Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Satumba pp. 14-19
  • Mu Riƙa Daraja Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mu Riƙa Daraja Mutane
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MENE NE DARAJA MUTANE YA ƘUNSA?
  • MU RIƘA DARAJA ꞌYAN IYALINMU
  • MU RIƘA DARAJA ꞌYANꞌUWANMU KIRISTOCI
  • MU RIƘA DARAJA WAƊANDA BA SA BAUTA WA JEHOBAH
  • Kana Girmama Mutane Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Me Ya Sa Ya Dace Mu Rika Yin Biyayya?
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Me Ya Sa Za a Girmama Hukuma?
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Kana A Kan Gaba Wajen Girmama ’Yan’uwa Masu Bi Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Satumba pp. 14-19

TALIFIN NAZARI NA 38

WAƘA TA 120 Mu Koyi Nuna Sauƙin Kai Kamar Yesu

Mu Riƙa Daraja Mutane

“Gwamma zama wanda ake darajawa da samun azurfa da zinariya.”—K. MAG. 22:​1, NWT.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga dalilin da sa muke bukatar mu riƙa daraja mutane. Da kuma yadda za mu daraja su ko da yin hakan yana da wuya.

1. Me ya sa ꞌyanꞌadam suke so a daraja su? (Karin Magana 22:1)

KANA jin daɗi idan mutane suka daraja ka? Babu shakka kana yin hakan. Kowane ɗanadam yana so a daraja shi kuma hakan yakan kawo farin ciki. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwamma zama wanda ake darajawa da samun azurfa da zinariya”!—Karanta Karin Magana 22:​1, NWT.a

2-3. Me ya sa yake mana wuya mu daraja mutane a wasu lokuta, kuma mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 A wasu lokuta, ba ya yi mana sauƙi mu daraja mutane. Me ya sa? Domin muna ganin kurakurensu. Ban da haka ma, muna rayuwa ne a lokacin da mutane da yawa ba sa daraja kowa. Amma ya kamata mu fita dabam, domin Jehobah yana so mu riƙa daraja da kuma girmama “kowa.”—1 Bit. 2:17.

3 A wannan talifin, za mu ga abin da daraja mutane ya ƙunsa da yadda za mu daraja (1) ꞌyan iyalinmu, (2) ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci da kuma (3) mutanen da ba sa bauta wa Jehobah. Za mu mai da hankali ga yadda za mu daraja mutane ko da yin hakan yana da wuya sosai.

MENE NE DARAJA MUTANE YA ƘUNSA?

4. Mene ne daraja mutane ya ƙunsa?

4 Daraja mutane ya ƙunshi yadda muke ɗaukan su, da yadda muke bi da su. Idan muka ga cewa mutum yana da halaye masu kyau, ko ya yi abubuwa masu burgewa, ko kuma yana da iko a kanmu, muna bi da shi a hanyar da za ta nuna cewa muna daraja shi. Yin hakan ba laifi ba ne musamman idan muna yin sa da zuciya ɗaya.—Mat. 15:8.

5. Mene ne zai taimaka mana mu daraja mutane?

5 Jehobah yana so mu riƙa daraja mutane. Alal misali, ya ce mu daraja “shugabannin gwamnati.” (Rom. 13:​1, 7) Amma wasu za su iya cewa: “Ina shirye in daraja duk wanda ya cancanci hakan.” Kana ganin irin wannan tunanin yana da kyau? A matsayinmu na bayin Jehobah, mun san cewa ba ayyukan mutane ne kawai suke sa mu daraja su ba. Muna yin hakan ne don Jehobah yana so mu daraja mutane. Kuma muna so mu sa shi farin ciki.—Yosh. 4:14; 1 Bit. 3:15.

