Abin Da Ke Ciki
15 Ga Maris, 2011
Na Nazari
TALIFOFIN NAZARI NA MAKONNIN:
2-8 ga Mayu, 2011
Ka Karɓi Ruhun Allah ba na Duniya Ba
SHAFI NA 8
WAƘOƘI: 60, 71
9-15 ga Mayu, 2011
Ka Dogara ga Jehobah Yayin da Ƙarshe Ya Yi Kusa
SHAFI NA 12
WAƘOƘI: 125, 48
16-22 ga Mayu, 2011
SHAFI NA 24
WAƘOƘI: 54, 135
23-29 ga Mayu, 2011
Ka Yi Tsaro Yadda Irmiya Ya Yi
SHAFI NA 28
WAƘOƘI: 65, 43
Manufar Talifofin Nazari
TALIFIN NAZARI NA 1 SHAFUFFUKA NA 8-12
Zai yiwu mu kasance dabam da yake mutane da suke kusa da mu suna nuna ruhun duniya? Wannan talifin zai taimaka mana mu ga yadda ruhun duniya zai iya shafe mu. Za mu kuma tattauna abin da za mu koya daga misalin Yesu game da samun ruhun Allah.
TALIFIN NAZARI NA 2 SHAFUFFUKA NA 12-16
Mene ne yake nufi a dogara ga Jehobah? A wannan talifin, za mu ga cewa yana nufin fiye da a gaskata alkawuransa game da sabuwar duniya kawai. Ya ƙunshi amincewa da hanyoyinsa da mizanansa da dukan zuciyarmu yayin da muke ƙin na duniya.
TALIFOFIN NAZARI NA 3, 4 SHAFUFFUKA NA 24-32
Waɗannan talifofin za su nuna yadda Nuhu, da iyalinsa da Musa da kuma Irmiya suka kasance a shirye don su yi ayyukansu kuma za su zama shaidu ga cikar alkawuran Allah. Ka ga darussan da za ka iya koya daga waɗannan mazan da kuma halinsu.
A FITOWAR NAN
3 Kada Ka Ruɗi Kanka da Tunanin Ƙarya
17 Kana da Dalilin Yin Farin Ciki
20 Kada Ka Yasar da ’Yan’uwanka Masu Bi