Kana Ƙin Mugunta Kuwa?
‘Yesu ya ƙi mugunta.’—IBRAN. 1:9.
1. Mene ne Yesu ya koyar game da ƙauna?
DA YAKE bayyana muhimmancin ƙauna, Yesu Kristi ya gaya wa almajiransa: “Sabuwar doka na ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna. Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yoh. 13:34, 35) Yesu ya umurci mabiyansa su nuna ƙauna ta sadaukarwa ga junansu. Ƙaunar za ta zama alama da za a san su da ita. Yesu ya kuma aririce su: “Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a.”—Mat. 5:44.
2. Me ya kamata mabiyan Kristi su tsane?
2 Ƙari ga koya wa almajiransa game da ƙauna, Yesu ya koya musu abin da ya kamata su tsane. An ce game da Yesu: “Ka yi ƙaunar adalci, ka ƙi mugunta.” (Ibran. 1:9; Zab. 45:7) Wannan ya nuna cewa bai kamata mu so yin adalci kaɗai ba amma ya kamata mu ƙi zunubi, ko mugunta. Yana da muhimmanci da manzo Bulus ya ce: “Dukan wanda yake aika zunubi yana ƙetaren shari’a kuma: zunubi shi ne ƙetaren shari’a.”—1 Yoh. 3:4.
3. Game da ƙin mugunta, waɗanne hanyoyin rayuwa ne wannan talifin zai tattauna?
3 A matsayin Kiristoci, ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Ina ƙin mugunta kuwa?’ Bari mu tattauna yadda za mu iya tsane abu marar kyau a waɗannan hanyoyi huɗu na rayuwa: (1) ra’ayinmu game da shan barasa yadda bai dace ba, (2) ra’ayinmu game da sihiri, (3) ra’ayinmu game da lalata, da (4) ra’ayinmu game da waɗanda suke son mugunta.
Kada Ka Zama Bawa ga Barasa
4. Me ya sa Yesu yake da ’yancin yin magana sa’ad da yake ba da gargaɗi game da yin maye?
4 Yesu ya sha ruwan inabi a wasu lokatai, yana ɗaukansa a matsayin baiwa daga wurin Allah. (Zab. 104:14, 15) Amma dai, bai taɓa ɓata wannan baiwar ba ta yin maye. (Mis. 23:29-33) Saboda haka Yesu yana da ’yancin yin magana sa’ad da yake magana game da irin wannan halin. (Karanta Luka 21:34.) Yin maye da barasa zai iya kai ga zunubai da yawa masu tsanani. Saboda haka, manzo Bulus ya rubuta: “Kada ku yi maye da ruwan anab kuma-cikinsa da hauka-amma ku cika da Ruhu.” (Afis. 5:18) Ya kuma aririce mata tsofaffi a cikin ikilisiya kada su zama bayi ga “yawan ruwan anab.”—Tit. 2:3.
5. Ya kamata waɗanda suka yanki shawarar shan barasa su yi wa kansu waɗanne tambayoyi?
5 Idan ka yanka shawara ka riƙa shan barasa, zai dace ka tambayi kanka: ‘Shin ina da ra’ayin Yesu game da yin maye da barasa? Idan ina so na yi wa mutane gargaɗi game da wannan batun, zan kasance da ’yancin yin magana kuwa? Ina shan barasa ne don na manta da alhini na ne? Kwalaben barasa nawa ne nake sha kowanne mako? Yaya nake aikatawa sa’ad da wani ya gaya mini cewa ba na shan barasa daidai wa daida? Shin ina yin fushi ne?’ Ƙyale kanmu mu zama bayin barasa zai iya shafan ingancinmu na yin tunani a kan abubuwa yadda ya dace da kuma yin zaɓi masu kyau. Ya dace mabiyan Kristi su yi ƙoƙari su kiyaye ingancinsu na yin tunani.—Mis. 3:21, 22.
Ku Ƙi Ayyukan Sihiri
6, 7. (a) Yaya Yesu ya bi da Shaiɗan da kuma aljanu? (b) Me ya sa ayyukan sihiri sun yaɗu sosai a yau?
6 Sa’ad da yake duniya, Yesu ya tsayayya wa Shaiɗan da aljanu sosai. Ya ƙi farmakin da Shaiɗan ya kai wa amincinsa. (Luk 4:1-13) Ya sani kuma ya tsayayya wa ƙananan hanyoyi da ya yi amfani da su don ya gurɓatar da tunaninsa da kuma ayyukansa. (Mat. 16:21-23) Yesu ya taimaki waɗanda suka cancanta su fita daga ikon aljanu.—Mar. 5:2, 8, 12-15; 9:20, 25-27.
