Kada Ka Ruɗi Kanka da Tunanin Ƙarya
BAYAN Hauwa’u ta ci daga itacen da aka hana su ci, Allah ya tambaye ta: “Menene wannan da kin yi?” Sai ta amsa, “Macijin ya ruɗe ni, ni kuwa na ci.” (Far. 3:13) Bayan hakan, an kira Shaiɗan, wato, wanda ya sa Hauwa’u ta yi wa Allah rashin biyayya maciji mai wayo “tsohon macijin nan, . . . mai-ruɗin dukan duniya.”—R. Yoh. 12:9.
Wannan labarin Farawa ya nuna cewa Shaiɗan mai wayo ne, wanda yake ƙarya da niyyar ruɗun marar wayo. Babu shakka, ya ruɗi Hauwa’u. Duk da haka, bai kamata mu yi tunani ba cewa Shaiɗan kaɗai ne zai iya yaudarar mu. Littafi Mai Tsarki ya kuma ba da kashedi game da haɗarin ‘ruɗin kanmu da tunanin ƙarya.’—Yaƙ. 1:22.
Yana iya zama kamar ba zai yiwu mu ruɗi kanmu ba. Amma akwai dalilin da ya sa Allah ya ba da wannan kashedin. Saboda haka, yana da kyau mu yi la’akari da yadda za mu iya ruɗin kanmu da kuma irin tunanin ƙarya da zai iya yaudarar mu. Misali na Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana.
Abin da Za Mu Iya Koya Daga Waɗanda Suka Ruɗi Kansu
A misalin shekara ta 537 K.Z., Sairus Mai Girma na Ƙasar Farisa ya ba da doka cewa Yahudawa da suke zaman bauta a Babila su koma Urushalima don su sake gina haikalin. (Ezra 1:1, 2) A shekara ta gaba, daidai da nufin Jehobah, mutanen sun kafa harsashi don sabon haikali. Waɗanda suka dawo daga bautar sun yi farin ciki kuma sun yabi Jehobah don albarkarsa ga sashe na farko na aikin mai muhimmanci, wato, gina harsashin. (Ezra 3:8, 10, 11) Amma, ba da daɗewa ba, aka soma hamayya ga aikin gini da suke yi kuma mutanen suka yi sanyin gwiwa. (Ezra 4:4) Kusan shekara 15 bayan dawowarsu, hukumomin ƙasar Farisa suka hana dukan aikin gine-gine a Urushalima. Don a zartar da hanin, hukumomin yankin sun zo Urushalima kuma sun “sa [Yahudawa] su dena ƙarfi da yaji.”—Ezra 4:21-24.
Da yake suna fuskantar wannan tangarɗa mai tsanani, Yahudawa suka ruɗi kansu da tunanin ƙarya. Sun gaya wa kansu “lokaci ba ya yi ba, da za a gina gidan Ubangiji.” (Hag. 1:2) Sun kammala cewa Allah ba ya son a gina haikalin nan da nan. Maimakon su yi ƙoƙarin yin nufinsa, sun yasar da aikinsu mai tsarki kuma suka shagala wajen gyara gidajensu. Haggai, annabin Allah ya tambaye su: “Ko lokaci ya yi da ku da kanku za ku zauna ranku a kwance cikin gidajenku da aka yi da rufin ɗakunan da katako, bayan gidana [haikalin Jehobah] ta zama kango?”—Hag. 1:4.
Ka koyi wani darasi daga wannan misalin? Kasancewa da ra’ayin da bai dace game da nufin Allah zai iya sa mu manta da muhimmancin ayyukanmu na ruhaniya kuma mu ƙyale biɗe-biɗe na kanmu su raba hankalinmu. Alal misali, a ce kana jiran baƙi. Jiransu zai sa ka shagala wajen yin aikace-aikacen gida da yawa da suka dace game da zuwansu. Amma sai ka samu saƙo cewa baƙinka ba za su zo da wuri ba. Shin za ka daina shirye-shiryen da kake yi ne?