6. Shin, zai yiwu mu daraja wanda ba ya daraja mu? Ka bayyana. (Ka kuma duba hoton.)

6 Shin, zai yiwu mu daraja wanda ba ya daraja mu? Ƙwarai kuwa. Ga wasu misalai. Sarki Shawulu ya kunyatar da ɗansa Jonathan a gaban mutane. (1 Sam. 20:​30-34) Duk da haka, Jonathan ya ci-gaba da daraja shi da kuma ba shi goyon baya a yaƙi har ƙarshe. (Fit. 20:12; 2 Sam. 1:23) Babban Firist Eli ya ce Hannatu ta bugu da giya. (1 Sam. 1:​12-14) Duk da haka, Hannatu ta daraja shi, ko da yake kowa da kowa a ƙasar Israꞌila sun san cewa yana da laifi a matsayinsa na uba da kuma babban firist. (1 Sam. 1:​15-18; 2:​22-24) Wasu mutanen Atina sun ce manzo Bulus, “mai surutu” ne. (A. M. 17:18) Duk da haka, Bulus ya yi musu magana a hanyar da ta nuna cewa ya daraja su. (A. M. 17:22) Waɗannan misalan sun nuna cewa idan muna ƙaunar Jehobah sosai, kuma ba ma so mu yi abin da zai ɓata masa rai, za mu riƙa daraja mutane, ko da yin hakan yana da wuya sosai. Bari mu tattauna game da mutanen da ya kamata mu riƙa darajawa, da kuma dalilin da ya sa ya kamata mu yi hakan.

Jonathan da Shawulu da kuma sojojin Israꞌila a filin daga suna yaƙi da wuƙa da mashi da kuma garkuwa.

Duk da cewa mahaifin Jonathan ya kunyatar da shi a gaban mutane, Jonathan ya ci-gaba da daraja shi da kuma ba shi goyon baya a matsayinsa na sarki (Ka duba sakin layi na 6)


MU RIƘA DARAJA ꞌYAN IYALINMU

7. Waɗanne abubuwa ne za su iya sa ya yi mana wuya mu daraja ꞌyan iyalinmu?

7 Dalilin da ya sa yin hakan zai iya yin wuya. Muna yawan zama da ꞌyan iyalinmu. Saboda haka, muna ganin halayensu masu kyau da kuma kasawarsu. Wasu kuma mai yiwuwa suna fama da rashin lafiya, ko tsananin damuwa da yake sa ya yi mana wuya mu kula da su. Ƙari ga haka, wasu ꞌyan iyalinmu za su iya gaya mana ko su yi abin da zai ɓata mana rai. Muna jin daɗin zama tare da ꞌyan iyalinmu, amma idan ꞌyan iyali ba sa daraja juna, za su iya soma yin fushi da juna. A sakamakon haka, za su daina kasancewa da haɗin kai. Za mu iya kwatanta yadda iyali yake da jikin ɗanadam. Rashin lafiya zai iya hana gaɓoɓin jikinmu yin aiki da kyau. Haka ma idan ꞌyan iyali ba sa daraja juna hakan zai hana su kasance da haɗin kai. Amma kamar yadda za mu iya shan magani mu warke idan ba mu da lafiya, ꞌyan iyali ma za su iya koyan yadda za su daraja juna kuma su yi hakan.

8. Me ya sa yake da muhimmanci mu daraja ꞌyan iyalinmu? (1 Timoti 5:​4, 8)

8 Me ya sa muke bukatar mu daraja ꞌyan iyalinmu? (Karanta 1 Timoti 5:​4, 8.) A wasiƙa ta farko da Bulus ya rubuta wa Timoti, ya gaya masa yadda ꞌyan iyali suke bukatar su kula da junansu. Ya bayyana cewa ya kamata mu daraja ꞌyan iyalinmu ba don kawai muna so mu yi hakan ba, amma don muna so mu “nuna hali irin Allah” ne. Muna yin hakan domin muna ƙaunar Jehobah kuma muna so mu bauta masa yadda yake so. Jehobah ne ya kafa iyali na farko. (Afis. 3:​14, 15) Don haka, idan muna daraja ꞌyan iyalinmu, hakan zai nuna cewa muna daraja Jehobah Wanda shi ne ya kafa dukan iyalai. Wannan dalili ne mai muhimmanci na daraja ꞌyan iyalinmu. Ko ba haka ba?

