Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w21 Yuni p. 25
  • Ka Sani?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sani?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
w21 Yuni p. 25
Yesu rike da kudin dinari.

Ka Sani?

A zamanin Yesu, wane irin haraji ne mutane suke biya?

ISRA’ILAWA sun yi shekaru da yawa suna biyan haraji don su tallafa wa bauta ta gaskiya. Amma a zamanin Yesu, Yahudawa sukan biya haraji dabam-dabam kuma hakan ya sa su cikin mawuyacin yanayi.

An bukaci kowane Bayahude da ya manyanta ya riƙa biyan raɓin shekel kowace shekara don tallafa wa aikin da ake yi a mazauni, kuma daga baya don aikin haikali. A ƙarni na farko, an yi amfani da harajin wajen kula da haikalin da Hiridus ya gina da kuma ayyukan da ake yi a wurin. Da wasu Yahudawa suka tambayi Bitrus ra’ayin Yesu game da harajin nan, Yesu bai ce biyan harajin laifi ba ne. Ya ma ce wa Bitrus ya je ya samo kuɗi don ya biya harajin.​—Mat. 17:​24-27.

Ban da haka ma, mutanen Allah a lokacin suna biyan zakka, wato kashi 1 cikin 10 na amfanin gonarsu ko kuma na kuɗin da suka samu. (L. Fir. 27:​30-32; L. Ƙid. 18:​26-28) Shugabannin addinai a lokacin sun nace cewa dole ne a biya zakka a kan kowane kayan lambu, har ma da “kayan yaji na ganye.” Yesu bai ce biyan zakka laifi ba ne, amma ya nuna cewa Farisawa da marubuta suna yin munafunci a wannan batun.​—Mat. 23:23.

Ƙari ga haka, Yahudawa a lokacin suna biyan haraji dabam-dabam ga Romawa, waɗanda ke mulki a kansu. Alal misali, an bukaci waɗanda suke da gona su biya haraji a kan gonar, kuma za su iya yin hakan da kuɗi ko kayayyakinsu. Mutane sukan biya kashi 20 zuwa 25 na amfanin gonarsu. Sa’an nan, kowane Bayahude yana biyan haraji don kansa. Game da wannan harajin ne Farisawa suka yi wa Yesu tambaya. Yesu ya faɗi irin ra’ayin da ya kamata mu kasance da shi idan ya zo ga batun biyan haraji. Ya ce: “Ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”​—Mat. 22:​15-22.

Ƙari ga haka, akan karɓi haraji a kan kayan sayarwa da ke fita da shiga yankin Yahudawa. Ana karɓan wannan harajin a tashar jirgin ruwa ko gadoji ko hanya ko ƙofar shiga gari ko kuma kasuwanni.

Duka harajin da Romawa suke karɓa daga hannun Yahudawa ya fi ƙarfin Yahudawan. Wani masanin tarihi ɗan Roma mai suna Tacitus, ya ce a ƙarƙashin mulkin Sarki Tiberius, wato a lokacin da Yesu yake duniya, “harajin da Suriyawa da Yahudawa suke biya ya fi ƙarfin su. Sai suka roƙa a rage musu.”

Abin da ya fi takura wa Yahudawan ma shi ne yadda ake karɓan harajin. Waɗanda suka fi ba da kuɗi don sayan matsayin masu karɓan haraji ne suke samun damar yin hakan. Sai masu karɓan harajin su nemi waɗanda za su riƙa karɓa musu harajin kuma su riƙa cin riba a kan harajin. Kamar dai Zakka ya samo irin mutanen nan su riƙa masa aiki. (Luk. 19:​1, 2) Hakan ya sa Yahudawa sun tsani masu karɓan haraji.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba