da daɗewa ba Masarawa suka kai bakin tekun suna kallon Isra’ilawa suna hayewa zuwa ɗayan gefen.—Fit. 13:21; 14:10-22.
Shugaba mai wayo zai daina bin mutanen, amma Fir’auna bai yi hakan ba. Da yake yana ji da kansa sai ya umurci karusarsa da mahayansu su bi Isra’ilawa cikin ruwan. Masarawa suka ci gaba da binsu. Amma an tsayar da su kafin su kai ga Isra’ilawa. Karusan Masar ba sa iya tafiya kuma, Jehobah ya kwaɓe kafafunsu.—Fit. 14:23-25; 15:9.
Sa’ad da Masarawa suke fama da kafafun karusansu da aka kwaɓe, dukan Isra’ilawa suka kai bakin teku na gabas. Musa ya miƙa hannunsa bisa Jan Teku. Sai Jehobah ya sa ruwan ya koma yadda yake a dā. Ruwa mai yawan gaske ya cinye Fir’auna da rundunarsa. Babu wanda ya tsira cikin waɗannan magabta. Isra’ila ta samu ’yanci!—Fit. 14:26-28; Zab. 136:13-15.
Labarin wannan aukuwa ya sa al’ummai da suke kusa da wajen su ji tsoro na dogon lokaci. (Fit. 15:14-16) Bayan shekaru arba’in, Rahab na Jericho ta gaya wa mazan Isra’ila guda biyu: “Razanarku kuma ta kama mu, . . . mun ji yadda Ubangiji ya shanyadda ruwan Jan Teku a gabanku, lokacinda kuka fito Masar.” (Josh. 2:9, 10) Waɗannan al’ummai arna ba su manta ba da yadda Jehobah ya ceci mutanensa. Hakika, Isra’ila tana da ƙarin dalilai na tuna da shi.
‘Ya Kiyaye Su Kamar Ƙwayar Idonsa’
Bayan sun haye Jar Teku, Isra’ilawa sun shiga Hamada na Sinai “mai-ban tsoro.” Sa’ad da suke tafiya ta “ƙasa mai-ƙishi inda babu ruwa,” kuma babu abincin da mutanen nan masu yawa za su ci, Jehobah bai ƙyale su ba. Musa ya ce: “[Jehobah] ya iske [Isra’ila] a cikin ƙasa saimuwa, cikin hamada, ƙungurmin jeji; Ya kewaye shi, ya yi ɗawainiya da shi, ya kiyaye shi kamar ƙwayar idonsa.” (K. Sha 8:15; 32:10) Ta yaya Allah ya kula da su?
Jehobah ya ba su “abinci daga sama,” da ake kira manna, wadda ta fito ta mu’ujiza “a sararin jeji.” (Fit. 16:4, 14, 15, 35) Jehobah ya kuma sa ruwa ya fito “daga cikin [dutse] mai-ƙanƙara.” Da taimakon Allah, tufafinsu ba su tsufa ba, ƙafafunsu ba su kumbura ba a wannan shekara arba’in da suke cikin jeji. (K. Sha 8:4) Menene Jehobah yake bukata a garesu su? Musa ya gaya wa Isra’ila: “Ka yi lura da kanka, ka kiyaye ranka da ƙwazo, domin kada ka manta da al’amuran da idanunka suka gani, kada kuma su rabu da zuciyarka dukan kwanakin ranka.” (K. Sha 4:9) Idan Isra’ilawa suna tunawa da ayyukan ceto na Jehobah, a koyaushe za su bauta masa kuma su yi ƙoƙari su yi biyayya ga dokokinsa. Menene Isra’ila za ta yi?
Mantuwa Tana Jawo Rashin Godiya
Musa ya sanar: “Dutsen da ya haife ka ka yi biris da shi, kuma ka manta da Allah wanda ya faradda kai.” (K. Sha 32:18) Ba da daɗewa ba, sun mance da ayyukan Jehobah a Jar Teku, tanadin da ya yi don su kasance da rai a cikin jeji, da dukan abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi. Isra’ilawa suka zama masu tawaye.