9. Ta yaya mata da miji za su nuna cewa suna daraja juna? (Ka kuma duba hotunan.)

9 Yadda za mu daraja juna a iyali. Mijin da ke daraja matarsa zai yi hakan ko da suna nan su kaɗai ko suna cikin jamaꞌa. (K. Mag. 31:28; 1 Bit. 3:7) Ba zai taɓa dūkan ta ko ya kunyatar da ita a gaban mutane ba. Kuma ba zai yi abin da zai sa ta ji kamar ba ya ƙaunar ta ba. Wani ɗanꞌuwa a ƙasar Ajantina mai suna Ariel,b ya ce: “Mamata tana rashin lafiya, kuma hakan yakan sa ta yi min baƙar magana a wasu lokuta. Idan hakan ya faru, nakan tuna wa kaina cewa, hakan ba halinta ba ne. Ban da haka ma, abin da ke 1 Korintiyawa 13:​5, yana taimaka min in yi mata magana a hanyar da za ta nuna cewa ina daraja ta, ba da fushi ba.” (K. Mag. 19:11) Mace tana daraja mijinta idan tana gaya wa mutane abubuwa masu kyau game da shi. (Afis. 5:33) Ba ta kushe shi ko ta zage shi, kuma ba ta masa baƙar magana a sunan wasa. Ta san cewa yin hakan zai iya sa aurensu ya lalace. (K. Mag. 14:1) Wata ꞌyarꞌuwa a Italiya da mijinta yake yawan damuwa ta ce: “A wasu lokuta, ina ganin kamar mijina yana yawan damuwa a kan abubuwan da ba su taka kara sun karya ba. A dā abubuwan da nake faɗa da yadda nake yi da fuskata suna nuna cewa ba na daraja shi. Amma na amfana sosai saꞌad da na soma tattaunawa da waɗanda suke daraja mutane. Hakan ya sa na ƙara daraja mijina.”

Hotuna: Mata da miji suna daraja juna. Na 1. Maigidan yana yi wa matarsa magana a hankali saꞌad da suke dafa abinci a kicin. Na 2. Matar tana gaya wa baƙinsu abubuwa masu kyau da maigidanta yake yi, yayin da shi kuma yake ba wa wani tsoho abinci.

Idan muna daraja ꞌyan iyalinmu, muna daraja Jehobah ne wanda shi ne Shugaban iyali (Ka duba sakin layi na 9)


10. Ta yaya matasa za su nuna cewa suna daraja iyayensu?

10 Matasa ku riƙa bin dokokin da iyayenku suka kafa a gida. (Afis. 6:​1-3) Ku riƙa daraja iyayenku saꞌad da kuke musu magana. (Fit. 21:17) Yayin da iyayenku suke tsufa, ku riƙa daraja su ta wurin taimaka musu da yin wasu abubuwa. Ku yi iya ƙoƙarinku wajen kula da su. Ku yi laꞌakari da labarin María, mahaifinta ba Mashaidin Jehobah ba ne. Saꞌad da ya soma rashin lafiya, hakan ya sa ya yi wa María wuya ta kula da shi. Ta ce: “Na roƙi Jehobah ya taimaka mini in daraja mahaifina kuma ayyukana su nuna hakan. Na san cewa Jehobah yana so in daraja iyayena, don haka zai taimaka min yi hakan. Da shigewar lokaci na gane cewa mahaifina ba ya bukatar ya canja halinsa kafin in daraja shi.” Idan muna daraja ꞌyan iyalinmu ko da yin hakan yana da wuya, hakan na nuna cewa muna daraja Jehobah wanda shi ne ya kafa iyali.

MU RIƘA DARAJA ꞌYANꞌUWANMU KIRISTOCI

11. Me ya sa zai iya mana wuya mu daraja ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci?

11 Dalilin da ya sa yin hakan zai iya yin wuya. ꞌYanꞌuwanmu Kiristoci suna iya ƙoƙarinsu su bi shawarar Littafi Mai Tsarki. Amma a wasu lokuta, sukan yi mana abin da bai dace ba, ko su yi saurin yanke hukunci a kanmu, ko kuma su ɓata mana rai. Idan wani ɗanꞌuwa a ikilisiya ya yi mana “laifi,” zai iya yi mana wuya mu ci-gaba da daraja shi. (Kol. 3:13) Mene ne zai taimaka mana?