Ka tuna cewa Haggai da Zakariya sun taimaki Yahudawa su fahimci cewa har ila Jehobah yana son a sake gina haikalin babu ɓata lokaci. Haggai ya aririce su: “Ku yi ƙarfi, dukanku mutanen ƙasa, . . . ku yi aiki.” (Hag. 2:4) Suna bukatar su yi aikin da ke gabansu, suna kasance da tabbaci cewa ruhun Allah zai goyi bayansu. (Zak. 4:6, 7) Shin wannan misalin zai iya taimaka mana mu guji kammalawa da bai dace ba game da ranar Jehobah?—1 Kor. 10:11.
Musanya Tunanin Ƙarya da na Kirki
A wasiƙarsa ta biyu, manzo Bitrus ya yi la’akari da ma’ajin lokaci na Jehobah don ƙafa “sababbin sammai da sabuwar duniya.” (2 Bit. 3:13) Ya lura cewa wasu masu ba’a sun yi shakka ko Allah zai taɓa sa hannu a harkokin ’yan Adam. Sun faɗa cewa ba abin da zai faru, wai “dukan al’amura suna nan kamar yadda suke tun farkon halitta.” (2 Bit. 3:4) Bitrus yana son ya ƙaryata irin wannan tunanin ƙarya. Ya rubuta: “Ina daman sahihin hankalinku yayinda ni ke yi maku tuni.” Ya tuna wa Kiristoci masu bi cewa masu ba’an sun yi kuskure. Allah a dā ya sa hannu a harkokin ’yan Adam, ya kawo rigyawa da ta yi ɓarna sosai a dukan duniya.—2 Bit. 3:1, 5-7.
Haggai ya ba da irin wannan gargaɗi ga Yahudawa da suka yi sanyin gwiwa da kuma marasa ƙwazo a shekara ta 520 K.Z. Ya gargaɗe su: “Ku lura da al’amuranku.” (Hag. 1:5) Don ya sa su yi tunani, ya tuna wa ’yan’uwansa masu bi game da nufe-nufen Allah da alkawuransa ga mutanensa. (Hag. 1:8; 2:4, 5) Ba da daɗewa ba bayan ya ba da wannan gargaɗin, aka soma aikin gine-gine duk da cewa hukumomi sun hana aikin. Har ila, abokan gaba sun yi ƙoƙari su ɓata aikin ginin, amma ba su yi nasara ba. Aka cire hanin, kuma bayan shekara biyar aka gama haikalin.—Ezra 6:14, 15; Hag. 1:14, 15.
Mu Mai da Hankali a Kan Al’amuranmu
Kana ganin cewa za mu iya yin sanyin gwiwa sa’ad da matsaloli suka taso kamar Yahudawa da suke zamanin Haggai? Idan hakan ya faru, yana iya yi mana wuya mu kasance da himma ga wa’azin bishara. Mene ne zai iya sa mu yi sanyin gwiwa? Muna iya shan wahala domin rashin gaskiya na wannan zamanin. Ka yi tunanin Habakkuk, wanda ya furta: “Har yaushe zan yi kira, kai kuwa ba ka yarda ka ji ba? Ina tada murya gareka saboda zafin mugunta, kai kuwa ka ƙi yin ceto.” (Hab. 1:2) Domin abin da wasu za su iya ɗauka kamar jinkiri ne, wani Kirista zai iya rashin azancin gaggawarsa kuma ya mai da hankali ga rayuwar jin daɗi. Hakan yana faruwa da kai? Idan muna irin wannan tunanin, kanmu muke ruɗa. Yana da muhimmanci mu yi biyayya ga gargaɗi na Nassi na ‘mu lura da al’amuranmu’ kuma mu ta da ‘sahihin hankalinmu’! Muna iya tambayar kanmu, ‘Ya kamata na yi mamaki ne cewa wannan mugun zamani ya daɗe fiye da yadda nake tsammani?’