7 Bayan an naɗa Yesu a matsayin Sarki a shekara ta 1914, ya tsabtace sammai daga gurɓatar Shaiɗan da aljanu. A sakamako, Shaiɗan ya ƙudurta fiye da dā ya ‘ruɗi dukan duniya.’ (R. Yoh. 12:9, 10) Bai kamata mu yi mamaki ba cewa marmarin saka hannu a sihiri yana daɗa yaɗuwa. Waɗanne matakai ne ya kamata mu ɗauka don mu kāre kanmu?
8. Wane binciken kai ne ya kamata mu yi game da nishaɗin da muka zaɓa?
8 Littafi Mai Tsarki ya ba da gargaɗi game da haɗarin da ke tattare da sihiri. (Karanta Kubawar Shari’a 18:10-12.) A yau, Shaiɗan da aljanu suna rinjayar tunanin mutane ta fina-finai, littattafai, da wasannin bidiyo da suke ɗaukaka ayyukan sihiri. Sa’ad da muke zaɓar nishaɗi da za mu yi, ya kamata kowannenmu ya tambayi kansa: ‘A watanni da suka wuce, shin na kalli fina-finai, wasannin talabijin, wasannin bidiyo, littattafai, ko kuwa wasanni masu ban dariya da suke nuna ayyukan sihiri? Na fahimci muhimmancin ƙin rinjayar sihiri, ko dai ba na ɗaukansu da muhimmanci? Shin na taɓa tunani a kan yadda Jehobah zai ji game da nishaɗin da na zaɓa? Idan ina saka hannu a waɗannan ayyukan sihiri, shin ƙauna ta ga Jehobah da mizanansa na adalci za su motsa ni na ɗauki mataki kuma na ƙi waɗannan ayyukan?’—A. M. 19:19, 20.
Ka Bi Gargaɗin Yesu Game da Lalata
9. Ta yaya ƙaunar mugunta za ta iya yaɗu a zuciyar mutum?
9 Yesu ya ɗaukaka mizanin Jehobah game da lalata ta jima’i. Ya ce: “Ba ku karanta ba, shi wanda ya yi su tun farko, namiji da tamata ya yi su, har ya ce, saboda wannan namiji za ya bar ubansa da uwatasa shi manne wa matatasa; su biyu kuwa za su zama nama ɗaya? Ya zama fa daga nan gaba su ba biyu ba ne, amma nama ɗaya ne. Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Mat. 19:4-6) Yesu ya san cewa abin da idanunmu suka gani zai iya shafar zuciyarmu. Saboda haka, a Huɗubarsa a kan Dutse, ya ce: “Kun ji aka faɗi, Ba za ka yi zina ba: amma ni ina ce muku, dukan wanda ya dubi mace har ya yi sha’awarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” (Mat. 5:27, 28) Hakika, waɗanda suka yi watsi da gargaɗin Yesu suna ƙaunar mugunta.
10. Ka ba da labari da ya nuna cewa mutum zai iya daina kallon hotunan batsa.
10 Shaiɗan yana ɗaukaka lalata ta jima’i ta hanyar hotunan batsa. Zamanin nan yana cike da su. Yana yi wa waɗanda suke kallon hotunan batsa wuya su share hotunan da suka ga daga zuciyarsu. Suna iya sabawa da hotunan batsa. Ka yi la’akari da abin da ya faru da wani Kirista. Ya ce: “Na kalli hotunan batsa a asirce. Na kasance a cikin wata duniya da nake tunani cewa ba ta da nasaba da duniya inda nake bauta wa Jehobah. Na san cewa wannan halin ba shi da kyau, amma na gaya wa kaina cewa har ila Allah yana amincewa da bauta ta.” Mene ne ya canja ra’ayin wannan ɗan’uwan? Ya ce: “Ko da yake abu mafi wuya ne da na taɓa yi, na tsai da shawara na gaya wa dattawa matsala ta.” Daga baya wannan ɗan’uwan ya daina wannan mummunar hali. “Bayan na daina wannan zunubin,” ya ce, “Na ji cewa ina da lamiri mai tsabta na gaske.” Ya kamata waɗanda suka tsani mugunta su koya yadda ake ƙin hotunan batsa.
11, 12. Ta yaya za mu iya nuna cewa mun tsane mugunta idan ya zo ga zaɓan kaɗe-kaɗe?
