Rashin Gaskiya Ne Kuwa?
“Ka ɗan gyara rahoton haɗarin da za ka ba da, kuma komi zai tafi daidai.”
“Masu karɓan haraji ba sa bukatar su san komi.”
“Abu mafi muhimmanci shi ne kada a kama ka.”
“Don me za ka biya tun da za ka iya samun ta kyauta?”
ZA KA iya jin kalamai irin waɗannan idan ka nemi shawara game da batun kuɗi. Wasu mutane kamar dai suna da “maganin” duk wani abu. Amma tambayar ita ce, Waɗannan hanyoyin magance matsaloli na gaskiya ne kuwa?
Rashin gaskiya ruwan dare ne a yau har ma mutane sukan ɗauki yin ƙarya, zamba, da sata kamar karɓaɓɓen abu don kada a hukunta su, don su samu kuɗi, ko kuma su samu ci gaba. Manyan mutane a al’umma sukan kafa mummunar misali game da yin gaskiya. A wata ƙasar Turai, batun ha’inci da zamba ya ƙaru zuwa kashi 85 daga shekara ta 2005 zuwa 2006. Kuma wannan rahoton bai haɗa da wasu ƙananan zance na rashin gaskiya ba, waɗanda wasu suke kira “ƙaramin zunubi.” Ba abin mamaki ba ne sa’ad da wasu manya-manyan ’yan kasuwa da ’yan siyasa a ƙasar suka yi abin kunya inda aka gano cewa sun yi amfani da takardar makarantar da ba tasu ba.
Duk da rashin gaskiya da ke ko’ina a duniya, mutane da yawa suna son su yi abu mai kyau. Mai yiwuwa kana ɗaya daga cikinsu. Wataƙila saboda kana ƙaunar Allah, kana son ka yi abin da ya dace a idanunsa. (1 Yohanna 5:3) Za ka iya ji kamar manzo Bulus, wanda ya rubuta: “Mun kawar da shakka muna da kyakkyawan lamiri, muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.” (Ibraniyawa 13:18) Saboda haka, muna gayyatarka ka duba wasu yanayi da za su iya gwada muradin mutum na kasancewa da “tasarrufin kirki cikin dukan abu.” Za mu kuma yi la’akari da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su iya taimakawa a irin waɗannan yanayin.
Wa Ya Kamata Ya Biya Kuɗin Ɓarnar da Aka Yi a Haɗari?
Wata rana, wata mata matashiya mai suna Lisaa tana kan tuka motarta, sai ta yi kuskure ta yi karo da wata mota. Babu wanda ya ji rauni, amma motocin biyu sun lalace. A ƙasar da take, direbobi matasa sukan biya kuɗaɗe da yawa don inshoran mota, kuma wannan kuɗaɗen sukan ƙaru bayan kowanne haɗarin da aka yi. Tun da ɗan’uwan Lisa, mai suna Gregor yana tare da ita kuma ya girme ta, wani abokinsu ya shawarce su cewa su rubuta cewa Gregor ne yake tuka motar. Da hakan, Lisa ba za ta biya kuɗi mai yawa don inshora ba. Kamar dai wannan shawarar mai kyau ce. Me ya kamata ta yi?
Kamfanonin inshora suna biyan waɗanda suke da matsaloli da kuɗaɗen waɗanda suke da asusu a kamfaninsu. Saboda haka, ta wajen bin shawarar abokinta, Lisa za ta tilasta wa wasu da suka yi inshora su biya kuɗi mai yawa don haɗarin da ta yi. Ta yin hakan za ta ba da rahoton ƙarya kuma za ta saci kuɗaɗen wasu. Hakan daidai ne da ba da rahoton ƙarya don a daɗa kuɗin inshoran da za a ba mutum.
Hukuncin kotu zai iya sa waɗannan ayyukan ƙarya su ɗan ragu. Amma dalili mafi muhimmanci na guje wa rashin gaskiya yana cikin Kalmar Allah. “Ba za ka yi sata ba,” in ji ɗaya daga cikin Dokoki Goma. (Fitowa 20:15) Manzo Bulus ya maimaita wa Kiristoci wannan umurnin, sa’ad da ya ce: “Mai-yin sata kada ya ƙara yin sata.” (Afisawa 4:28) Ta wajen yin biyayya ga Kalmar Allah a irin wannan batu na inshora, kana guje wa yin abin da Allah ya haramta. Kana kuma nuna ƙaunarka da girmamawa ga dokar Allah da kuma maƙwabtanka.—Zabura 119:97.
“Ku Ba Kaisar Abin da ke na Kaisar”
Peter ɗan kasuwa ne. Akanta ɗinsa ya ba shi shawara cewa ya nemi ragin haraji na kwamfuta mai tsada da ya “saya.” Masu yin irin sana’ar da Peter yake yi suna yin irin wannan sayayyar. Ko da yake Peter bai yi sayayyar ba, zai yi wuya gwamnati ta bincika irin wannan sayayyar. Za a rage wa Peter kuɗaɗe da yawa a harajin da zai biya. Me ya kamata ya yi? Menene zai ja-gorance shi wajen yanke shawara?
Manzo Bulus ya gaya wa Kiristocin zamaninsa: “Bari kowa ya yi biyayya ga mahukunta. . . . Ku ba kowa hakkinsa, masu haraji, harajinsu, masu kuɗin fito, kuɗinsu na fito.” (Romawa 13:1, 7, Littafi Mai Tsarki) Waɗanda suke son su samu amincewar Allah suna biyan dukan harajin da hukuma take bukata. A wani ɓangaren kuma, idan dokar ƙasar ta rage wa wasu mutane da sana’o’i harajinsu, babu laifi idan mun karɓi kuɗaɗen in mun cancanci hakan.
Ga wani yanayin da ya shafi biyan haraji. David kafinta ne a wani kamfani. Sai abokansa da maƙwabta suka ce masa ya yi musu kabat da kayayyakin ɗaki, kuma ya yi hakan bayan an tashi aiki. Sun ce za su biya shi kuɗin da ya ɗara wanda ake biyansa a wajen aikinsa, amma suna son ya yi aikin ba tare da ya rubuta rasit ba. Da hakan aikin ba zai kasance a rubuce ba kuma babu wanda zai biya haraji. Mutane da yawa suna zaton cewa yin hakan ya dace, tun da duk sun amfana daga wannan shirin. Amma domin David yana son ya faranta wa Allah rai, yaya ya kamata ya ɗauki irin wannan aikin da aka yi a ɓoye?
Ko da yake wataƙila ba za a kama mutumin da ke yin irin waɗannan ayyukan ba, amma ba ya biyan harajin da gwamnati take da ikon karɓa. Yesu ya ba da wannan umurnin: “Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar; Allah kuma abin da ke na Allah.” (Matta 22:17-21) Yesu ya faɗi hakan ne don ya daidaita tunanin masu sauraronsa game da biyan haraji. Hukumomi waɗanda Yesu ya kira Kaisar, sun ɗauki biyan haraji a matsayin hakkinsu. Saboda haka, mabiyan Kristi sun ɗauki biyan dukan haraji a matsayin farilla ne daga Nassosi.
Yin Sata a Wajen Jarrabawa
Wata ɗalibar makarantar sakandare mai suna Marta tana shirin rubuta jarrabawar kammala makaranta. Domin za ta iya samun aiki mai kyau ne kawai idan ta ci jarrabawar sosai, ta yi awoyi tana yin nazari. Wasu ’yan ajinta su ma sun shirya, amma a wata hanya dabam. Za su riƙa yin amfani da pager, tsararren kalkuleta da kuma tarho don su saci amsa kuma su samu maki mai yawa. Shin zai dace Marta ta yi abin da “kowa” ke yi don ta ci jarrabawar?
Domin sata ya zama gama gari, mutane da yawa suna ganin cewa hakan ba laifi ba ne. Sukan ce, “Abu mafi muhimmanci shi ne kada a kama ka.” Irin wannan tunanin ba abin karɓa ba ne ga Kiristoci na gaskiya. Ko da yake wataƙila malami ba zai gan waɗanda suke satar amsa ba, amma akwai wanda yake gani. Jehobah Allah ya san abin da muke yi kuma zai hukunta mu bisa ga ayyukanmu. Manzo Bulus ya rubuta: “Babu wani abu mai-rai kuma da ba a bayyane a gabansa ba: amma abubuwa duka a tsiraice su ke, buɗaɗu kuma gaban idanun wannan wanda mu ke gare shi.” (Ibraniyawa 4:13) Sanin cewa Allah yana kallonmu da niyar ganin cewa muna yin abu mai kyau, kyakkyawan dalili ne da ya kamata ya motsa mu mu yi gaskiya sa’ad da muke rubuta jarrabawa, ko ba haka ba?