Littafi Mai Tsarki Ya Annabta Cewa Akwai Lokacin da Za a Yi Jira
Ka yi la’akari da kalaman Yesu game da ƙarshen wannan zamanin. Labarin Markus game da annabcin Yesu na kwanaki na ƙarshe ya nuna cewa Yesu a kai a kai ya gargaɗe mu mu yi tsaro. (Mar. 13:33-37) Mun ga irin wannan kashedi a cikin kwatanci na annabci na babbar ranar Jehobah a Armagedon. (R. Yoh. 16:14-16) Me ya sa aka yi wannan gargaɗi a kai a kai? Ana bukatar irin waɗannan gargaɗi saboda a sakamakon jiran abin da ke kama da dogon lokaci, mutane suna cikin kasadar rashin azancinsu na gaggawa.
Yesu ya ba da dalilin da ya sa za mu ci gaba da yin tsaro yayin da muke jiran ƙarshen wannan zamanin. Ya yi maganar maigida wanda ɓarayi sun shiga gidansa. Da mene ne zai yi don kada a shiga masa gida? Ta wajen kasancewa a faɗake dukan dare. Yesu ya kammala wannan kwatanci ta wajen yi mana gargaɗi: ‘Ku zama da shiri: gama cikin sa’an da ba ku sa tsammani ba Ɗan mutum yana zuwa.’—Mat. 24:43, 44.
Wannan kwatancin ya nuna bukatar mu kasance a shirye mu jira, ko da na dogon lokaci ne. Bai kamata mu damu ainun cewa wannan mugun zamani zai daɗe fiye da yadda muke tsammani ba. Bai kamata mu ruɗi kanmu da tunanin ƙarya cewa ‘lokacin Jehobah bai zo ba.’ Irin wannan tunanin zai sa ba za mu kasance da sha’awar yin wa’azin bisharar Mulki ba.—Rom. 12:11.
Kawar da Tunanin Ƙarya
Galatiyawa 6:7 tana ɗauke da ƙa’idar da ta shafi tunanin ƙarya, “Kada ku ɓata . . . iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe.” Idan ba a nome wata fage ba, ciyayi za su mamaye shi da sauri. Haka nan ma, idan ba mu yi hankali ba, za mu riƙa tunanin ƙarya. Alal misali, muna iya gaya wa kanmu, ‘Babu shakka ranar Jehobah tana zuwa, amma ba nan da nan ba.’ Irin wannan tunanin zai iya sa ba za mu kasance da ƙwazo ba game da ayyukanmu na tsarin Allah. Da shigewar lokaci, ƙwazonmu zai iya ragu, hakan zai sa mu yi ƙyuya. Ranar Jehobah za ta iya same mu babu shiri.—2 Bit. 3:10.
Amma, ba za mu riƙa tunanin ƙarya ba idan a ko da yaushe muna tabbatar wa kanmu cewa “nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke” ne. (Rom. 12:2) Karanta Kalmar Allah a kai a kai shi ne abin da zai fi taimaka mana wajen yin hakan. Nassosi za su iya ƙarfafa tabbacinmu cewa a ko da yaushe Jehobah zai zartar da adalcinsa a lokacin da ya dace.—Hab. 2:3.
Nazarinmu da addu’o’inmu da halartan taro a kai a kai da yin wa’azi, tare da ayyuka na alheri, za su taimaka mana mu ‘saurari ranar Jehobah.’ (2 Bit. 3:11, 12) Jehobah zai lura cewa muna hakan a kai a kai. Manzo Bulus ya tuna mana: “Kada mu yi kasala kuma cikin aikin nagarta: gama in lokaci ya yi za mu girbe, in ba mu yi suwu ba.”—Gal. 6:9.
Yanzu ba lokaci ba ne da za mu bar tunanin ƙarya ya ruɗe mu cewa ranar Jehobah tana jinkiri. Maimakon haka, yanzu ne za mu sa zuciyarmu ta yi ƙarfi, gama ranar Jehobah ta yi kusa.
[Hoton da ke shafi na 4]
Haggai da Zakariya sun aririce Yahudawa su yi gini
[Hoton da ke shafi na 5]
Idan maigidan ya san cewa ɓarawo zai shiga masa gida kuma fa?