A wani lokaci, Isra’ilawa sun zargi Musa domin suna ganin cewa babu yadda za su samu ruwa. (Lit. Lis. 20:2-5) Sun yi gunaguni game da manna da ta sa suka kasance da rai suna cewa: “Ranmu ya gundura da wannan mummunan abinci.” (Lit. Lis. 21:5) Sun yi shakkar ayyukan Allah kuma suka ƙi Musa a matsayin shugaba, suna cewa: “Da ma mun mutu cikin ƙasar Masar! da ma mun mutu cikin jejin nan! . . . Bari mu shugabantadda wani, mu koma Masar.”—Lit. Lis. 14:2-4.
Yaya Jehobah ya ji game da rashin biyayyar Isra’ilawa? Sa’ad da ya tuna game da waɗannan aukuwa, wani mai zabura ya rubuta: “So nawa suka tayar masa a cikin jeji, suka ɓata masa rai a cikin hamada! Suka juya suka jarabci Allah, suka cakuni Mai-tsarki na Isra’ila. Ba su tuna da hannunsa ba, ko kuwa rana da ya panshe su daga hannun abokin gaba ba. Yadda ya sanya alamunsa cikin Masar.” (Zab. 78:40-43) Hakika, mantuwar da Isra’ilawa suka yi ta sa Jehobah baƙin ciki sosai.
Mutane Biyu da ba Su Manta Ba
Akwai Isra’ilawan da ba su manta da Jehobah ba. Biyu daga cikinsu su ne Joshua da Kaleb. Suna cikin’yan lekan asiri goma sha biyu da aka aika zuwa Ƙasar Alkawari daga Kadesh-barnea. Goma sun ba da rahoto da ba shi da kyau, amma Joshua da Kaleb sun gaya wa mutanen: “Ƙasa wadda muka ratsa domin mu yi gewaya, kyakkyawar ƙasa ce ƙwarai. Idan Ubangiji ya ji daɗinmu, sai shi kawo mu ciki, shi ba mu ita; ƙasa mai-zuba da madara da zuma. Sai dai kada ku tayar ma Ubangiji.” Sa’ad da mutanen suka ji waɗannan kalaman, sun so su jefi Joshua da Kaleb da duwatsu. Amma, su biyu sun yi tsayin daka da gaba gaɗi ga Jehobah.—Lit. Lis. 14:6-10.
Shekaru daga baya, Kaleb ya gaya wa Joshua: “Musa bawan Ubangiji ya aike ni daga Kadesh-barnea, domin in yi gewayar ƙasar: na kuwa dawo masa da magana kamar yadda ta ke cikin zuciyata. Duk da haka ’yan’uwana da suka hau tare da ni suka sa zuciyar jama’a ta narke: amma ni na bi Ubangiji Allahna sosai.” (Josh. 14:6-8) Da yake sun dogara ga Allah, Kaleb da Joshua sun jimre da wahaloli dabam dabam. Sun ƙuduri aniya su tuna da Jehobah dukan kwanakin rayuwarsu.
Kaleb da Joshua sun kuma nuna godiya, sun fahimci cewa Jehobah ya cika alkawarinsa na yi wa mutanensa tanadin ƙasa mai dausayi. Hakika, ya kamata Isra’ilawa su yi godiya ga Jehobah domin shi ne ya kāre su. Joshua ya rubuta: “Ubangiji ya ba Isra’ila dukan ƙasa wadda ya rantse za ya bayas ga ubanninsu; . . . dukan alherin da Ubangiji ya yi zancensa ga gidan Isra’ila babu wani abin da ya sare: dukan abu ya tabbata.” (Josh. 21:43, 45) Ta yaya za mu nuna godiya kamar Kaleb da Joshua a yau?
Ka Nuna Godiya
Wani mutum mai tsoron Allah ya taɓa tambaya: “Me zan bayar ga Ubangiji sabili da dukan alherinsa a gareni?” (Zab. 116:12) Bashin da Allah yake binmu yana da yawa sosai saboda alherinsa, ja-gorarsa na ruhaniya a gare mu, da kuma hanyar ceto ta nan gaba da ya yi mana tanadinta, waɗannan abubuwa ne da ba za mu iya biya ba har abada. Hakika, ba za mu taɓa iya biyan Jehobah ba. Amma dukanmu muna iya nuna godiya.