Menene Za Ka Yi?
Lisa, Gregor, Peter, David da Marta sun fahimci muhimmancin yanayin da suka fuskanta. Sun yanke shawarar kasancewa da aminci don su riƙe lamiri mai kyau da kuma nagarta. Me za ka yi idan ka fuskanci irin wannan yanayin?
Abokanka, ’yan ajinku, da maƙwabtanka za su iya yin ƙarya, zamba, ko sata ba tare da sun damu ba. Za su iya yi maka ba’a don su tilasta maka ka yi abin da suke yi. Menene zai taimaka maka ka yanke shawara mai kyau duk da matsin yin rashin gaskiya?
Ka tuna cewa, yin abubuwa cikin jituwa da nufin Allah zai sa mu kasance da lamiri mai kyau tare da amincewa da kuma tagomashin Allah. Sarki Dauda ya rubuta: “Ya Ubangiji, wa za ya sauka cikin tenti naka? Wanene za ya zauna cikin tudunka mai-tsarki? Shi wanda ke tafiya sosai, yana aika adalci, yana kuwa faɗin gaskiya cikin zuciyatasa. . . . Shi wanda ke yin haka nan ba shi jijjiguwa ba har abada.” (Zabura 15:1-5) Lamiri mai kyau da dangantaka mai kyau da Allah na samaniya ya fi duk wani irin wadata da za mu iya samu ta hanyar rashin gaskiya.
[Hasiya]
a An canja wasu sunaye.
[Bayanin da ke shafi na 12]
“Mai-yin sata kada ya ƙara yin sata.”
Daraja dokar Allah da kuma ƙauna ga maƙwabta za su motsa mu mu kasance da gaskiya a batun inshora
[Bayanin da ke shafi na 12]
“Ku ba kowa hakkinsa, masu haraji, harajinsu.”
Don samun amincewar Allah, muna biyan dukan haraji da hukuma ta ce mu biya
[Bayanin da ke shafi na 13]
‘Abubuwa duka . . . buɗaɗu suke gaban idanun wannan wanda mu ke gare shi.’
Ko da yake wataƙila malamai ba za su kama mu muna satan amsa ba, amma muna son mu kasance da gaskiya a gaban Allah
[Akwati/Hotuna da ke shafi na 14]
Sata na “Ɓoye”
Abokinka ya sayi wani sabon tsarin furogram na kwamfuta, kuma kana son furogram ɗin. Don ba ya son ka kashe kuɗi, sai ya ce zai kofe maka tsarin. Hakan rashin gaskiya ne?
Sa’ad da mutane suka sayi software na kwamfuta, suna amincewa da bin umurnin da aka bayyana dalla-dalla a yarjejeniyar lasisin wannan tsarin. Lasisin zai iya amince wa wanda ya sayi tsarin ya saka kuma ya yi amfani da shi a cikin kwamfuta guda kawai. A irin wannan yanayin, kofe wa wani wannan software ɗin ya ƙarya yarjejeniyar lasisin kuma hakan karya doka ce. (Romawa 13:4) Yin irin wannan kofen sata ne, domin hakan ya hana mai hakkin wallafawa ya samu kuɗin da ya kamata ya samu.—Afisawa 4:28.
Wasu suna iya cewa, ‘Ai babu wanda zai taɓa sani.’ Hakan zai iya kasancewa gaskiya, amma mu tuna kalaman Yesu: “Dukan abu fa iyakar abin da ku ke so mutane su yi maku, ku yi musu hakanan kuma.” (Matta 7:12) Dukanmu muna son a biya mu kuɗin aikin da muka yi kuma muna son mutane su daraja dukiyarmu. Saboda haka, dole ne mu nuna irin wannan halin ga wasu. Ya kamata mu guji sata na “ɓoye,” kamar su ɗaukan cin gumin wasub da ba namu ba.—Fitowa 22:7-9.
[Hasiya]
b Gumin wasu ya ƙunshi abubuwan nan masu hakkokin wallafawa kamar su waƙa, littattafai, ko software, a rubuce a kan takarda ko kofansu a cikin wani abu. Tambarin kamfani, takardar izini, sirrin kasuwanci, da kuma ikon yin talla duk sun faɗa ƙarƙashin hakan.