12. Me ya sa yake da muhimmanci mu daraja ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci? (2 Bitrus 2:​9-12)

12 Me ya sa muke bukatar mu daraja ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci? (Karanta 2 Bitrus 2:​9-12.) A wasiƙar Bitrus ta biyu, Bitrus ya ambata cewa wasu a lokacin suna magana a hanyar da ta nuna cewa ba sa daraja “halittu masu daraja,” wato dattawa. Mene ne malaꞌiku da suka ga abin da ke faruwa suka yi? Da yake suna daraja Jehobah, ba su yi maganar da ba ta dace ba game da mutanen. Hakan abu ne mai kyau sosai! Duk da cewa mutanen suna da girman kai sosai, malaꞌikun sun tabbata cewa ba su yi musu maganar da ba ta dace ba. A maimakon haka, sun bar Jehobah ya tsawata kuma ya hukunta su. (Rom. 14:​10-12; ka kuma duba Yahuda 9.) Za mu iya koyan darasi daga abin da malaꞌikun suka yi. Idan har za mu daraja magabtanmu, zai dace mu daraja ꞌyanꞌuwanmu maza da mata da suke ƙaunar Jehobah. Muna bukatar mu yi “saurin girmama” su. (Rom. 12:10) Yin hakan zai nuna cewa muna daraja Jehobah.

13-14. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja ꞌyanꞌuwa a ikilisiya? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hotunan.)

13 Yadda za mu daraja ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci. Dattawa, a duk lokacin da kuke koyar da ꞌyanꞌuwa, ku yi hakan a hanyar da za ta nuna cewa kuna ƙaunar su. (Fil. 8, 9) A duk lokacin da kuke so ku yi wa wani gyara, ku yi hakan da ƙauna kuma ba a lokacin da kuke fushi ba. ꞌYanꞌuwa mata, za ku taimaka wa ꞌyanꞌuwa su riƙa daraja juna a ikilisiya, idan ba kwa gulma ko kuma ɓata sunan mutane. (Tit. 2:​3-5) Dukanmu za mu nuna cewa muna daraja dattawa a ikilisiya, idan muna ba su goyon baya da kuma nuna godiya don aikin da suke yi wajen gudanar da taro, da shirya yadda za a yi waꞌazi, da kuma taimaka wa waɗanda suke “cikin yin laifi.”—Gal. 6:1; 1 Tim. 5:17.

14 Akwai wata ꞌyarꞌuwa mai suna Rocío da ya yi mata wuya ta daraja wani dattijo da ya ba ta shawara. Ta ce: “Raina ya ɓace don na ji kamar bai yi min magana a cikin ƙauna ba. A gida ina maganganun da ba su dace ba game da shi. Ko da yake ina ƙoƙari kada in nuna masa hakan, a zuciyata na ga kamar ba taimako na ya zo yi ba, kuma na ƙi in bi shawararsa.” Me ya taimaka wa Rocío? Ta ƙara da cewa: “Da nake karanta Littafi Mai Tsarki, na karanta 1 Tasalonikawa 5:​12, 13. Da na ga cewa ba na daraja ɗanꞌuwan nan, zuciyata ta soma damuna. Na yi adduꞌa ga Jehobah, kuma na bincika littattafanmu don in ga bayanan da za su taimaka min in gyara yadda nake tunani. Na zo na gane cewa ba ɗanꞌuwan ba ne matsalar, ni ce nake da girman kai. Yanzu na gane cewa ina bukatar in kasance da sauƙin kai don in iya daraja mutane. Har yanzu ina kan koyan yadda zan riƙa daraja mutane, kuma na san cewa Jehobah yana farin cikin domin ƙoƙarin da nake yi.”

Hotuna: Wata ꞌyarꞌuwa da tsufa tana karanta Littafi Mai Tsarki kuma tana tunani a kan ayyuka dabam-dabam da dattawa suke yi. Na 1. Wani dattijo yana ba da jawabi a taron ikilisiya. Na 2. Yana taimaka wa wani ɗanꞌuwa da ke zaune a keken guragu. Na 3. Yana kwashe dusar ƙanƙara a gaban Majamiꞌar Mulki.