11 Kaɗe-kaɗe da kuma kalmominta za su iya shafan tunaninmu sosai, da kuma zuciyarmu ta alama. Kiɗa da kanta baiwa ce daga wurin Allah kuma an daɗe ana amfani da ita a bauta ta gaskiya. (Fit. 15:20, 21; Afis. 5:19) Amma muguwar duniyar Shaiɗan tana gabatar da kiɗa da ke ɗaukaka lalata. (1 Yoh. 5:19) Ta yaya za ka iya sanin cewa kiɗar da kake ji tana ɓata ka ko a’a?
12 Za ka iya somawa ta tambayar kanka: ‘Shin kaɗe-kaɗen da nake saurarawa suna ɗaukaka kisa, zina, fasikanci, da saɓo? A ce ina so na karanta wa wani kalmomin kaɗe-kaɗen, shin mutumin zai yi tunani cewa ina ƙin mugunta, ko kuwa kalmomin za su nuna cewa zuciyata tana da dauɗa?’ Ba za mu iya tsane mugunta da baki ba amma muna ɗaukaka ta a kiɗa. “Abubuwan da ke fita daga baki, daga zuciya su ke fitowa,” in ji Yesu, kuma “su ne masu ƙazamtar da mutum. Gama daga cikin zuciya miyagun tunani ke fitowa, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, alfasha.”—Mat. 15:18, 19; Yaƙ. 3:10, 11.
Ka Bi Ra’ayin Yesu Game da Waɗanda Suke Son Mugunta
13. Ta yaya Yesu ya ɗauki waɗanda suke zunubi da ba su tuba ba?
13 Yesu ya ce ya zo wurin dukan masu zunubi, ko masu mugunta domin su tuba. (Luk 5:30-32) Ta yaya ya ɗauki waɗanda zuciyarsu ta yi tauri sosai saboda zunubi? Yesu ya ba da gargaɗi game da ƙyale waɗannan su rinjaye mu. (Mat. 23:15, 23-26) Ya kuma ce dalla-dalla: “Ba dukan mai-ce mani, Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga cikin mulkin sama ba; sai wanda ke aikata nufin Ubana wanda ke cikin sama. A cikin wannan rana [sa’ad da Allah zai yi hukunci] mutane dayawa za su ce mani, Ubangiji, Ubangiji, ba mu yi annabci da sunanka ba, da sunanka kuma muka fitarda aljanu, da sunanka kuma muka yi ayyuka dayawa masu-iko?” Amma dai, zai ƙi waɗanda suke yin mugunta ba tare da tuba ba, yana cewa: Ku “rabu da ni.” (Mat. 7:21-23) Me ya sa hukuncinsu zai kasance haka? Domin waɗannan suna raina sunan Allah kuma suna la’anta wasu ta miyagun ayyukansu.
14. Me ya sa ake cire masu zunubi da ba su tuba ba daga cikin ikilisiya?
14 Kalmar Allah ta ba da umurni cewa a cire masu zunubi da ba su tuba ba daga cikin ikilisiya. (Karanta 1 Korintiyawa 5:9-13.) Hakan yana da muhimmanci don aƙalla dalilai uku: (1) don a tsabtace sunan Jehobah daga zargi, (2) don kāre ikilisiya daga gurɓatarwa, da (3) don taimaka wa masu zunubi su yi tuba idan zai yiwu.
15. Idan muna son mu kasance da aminci ga Jehobah, waɗanne muhimman tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?
15 Shin muna da ra’ayin Yesu game da waɗanda zuciyarsu ta yi tauri a yin mugunta? Ya kamata mu yi tunani a kan waɗannan tambayoyin: ‘Zan zaɓa in riƙa yin tarayya kullum da wanda aka yi wa yankan zumunci ko wanda ya ware kansa daga ikilisiyar Kirista? Shin idan wannan dangi na ne wanda ba ma zama a gida ɗaya kuma fa?’ Irin wannan yanayin zai iya gwada yadda muke ƙaunar adalci da kuma amincinmu ga Allah.a
16, 17. Wane yanayi mai wuya ne wata ’yar’uwa ta fuskanta, kuma mene ne ya taimake ta ta yi biyayya ga shirin yi wa mai zunubi da bai tuba ba yankan zumunci?
16 Ka yi la’akari da misalin wata ’yar’uwa wadda ɗanta da ya yi girma yana ƙaunar Jehobah a dā. Daga baya, ya zaɓa ya yi miyagun ayyuka ba tare da tuba ba. A sakamako, aka masa yankan zumunci daga ikilisiya. ’Yar’uwarmu tana ƙaunar Jehobah, amma tana kuma ƙaunar ɗanta, hakan ya kuma kasance mata da wuya ta bi shawarar Nassi na ƙin yin tarayya da shi.
