Ka Kusaci Allah
“Yana Duban Zuciya”
1 SAMA’ILA 16:1-12
SHIGAR da mutum ya yi zai iya ruɗar da mu. Yadda surar mutum yake ba zai iya bayyana abin da ke cikin zuciyarsa ba. Mutane suna yin hukunci bisa abin da suka gani. Amma abin godiya, Jehobah Allah yana kallon fiye da bayyanuwarmu. Hakan ya bayyanu sosai a kalaman da ke rubuce a 1 Sama’ila 16:1-12.
Ka yi la’akari da wannan yanayin. Jehobah yana dab da naɗa sabon sarki bisa al’ummar Isra’ila. Allah ya ce wa annabi Sama’ila: Zan “aike ka wurin Jesse mutumin Baitalahmi: gama daga cikin ’ya’yansa na zaɓo sarki.” (Aya ta 1) Jehobah bai faɗa sunan mutumin ba amma ya faɗa kawai cewa wanda ya zaɓa yana cikin ’ya’yan Jesse. Sa’ad da Sama’ila yake tafiya zuwa Bai’talami, wataƙila ya yi mamaki, ‘Yaya zan san ɗan Jesse wanda Jehobah ya zaɓa?’
Sa’ad da ya isa Bai’talami, Sama’ila ya shirya Jesse da ’ya’yansa don su yi rabo a hadaya. Sa’ad da Eliab, ɗa na fari ya shigo, surarsa ta jawo hankalin Sama’ila farat ɗaya. Sama’ila ya yi tunani cewa surar Eliab ya dace ga sarki sai ya ce wa kansa: “Lallai shafaffe na Ubangiji yana gabansa.”—Aya ta 6.
Amma, Jehobah yana ganin abu a hanya dabam. Ya ce wa Sama’ila: “Kada ka dubi fuskarsa, ko kuwa tsawon jikinsa: gama na ƙi shi.” (Aya ta 7) Tsawo da kuma kyaun Eliab bai burge Jehobah ba. Jehobah yana gani fiye da sura da bayanuwar mutum.
Jehobah ya bayyana wa Sama’ila: “Gama ganin Ubangiji ba kamar na mutum ba ne: gama mutum yana duban aini, amma Ubangiji yana duban zuciya.” (Aya ta 7) Babu shakka, zuciya ce, wato, mutum na ciki, tushen tunanin mutum, halayensa, da sosuwar zuciyarsa ne Jehobah yake dubawa. ‘Mai auna zukata’ ya ƙi Eliab, har ma ’ya’yan Jesse shida da suka zo wurin Sama’ila.—Misalai 17:3.
Jesse yana da sauran ɗa guda, Dauda, autansu, wanda yake “kiwon tumaki.” (Aya ta 11) Sai aka kirawo Dauda daga daji zuwa wurin Sama’ila. Sai Jehobah ya gaya wa Sama’ila: “Tashi, ka shafe shi: gama wannan shi ne.” (Aya ta 12) Hakazalika, Dauda “dai ja ne, mai-kyaun fuska, mai-daɗin gani kuwa.” Amma dai zuciyarsa ne ya sa Allah ya amince da shi.—1 Sama’ila 13:14.
A wannan duniyar da ake cika damuwa da surar mutum, za mu iya samun ƙarfafa don sanin cewa surar mutum ba ta burge Jehobah Allah. Ba ya kallon tsawon mutum ko da wasu suna ɗaukan sa kamar mutum mai kyaun sura. Abin da kake ciki ne, wato, zuciyarka ne Jehobah yake kallo. Shin sanin hakan ya motsa ka ka so samun irin halayen da za su sa ka zama kyakkyawa a idanun Allah?