Gargaɗin da Jehobah ya bayar sun taimake ka ka guji matsaloli? Gafararsa ta taimake ka ka sake samun lamiri mai tsabta? Waɗannan ayyukan na Allah suna da amfani na dogon lokaci, saboda haka, ya kamata ka ci gaba da yin godiya ga Allah. Wata yarinya ’yar shekara goma sha huɗu, mai suna Sandra ta fuskanci matsaloli masu tsanani amma ta sha kansu da taimakon Jehobah. Ta ce: “Na yi addu’a ga Jehobah don taimako, kuma yadda ya taimake ni ya burge ni. Yanzu na fahimci dalilin da ya sa babana sau da yawa yake mini magana game da Misalai 3:5, 6: ‘Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.’ Na tabbata cewa da yake Jehobah ya taimake ni har yanzu, zai ci gaba da taimako na.”
Ka Nuna Kana Tunawa da Jehobah ta Wajen Jimrewa
Littafi Mai Tsarki ya nanata wani hali da ke da nasaba da tunawa da Jehobah, ya ce: “Bari haƙuri shi cika aikinsa, domin ku kamilta, ku cika kuma, ba ragaggu ne cikin kome ba.” (Yaƙ. 1:4) Menene ‘kamilta, cika kuma, cikin kome’ ya ƙunsa? Ya ƙunshi koyan halaye da za su taimake mu mu fuskanci gwaji ta wajen dogara ga Jehobah da kuma ƙudurin jimre su, ban da yin kasala. Irin wannan jimiri yana kawo gamsuwa sosai sa’ad da gwajin bangaskiya ya ƙare. Kuma za su ƙare.—1 Kor. 10:13.
Wani bawan Jehobah da ya daɗe yana rashin lafiya mai tsanani ya bayyana abin da ya taimake shi ya jimre: “Na yi ƙoƙari na yi tunanin abin da Jehobah yake yi, ba abin da nake son na yi ba. Aminci yana nufin mai da hankali bisa nufe-nufen Allah, ba sha’awoyi na ba. Sa’ad da nake fuskantar matsaloli, ba na cewa, ‘Me ya sa hakan ya faru da ni, Jehobah?’ Na ci gaba kawai da bauta masa da kuma manne masa har a lokacin da matsala da ba na tsammani ta faɗo.”
A yau Kiristoci na gaskiya suna bauta wa Jehobah “cikin Ruhu da cikin gaskiya.” (Yoh. 4:23, 24) A matsayin rukuni, Kiristoci na gaskiya ba za su taɓa manta da Allah ba yadda al’ummar Isra’ila ta yi. Amma kasancewa cikin ikilisiya ba ya nufin cewa kowannenmu zai kasance da aminci. Kamar Kaleb da Joshua, dole ne kowannenmu ya nuna godiya da jimiri a hidimar Jehobah. Muna da dalili mai kyau na yin hakan, domin Jehobah yana ci gaba da yi mana ja-gora kuma yana kula da mu ɗaɗɗaya a wannan lokaci na ƙarshe mai wuya.
Kamar abin tunawa da Joshua ya kafa, ayyukan ceto na Allah sun tabbatar da mu cewa ba zai yasar da mutanensa ba. Saboda haka, bari ka ji yadda mai zabura ya ji, ya rubuta: “Zan tuna da al’ajibanka na dā. Zan yi ta bimbinin dukan aikinka, in yi maganar zuci a kan aike aikenka.”—Zab. 77:11, 12.
[Hotunan da ke shafi na 7]
Dukan al’ummar sun yi tafiya cikin “ƙasa mai-kishi”
[Credit Line]
Pictorial Archive (Near Eastern History) Est.
[Hotunan da ke shafi na 8]
Sa’ad da Isra’ila ta kafa sansani a Kadesh-barnea, an aika da ’yan lekan asiri zuwa cikin Ƙasar Alkawari
[Credit Line]
Pictorial Archive (Near Eastern History) Est.
[Hotunan da ke shafi na 9]
Bayan sun yi shekaru da yawa a cikin jeji, ya kamata Isra’ilawa su nuna godiya don Ƙasar Alkawari mai dausayi
[Credit Line]
Pictorial Archive (Near Eastern History) Est.
[Hotunan da ke shafi na 10]
Mai da hankali ga nufe-nufen Jehobah yana taimaka mana mu jimre duk wani ƙalubalen da muka fuskanta