Mene ne Yaronka Zai Faɗa?
IYAYE: A fitowar Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 2010, shafuffuka na 16-20, mun ambata yin gwaji da yaranku. Wannan talifin ya faɗi abubuwa da za su taimaka muku ku shirya yaranku su bi da ƙalubale da suke fuskanta a makaranta. Kuna iya yin waɗannan gwaji a lokacin Bautarku ta Iyali da yamma.
YARA da Shaidun Jehobah ne suna fuskantar kaluɓale masu yawa. Sau da yawa, abokan makaranta suna tambayar dalilin da ya sa ba za su yi wasu ayyuka ba, kamar su rera taken ƙasa da bukukuwan ranakun haihuwa, da kuma ayyukan ranar hutu. Idan aka yi wa yaronku ko ’yarku irin waɗannan tambayoyi, wane amsa ne yaronku ko ’yarku zai ba da?
Wasu yara Kiristoci sun faɗa kawai: “Ba zan iya yin hakan ba. Addini na bai amince da hakan ba.” Ya kamata a yaba wa waɗannan yaran don tsayin daka da suka yi. Amsa da suka ba da zai iya sa ba za a yi musu ƙarin tambayoyi ba. Duk da haka Littafi Mai Tsarki ya yi mana gargaɗi mu kasance ‘a shirye mu amsa ma kowane mai-tambayarmu dalilin’ imaninmu. (1 Bit. 3:15) Yin hakan ba kawai faɗan cewa, “Ba zan iya yin hakan ba.” Ko idan wasu ba su amince da mu ba, wasu suna iya son sanin dalilan da suka sa muka tsai da wannan shawara.
Matasa Shaidu da yawa sun faɗa wa abokan makarantarsu labaran Littafi Mai Tsarki ta wajen yin amfani da littattafai kamar su littafin nan Ka Koya Daga Wurin Babban Malami. Waɗannan labaran suna iya taimaka wajen bayyana dalilin da ya sa yara Shaidu suke yi ko kuma ba sa yin wasu abubuwa. Wasu ɗalibai suna saurara wa labaran Littafi Mai Tsarki sosai, kuma an soma nazarorin Littafi Mai Tsarki da yawa ta wannan hanyar. Yana iya yi wa wasu ɗalibai wuya su saurari labarin Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya. Idan ba a bayyana musu sosai ba, yana iya yi wa yaran makaranta wuya ainun su fahimci wasu labaran Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da abokiyarta ta gayyace ta zuwa fatin ranar haihuwa, Minhee ’yar shekara 11 ta gaya wa abokiyarta: “Littafi Mai Tsarki bai gaya mana mu yi bikin ranakun haihuwa ba. An kashe wani da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki, wato, Yohanna Mai Baftisma, a ranar bikin haihuwa.” Amma, Minhee ta tuna cewa abokiyarta ba ta fahimci amsarta ba.
A wani lokaci, yana da kyau a nuna wa wani ɗalibi hoto ko kuma wani labari a ɗaya daga cikin littattafanmu. Idan hukumar makarantar suka faɗa cewa za su fi son kada yara su nuna littattafai na addininsu ga wasu ɗalibai kuma fa? Shin yaranmu suna iya yin wa’azi da kyau ba tare da yin amfani da littattafanmu ba? Ta yaya za ku taimaka wa yaranku su ba da amsa ga imaninsu?
Ku Yi Gwaji
Yin gwaji a gida zai kasance da taimako, iyaye su ɗauki matsayin abokan makaranta. Yayin da yara suke ƙoƙari su ba da amsa ga dalilin imaninsu, iyaye su yaba musu kuma su nuna musu yadda za su iya kyautata mahawararsu da abin da ya sa hakan yake da kyau. Alal misali, ku ba su shawarar yin amfani da kalamai da ɗalibai na wasu shekaru za su iya fahimta. Joshua, ɗan shekara tara ya ce abokan makarantarsa ba su fahimci kalamai kamar su “lamiri” da “aminci” ba. Saboda haka yana amfani da kalamai masu sauƙi don ya tattauna da su.—1 Kor. 14:9.
Wasu yaran makaranta da suka yi tambaya suna iya ƙin saurarawa idan aka ba da dogon amsa. Ta wajen tattaunawa da su da kuma yi musu tambaya, matasa Shaidu suna iya ci gaba da sa su so saƙon. Haneul, wata yarinya ’yar shekara goma ta ce, “Abokan makaranta na suna son tattaunawa, ba sa son bayani.” Don ku tattauna, ku yi tambayoyi, sai kuma ku saurara da kyau ga ra’ayin da suka furta.
Tattaunawa da aka tsara a ƙasa sun nuna yadda yara Kiristoci za su iya tattaunawa da abokan makarantarsu. Ba ku bukatar ku haddace waɗannan tattaunawar domin yara sun bambanta da juna, kuma amsoshin da za su ba da sun bambanta ga yanayi dabam dabam. Saboda haka, ya kamata matashi Mashaidi ya yi tunanin amsoshin, ya saka shi a nasa kalamai, kuma ya faɗe shi yadda zai dace ga yanayin da kuma abokan makarantarsa. Idan kuna da yara da suke zuwa makaranta, ku yi ƙoƙari ku gwada waɗannan tattaunawar da su.
Koyar da yara yana bukatar lokaci da ƙoƙari. Iyaye Kiristoci suna son su koya wa yaransu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma su rinjaye su su yi rayuwa da ta jitu da waɗannan ƙa’idodin.—K. Sha 6:7; 2 Tim. 3:14.
