Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 2/15 pp. 3-5
  • Ku Koya wa Yaranku Yin Ladabi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Koya wa Yaranku Yin Ladabi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yara Suna Koyan Halaye Masu Kyau da Suka Gani
  • Ku Koyar da Misalan Littafi Mai Tsarki
  • Nuna Halin Kirki A Matsayin Masu Hidima Ta Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ya Jimre Har Zuwa Karshe
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Allahnsa Ya Ƙarfafa Shi
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Mu Riƙa Daraja Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 2/15 pp. 3-5

Ku Koya wa Yaranku Yin Ladabi

WANI ƙarin magana na ƙasar Jamus ya ce: “Idan mutum ya riƙe hularsa a hannu, zai iya zagaya garin baki ɗaya.” A al’adu da yawa, ana ɗaukan mutumin da ya cire hularsa kafin ya shiga gidan mutum ko kuma gaisawa da wani a matsayin ladabi. Saboda haka, ƙarin magana da aka ambata a sama yana nufin cewa mutane sun fi kasancewa da kirki ga waɗanda suke da kan gado.

Abin farin ciki ne sosai idan matasa suna da halaye masu kyau! Wani mai kula da da’ira a ƙasar Honduras wanda yake fita hidimar fage tare da masu shela yara da manya ya ce, “Na lura cewa yaro mai hankali sosai da kuma ladabi yana taɓa zuciyar masu gida sosai fiye da kalaman da nake furta wa masu gida.”

A zamaninmu da rashin ladabi yake daɗa yaɗuwa, sanin yadda za mu bi da mutane yana da muhimmanci. Fiye da hakan, Nassosi sun aririce mu mu “yi irin zaman da ya cancanci bisharar Kristi.” (Filib. 1:27; 2 Tim. 3:1-5) Yana da muhimmanci mu koya wa yaranmu su riƙa yi wa mutane ladabi. Ta yaya za a iya koya musu su riƙa yin ladabi na gaske ba kawai don mutane su gani ba?a

Yara Suna Koyan Halaye Masu Kyau da Suka Gani

Yara suna koyo ta bin misalin abubuwan da suka lura. Saboda haka, hanya mafi kyau da iyaye za su iya koya wa yaransu halaye masu kyau ita ce ta kasancewa da hali mai kyau. (K. Sha 6:6, 7) Yi wa yaronka magana game da ladabi yana da muhimmanci, amma ba shi ke nan ba. Tunasarwa da kuma kafa misali mai kyau suna da muhimmanci sosai.

Ka yi la’akari da misalin Paula,b wadda iyaye gwauruwa Kirista ce ta rene ta. Kasancewa da ladabi ga kowa ya zama halinta na yau da kullum. Me ya sa? Ta amsa, “Mahaifiyarmu ta nuna mana misali mai kyau, saboda haka yin ladabi ya zama halinmu.” Wani Kirista mai suna Walter ya koya wa yaransa su yi wa mahaifiyarsu da ba mai bi ba ce ladabi. Ya ce, “Na koya wa yarana ta misali na su riƙa yi wa mahaifiyarsu ladabi, wato, ban taɓa baƙar magana game da ita ba.” Walter ya ci gaba da yin amfani da Kalmar Allah don koyar da yaransa, kuma ya yi addu’a ga Jehobah don ya taimake shi. Ɗaya cikinsu yana hidima a ofishin reshe na Shaidun Jehobah yanzu, kuma na biyun majagaba ne. Yaransa suna ƙauna da kuma yi wa iyayensu ladabi.

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba Allah na yamutsai ba ne, amma na kwanciyar rai ne.” (1 Kor. 14:33) Dukan abin da Jehobah ya yi yana da tsari mai kyau. Ya kamata Kiristoci su yi ƙoƙarin yin koyi da wannan hali mai kyau kuma su riƙa tsabtace gidajensu. Wasu iyaye sun koyar da yaransu su riƙa gyara gadonsu kullum kafin su tafi makaranta, su riƙa ajiye tufafinsu yadda ya dace, kuma su riƙa yin aikace-aikacen gida. Idan yara sun lura da yadda yanayin wasu ɗakunan da ke gidan suke da tsabta da kyau sosai, hakan zai motsa su su sa ɗakunansu su kasance masu tsabta.

Ta yaya yaranku suke ɗaukan abin da suke koya a makaranta? Shin suna nuna godiya ga abin da malamansu suke musu kuwa? A matsayin iyaye, kuna nuna irin wannan godiyar kuwa? Yaranku za su bi ra’ayinku na yadda kuke ɗaukan ayyukan makaranta da kuma malamai. Zai dace ku ƙarfafa su su riƙa yi wa malamansu godiya. Yin godiya don abin da aka yi mana hanya ce mai kyau na nuna biyayya, ko ga malami, likita, mai kanti, ko kuma ga ko waye. (Luk 17:15, 16) Muna yaba wa Kiristoci matasa waɗanda suka kasance dabam da tsaransu a makaranta domin suna da ladabi da kuma kan gado sosai.

Ya kamata ’yan’uwa a cikin ikilisiya su kafa misali mai kyau idan ya zo ga batun halaye masu kyau. Abu mai kyau ne a ga matasa da suke tarayya da ikilisiya suna nuna halaye masu kyau ta wajen cewa “don Allah” da kuma “na gode”! Idan manya sun yi ladabi ga Jehobah ta saurarawa ga umurnin da aka ba da a tarurruka, hakan zai ƙarfafa yara su yi koyi da su. Yara suna iya koyon yi wa maƙwabtansu ladabi ta wajen lura da misali mai kyau da ake yi a Majami’ar Mulki. Alal misali, Andrew mai shekara huɗu ya riga ya koya yadda ake cewa, “Don Allah zan wuce,” sa’ad da yake son ya wuce manya.