17 A ce kana wurin, da wace shawara ce za ka ba wannan ’yar’uwar? Wani dattijo ya taimake ta ta fahimci cewa Jehobah ya fahimci baƙin cikin da take yi. Ɗan’uwan ya sa ta yi tunani a kan baƙin cikin da Jehobah ya yi sa’ad da wasu cikin mala’ikunsa suka yi tawaye. Dattijon ya tattauna da ita cewa ko da Jehobah ya san irin baƙin cikin da take yi, amma yana son a yi wa masu zunubi da ba su tuba ba yankan zumunci. Ta karɓi tunasarwar kuma ta yi biyayya da shirin yi wa mutum yankan zumunci.b Irin wannan amincin yana faranta zuciyar Jehobah.—Mis. 27:11.
18, 19. (a) Ƙin yin tarayya da wanda yake mugunta ya nuna cewa mun tsane mene ne? (b) Wane sakamako ne za mu iya samu don kasancewa da aminci ga shirin Allah?
18 Idan ka fuskanci irin wannan yanayin, ka tuna cewa Jehobah ya san yadda kake ji. Ta ƙin yin tarayya da wanda aka yi wa yankan zumunci ko wanda ya ware kansa, kana nuna cewa ka tsane hali da ayyukan da suka sa wannan ya faru da shi. Amma dai, kana nuna cewa kana ƙaunar mai zunubin kuma kana yin abin da ya dace da shi ko ita. Kasancewa da aminci ga Jehobah zai sa wanda aka yi wa horo ya gaggauta yin tuba kuma ya komo ga Jehobah.
19 Wata da aka wa yankan zumunci kuma aka sake dawowa da ita ta rubuta: “Ina farin ciki don ƙaunar da Jehobah yake wa mutanensa sosai ne ya sa yake tsabtace ƙungiyarsa. Abin da mutanen da ba sa cikin ƙungiyar za su ɗauka kamar rashin tausayi yana da muhimmanci sosai.” Kana zato cewa da wannan matar ta yi wannan kammalawar da a ce ’yan’uwa a cikin ikilisiya, haɗe da iyalinta sun ci gaba da yin cuɗanya da ita sa’ad da aka mata yankan zumunci? Yin biyayya ga tsarin Nassi na yi wa mutum yankan zumunci yana nuna cewa muna ƙaunar adalci kuma muna sane da ikon Jehobah na kafa mizanai game da ɗabi’a.
“Ku Ƙi Mugunta”
20, 21. Me ya sa yake da muhimmanci mu koyi ƙin mugunta?
20 Manzo Bitrus ya ba da gargaɗi: “Ku yi hankali shinfiɗe, ku yi zaman tsaro.” Don me? “Magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” (1 Bit. 5:8) Shin za ka kasance wannan da zai cinye? Hakan ya dangana ga yadda ka koya ƙin mugunta.
21 Ƙin mugunta ba shi da sauƙi. An haife mu cikin zunubi, kuma muna rayuwa a duniya da ke ƙarfafa mu mu bi sha’awoyinmu. (1 Yoh. 2:15-17) Ta yin koyi da Yesu Kristi da kuma yin ƙaunar Jehobah Allah sosai, za mu iya yin nasara wajen ƙin mugunta. Bari mu ƙuduri aniya mu “ƙi mugunta,” muna kasancewa da gaba gaɗi cewa Jehobah “mai-kiyayar da . . . tsarkakansa ne; yana fishe su daga hannun masu-mugunta.”—Zab. 97:10.
[Hasiya]
a Don tattaunawa dalla-dalla a kan wannan batun, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 1981 na Turanci, shafuffuka na 26-31.
b Ka kuma duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 2007 na Turanci, shafuffuka na 17 zuwa 20.
Yaya Za Ka Amsa?
• Mene ne zai taimaka mana mu bincika ra’ayinmu game da barasa?
• Waɗanne matakai ne za mu iya ɗauka don mu kāre kanmu daga sihiri?
• Me ya sa hotunan batsa suke da haɗari?
• Yaya za mu nuna cewa mun tsane mugunta sa’ad da aka yi wa wanda muke ƙauna yankan zumunci?
[Hoton da ke shafi na 29]
Idan ka tsai da shawara cewa kana son ka sha barasa, mene ne ya kamata ka yi la’akari da shi?
[Hoton da ke shafi na 30]
Ka mai da hankali da rinjayar Shaiɗan a nishaɗi
[Hoton da ke shafi na 31]
Mai kallon hotunan batsa yana ƙaunar me?