A Bautarku ta Iyali da yamma na gaba, ku yi ƙoƙari ku gwada tattaunawa da aka faɗa a nan da yaranku. Ku gwada ku ga yadda wannan zai kasance muku da amfani. Ku tuna cewa makasudin ba don a haddace amsoshi ko kuma kalamai ba ne. Kuna iya sake gwada wani yanayi sau da yawa, kuna ba da amsoshi dabam dabam kuma ku ga yadda yaranku suke amsa kowace tambaya. Yayin da suke ƙoƙari su bayyana dalilin imaninsu, ku taimaka musu su koya yadda ake tattaunawa da kuma kasancewa da basira. Da shigewar lokaci, za ku koya wa yaranku yadda za su kāre imaninsu a gaban abokan aji da maƙwabta, da kuma malamai.
[Akwati/Hotuna da ke shafi na 4]
BUKUKUWAN RANAR HAIHUWA
Maryamu: Barka dai, Yohanna! Ina so na gayyace ka zuwa bikin da na shirya.
Yohanna: Na gode da kika tuna da ni. Wane irin biki ne?
Maryamu: Bikin ranar haihuwata ne, kuma za a sakata a wala.
Yohanna: Don Allah kada ki yi fushi, amma ba zan iya zuwa ba don ba na yin bikin haihuwa.
Maryamu: Me ya sa? Za a fa sakata a wala a bikin.
Yohanna: Ni ma ina son fati. Amma mu Shaidun Jehobah muna son mu yi koyi da Yesu, kuma bai yi bikin ranar haihuwa ba. Shi ya sa ba na bikin ranar haihuwa.
Maryamu: Amma za ka iya halartar fatin? Ba ka bukatar ka sa hannu a bikin ko kuma ka kawo mini kyauta.
Yohanna: A’a, ba zan iya ba. Bin shawarar Littafi Mai Tsarki tana da muhimmanci a gare ni. Kuma ya ce mabiyin Yesu ba su yi bikin haihuwa ba kuma ba su halarci irin wannan bikin ba.
Maryamu: Kana nufin cewa kada na yi bikin haihuwata?
Yohanna: Wannan shawarar ki ne. Amma a iyalina, mun yanki shawara cewa ba za mu yi bikin haihuwa ba.
Maryamu: Wato, iyayenka ba sa ba ka kyauta?
Yohanna: Hakika suna ba ni. Iyayena ba sa jira sai ranar bikin haihuwa na. Suna ba ni kyauta duk lokacin da suke so. Amma za ki so ki san tushen bikin ranar haihuwa?
Maryamu: Za ka iya gaya mini?
Yohanna: To, gobe zan gaya miki labari mai daɗi game da bikin ranar haihuwa na zamanin dā.
RERA TAKEN ƘASA
Hajara: Me ya sa ba ki rera taken ƙasa?
Binta: Zan so na gaya miki, amma ina son ki fara gaya mini dalilin da ya sa kike rera waƙar.
Hajara: Domin ina ƙaunar ƙasata.
Binta: Ni ma haka. Amma wasu ƙasashe ma ba su da kyau ne?
Binta: Hakika, suna da kyau.
Hajara: Ba ma tashi tsaye mu rera waƙa ga kowa ko kome da muke ƙauna, ko ba haka ba?
Binta: Hakika. Ina gani kamar ban san dalilin da ya sa nake rera taken ƙasa ba, wataƙila saboda kowa yana yin hakan ne.
Hajara: Mutane da yawa suna ganin cewa ƙasarsu ce ta fi kyau a duniya. Za su iya yin kome saboda ƙasarsu. Amma ni ba na jin hakan. Ba zan taɓa sa hannu a yaƙi ba kuma ba zan mutu don ƙasarmu ba. Allah ba ya son yaƙi da kuma ƙishin ƙasa, ni ma hakan. Ko da yake ina ƙaunar ƙasarmu, amma na yanki shawara cewa ba zan rera taken ƙasa ba.
Binta: Na fahimta.
Hajara: Binta, na yi farin ciki da kika ambata wannan. Kuma idan kina son ki san dalilin da ya sa nake yin wasu abubuwa kuma ba na yin wasu, ki tambaye ni. Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa tun da daɗewa, wani sarki na Babila ya umurci mutane su rusuna a gaban wata siffa da ke wakiltar ƙasarsu. Wasu sun ƙi rusunawa, ko da hakan ya sa rayuwarsu cikin kasada.
Binta: Da gaske? Mene ne ya faru da su?
Hajara: Zan gaya miki game da su a lokacin cin abincin rana.
YIN SIYASA A MAKARANTA
Bala: Haruna, kai ma za ka tsaya takaran shugaban ajinmu kuwa? Gaskiya wannan mukamin ya dace da kai sosai. Kuma ni ne zan fara jefa maka ƙuri’a.
Haruna: Na gode, amma ba na so na zama shugaban ajin.
Bala: Me ya sa?
Haruna: Domin ni Kirista ne kuma ina so na yi koyi da Yesu. Bai saka hannu a siyasa ba. Za ka so ka san dalilin da ya sa bai yi hakan ba?
Bala: A’a, ba na son na sani.
Haruna: To, duk lokacin da kake son ka sani, zan yi farin cikin gaya maka.
[Hoton]
“Barka dai Yohanna. Ina so na gayyace ka zuwa fatin tuna ranar haihuwata”
[Hoton da ke shafi na 3]
“Me ya sa ba ka rera taken ƙasa?”