Mene ne kuma iyaye za su iya yi don su taimaki yaransu su san irin halin da ya kamata su kasance da shi? Iyaye za su iya kuma ya kamata su ɗauki lokaci don koya wa yaransu darussa masu yawa da suke cikin Kalmar Allah.—Rom. 15:4.

Ku Koyar da Misalan Littafi Mai Tsarki

Babu shakka mahaifiyar Sama’ila ta koya masa ya riƙa rusuna wa Babban Firist Eli. Sa’ad da ta kai Sama’ila mazaunin, wataƙila shi ɗan shekara uku ko huɗu ne. (1 Sam. 1:28) Shin za ku iya gwada da ƙananan yaranku gaisuwa kamar su “barka da safiya” da “barka da rana” da “barka da yamma” ko kuma irin gaisuwa da ta fi dacewa a yankinku? Kamar Sama’ila matashi, yaranku ma za su iya samun “tagomashi a wurin Ubangiji duk da mutane.”—1 Sam. 2:26.

Zai dace ka yi amfani da labaran Littafi Mai Tsarki don ka nanata bambancin da ke tsakanin ladabi da rashin ladabi. Alal misali, sa’ad da Ahaziah, Sarki marar aminci na Isra’ila yake son ya ga annabi Iliya, ya tura ‘shugaban yaƙi da mutanensa hamsin’ su kira shi. Shugaban ya gaya wa annabin ya bi shi. Bai dace a yi wa wakilin Allah magana haka ba. Mene ne Iliya ya ce? “Idan ni mutumin Allah ne” in ji shi “bari wuta ta sauko daga sama, ta cinye ka duk da hamsin ɗin naka.” Kuma hakan ya faru. “Wuta kuwa ta sauko daga sama, ta cinye shi da hamsin ɗin nasa.”—2 Sar. 1:9, 10.

Aka sake tura wani shugaban yaƙi na mutum hamsin ya taho da Iliya. Shi ma ya yi ƙoƙari ya ba Iliya umurni ya bi shi. Kuma wuta ta sake saukowa daga sama. Amma kuma shugaban yaƙi na hamsin na uku ya zo ya sami Iliya. Wannan mutum ya nuna ladabi. Amma, maimakon ya umurci Iliya ya bi shi, ya durƙusa a gabansa kuma ya roƙe shi: “Ya mutumin Allah, ina roƙonka, ka ba raina da ran hamsin nan bayinka ya zama abin kiyayewa a idanunka. Ga shi, wuta ta sauko daga sama, ta cinye waɗancan shugabannai na hamsin tare da hamsin ɗin nasu: amma yanzu ka bar raina ya zama abin kwarjini a gabanka.” Annabin Allah zai ce wuta ta sauko ta cinye mutumin da ya ji tsoro kuma ya yi magana da ladabi? Ba zai yi haka ba! Maimakon hakan, mala’ikan Jehobah ya gaya wa Iliya ya tafi da wannan shugaban. (2 Sar. 1:11-15) Shin hakan bai nanata amfanin nuna ladabi ba?

Sa’ad da sojojin Roma suka tsare Bulus a haikali, bai yi tsammani ba cewa yana da ikon yin magana. Cikin ladabi ya tambayi sarkin yaƙin: “Ko ka yarda in yi magana da kai?” A sakamakon haka, aka ba Bulus zarafin yin magana don ya kāre kansa.—A. M. 21:37-40.

An mare Yesu sa’ad da yake fuskantar gwaji. Amma, Yesu ya san yadda ya dace a riƙa ba da amsa: “Idan na yi muguwar magana, sai ka shaida mugunta; amma idan mai-kyau ce, don me ka ke mārina?” Babu wanda zai iya ganin laifin yadda Yesu ya yi magana.—Yoh. 18:22, 23.

Kalmar Allah ta kuma ba da misalan yadda ya kamata mu aikata sa’ad da aka mana gargaɗi da kuma yadda za mu amince cikin ladabi wani laifi da muka yi a dā. (Far. 41:9-13; A. M. 8:20-24) Alal misali, Abigail ta roƙi gafara don raini da mijinta Nabal, ya yi wa Dauda. Ƙari ga roƙon gafara, ta ba Dauda abinci da yawa. Abin da Abigail ta yi ya burge Dauda sosai da har ya aure ta bayan mutuwar Nabal.—1 Sam. 25:23-41.

Ku koya wa yaranku yin ladabi, ko idan suna bukatar yin hakan sa’ad da suke fuskantar gwaji ko kuma sa’ad da suke hakan don nuna halin kirki kawai. ‘Barin haskenmu ya haskaka a gaban mutane’ ta wannan hanya yana ‘girmama Ubanmu wanda ke cikin sama.’—Mat. 5:16.

[Hasiya]

a Hakika, iyaye suna bukatar su taimaki yaransu su ga bambancin da ke tsakanin kasancewa da ladabi ga manya da kuma ba da kai ga wani wanda zai iya yi musu lahani. Ka duba babi na 32 na littafin nan Ka Koya Daga Wurin Babban Malami.

b An canja wasu sunaye.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba