“Wata Babbar Rana a Rayuwata”
“BAƘIN ciki shi ne babban matsala mai taɓa hankali da sau da yawa ake ba da rahotonsa tsakanin matasa,” in ji Beyondblue, wata ma’aikatar gwamnati a Austireliya. Bincike ya nuna cewa Austireliyawa matasa 100,000 ne suke fama da baƙin ciki kowace shekara.
Kiristoci Matasa ma suna baƙin ciki. Amma bangaskiyarsu ga Jehobah ta taimake su su shawo kan baƙin ciki, su kuma ji daɗin rayuwarsu. Ta wurin yin haka suna burge mutane. Ta yaya?
Ka yi la’akari da labarin Claire ’yar shekara 18. Ita da mahaifiyarta suna halartar taro a ikilisiyar Shaidun Jehobah wadda take birnin Melbourne. Sa’ad da mahaifin Claire ya yi watsi da iyalinsa, Claire ta yi baƙin ciki sosai. Amma bangaskiyarta ga Ubanta na samaniya, Jehobah, ya kasance da ƙarfi. Wata rana likitar gidansu Claire mai suna Lydia ta ziyarce su, ta ga ko yaya Claire take. Bayan haka, ta gayyaci Claire su tafi sayayya. Suna cikin tafiya sai ta tambayi Claire ko tana da saurayi. Claire ta yi mata bayani cewa ita Mashaidiyar Jehobah ce, saboda haka ba ta fita zance da maza. Wannan amsar ta ba wa likitar mamaki. Sai Claire ta yi mata bayani yadda Littafi Mai Tsarki ya taimake ta, ta yanke shawarwari masu kyau a rayuwarta. Sai, ta ce za ta bai wa likitar littafi na Littafi Mai Tsarki wanda ya taimake ta sosai. Littafin yana da jigo Question Young People Ask—Answers That Work.
Bayan kwanaki uku da samun littafin, Lydia ta buga wa mahaifiyar Claire waya, ta gaya mata yadda ta ji daɗin karanta littafin. Sai ta ce a ba ta ƙarin littattafan shida domin ta ba abokan aikinta. Sa’ad da Claire ta kai waɗannan littattafan, likitar ta bayyana yadda bangaskiyar Claire ta burge ta. Claire ta gaya mata za ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita, likitar kuwa ta yarda.
Claire ta yi watanni tana yin nazari da likitar a lokacin da likitar take hutawa da rana. Lydia ta tambayi Claire ko za ta so ta yi magana a kan batun baƙin ciki a tsakanin matasa a wani taron ƙara wa juna sani. Ko da yake ta tsorata, amma sai ta yarda. Fiye da mutane 60 suka halarci taron. Gwanaye huɗu a kimiyyar taɓuwa, dukansu manyan mutane, suka yi wa jama’a jawabi. Sai lokacin da Claire za ta yi jawabi ya yi. Claire ta nanata yadda yake da muhimmancin matasa su yi dangantaka da Allah. Ta yi bayani game da yadda Jehobah Allah yake kula da matasa sosai kuma yake taimakon waɗanda suke neman tallafi da sanyayar zuciya a gare shi. Bugu da ƙari, ta furta tabbacinta cewa ba da daɗewa ba Jehobah zai kawar da ko wane irin taɓuwa. (Ishaya 33:24) Menene sakamakon wannan shaida mai kyau?
“Da aka gama taron, mutane da yawa suka zo wurina, suka faɗi yadda suka yi sha’awar jin matashiya tana magana game da Allah,” in ji Claire. “Na ba da littafin nan Young People Ask wajen 23. ’Yan mata uku daga cikin masu sauraron suka ba ni lambar tarhonsu. Ɗaya daga cikin ’yan matan yanzu tana nazarin Littafi Mai Tsarki. Wannan babbar rana ce a rayuwata.”