Dukanmu za mu nuna cewa muna daraja dattawa a ikilisiya, idan muna ba su goyon baya da kuma nuna godiya don aikin da suke yi (Ka duba sakin layi na 13-14)


MU RIƘA DARAJA WAƊANDA BA SA BAUTA WA JEHOBAH

15. Me ya sa zai iya mana wuya mu daraja waɗanda ba sa bauta wa Jehobah?

15 Dalilin da ya sa yin hakan zai iya yin wuya. Muna yawan haɗuwa da mutane a waꞌazi da ba sa ƙaunar Allah ko Littafi Mai Tsarki. (Afis. 4:18) Wasu ba sa son waꞌazinmu domin abin da aka koya musu tun suna yara. Ƙari ga haka, wasu abokan aikinmu ko ꞌyan makarantarmu suna da wuyan shaꞌani. Kuma wasu da muke musu aiki ko kuma malaman makarantarmu ba sa son mu ko kuma waꞌazin da muke yi. Da shigewar lokaci, za mu iya daina daraja su kuma mu so mu bi da su a hanyar da ba ta dace ba.

16. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa daraja mutanen da ba sa bauta wa Jehobah? (1 Bitrus 2:12; 3:15)

16 Me ya sa muke bukatar mu daraja waɗanda ba sa bauta wa Jehobah? Mu tuna cewa Jehobah ya damu da yadda muke bi da waɗanda ba sa bauta masa. Manzo Bitrus ya tuna wa Kiristoci cewa halayensu masu kyau za su iya sa mutane su “ɗaukaka Allah.” Saboda haka, ya gaya musu su bayyana imaninsu cikin “sauƙin kai da ban girma.” (Karanta 1 Bitrus 2:12; 3:15.) Ko da muna bayyana imaninmu ga hukumomin gwamnati ko wasu mutane dabam, muna bukatar mu yi hakan a hanyar da za ta nuna cewa muna daraja su. Domin Jehobah yana kallo kuma yana sauraron abin da muke faɗa. Wannan babban dalili ne da ya sa za mu riƙa daraja mutanen da ba shaidu ba. Ko ba haka ba?

17. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja waɗanda ba sa bauta wa Jehobah?

17 Yadda za mu daraja waɗanda ba sa bauta wa Jehobah. Saꞌad da muke waꞌazi, bai kamata mu sa mutane su ga kamar ba su san kome ba game da Littafi Mai Tsarki. A maimakon haka, zai dace mu tuna cewa suna da daraja a gaban Allah, kuma suna da muhimmanci a gare mu. (Hag. 2:7; Filib. 2:3) Idan mutum ya yi mana maganar da ba ta dace ba domin imaninmu, kada mu rama, kuma kada mu faɗa abin da zai sa shi fushi ko ya nuna cewa mun fi shi wayo. (1 Bit. 2:23) Idan ka faɗi wani abin da bai dace ba, ka nemi gafara nan da nan. Ta yaya za ka nuna cewa kana daraja abokan aikinka? Ka riƙa yin aikinka da kyau sosai, kuma ka riƙa mai da hankali ga halaye masu kyau da abokan aikinka, da kuma waɗanda kake musu aiki suke nunawa. (Tit. 2:​9, 10) Idan muna faɗin gaskiya kuma muna yin aikinmu da kyau, wasu za su ji daɗin hakan, wasu kuma ba za su ji daɗi ba. Amma Allah zai yi farin ciki da mu.—Kol. 3:​22, 23.

18. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa girmama mutane?

18 Muna da dalilai masu kyau da za su sa mu daraja mutane! Mun ga cewa idan mun daraja ꞌyan iyalinmu muna daraja Jehobah, wanda shi ne Shugaban iyali. Haka ma, idan muna daraja ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci, hakan ya nuna cewa muna girmama Ubanmu na sama. Kuma idan muka daraja waɗanda ba sa bauta wa Jehobah, hakan zai sa ya yi musu sauƙi su girmama Jehobah wata rana. Ko da mutane ba sa daraja mu, yana da muhimmanci mu riƙa daraja su. Me ya sa? Domin Jehobah zai yi mana albarka, kuma ya yi alkawari cewa zai “girmama waɗanda suke girmama” Shi.—1 Sam. 2:30.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja ꞌyan iyalinmu?

  • Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci?

  • Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja waɗanda ba sa bauta wa Jehobah?

WAƘA TA 129 Za Mu Riƙa Jimrewa

a Karin Magana 22:1 (NWT): “Gwamma suna mai kyau da samun dukiya. Gwamma zama wanda ake darajawa da samun azurfa da zinariya.”

b An canja wasu sunayen.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba