Jehobah Yana Son ka Zauna “Lafiya Ƙalau”
SA’AD da aukuwa mafi haɗari a tarihi suka ɓarke, Allah Mai Iko zai tabbatar da cewa dukan waɗanda suka sami amincewarsa ‘za su tsira.’ (Joe 2:32) Amma, a gaskiya, Jehobah a koyaushe yana son ya ceci mutane daga lahani. Tun da yake ‘a wurinsa maɓulɓular rai ta ke,’ yana ɗaukan dukan yan Adam da tamani, waɗanda suka cancanci samun kāriya.—Zab. 36:9.
Bayin Allah masu aminci na dā suna da ra’ayi irin nasa game da rai. In ji Farawa 33:18, Yakubu da iyalinsa sun gama tafiya mai haɗari “lafiya.” Yakubu ya dogara ne ga Jehobah domin samun kāriya, amma kuma ya ɗauki matakai masu amfani domin ya kāre dukan waɗanda suka yi tafiya tare da shi. (Far. 32:7, 8; 33:14, 15) Ta wajen yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, za ka iya ƙara kiyaye lafiyarka da ta wasu. Bari mu ga yadda wannan gaskiyar ta shafi waɗanda suke gina Majami’un Mulki, da makamancin ayyukan da kuma masu yin aikin agaji a lokacin bala’i.
Kāre Lafiya a Ƙarƙashin Dokar Musa
Dokar Musa ta bukaci mutanen Allah su bi umurnin da aka ba da na kāre lafiya. Alal misali, an bukaci Ba’isra’ila da ke gina gida ya ja rawani soro a saman gidan. Domin mutane sau da yawa suna sama a kan rufin gidajensu, kuma rawanin soron zai hana su faɗowa. (1 Sam. 9:26; Mat. 24:17) Idan haɗari ya faru domin ba a bi wannan dokar kāre lafiya ba, Jehobah zai ɗora wa maigidan alhakin hakan. —K. Sha 22:8.
Dokar ta kuma shafi rauni da dabbobi na gida suka yi wa mutane. Idan bijimi ya kashe mutum ta wurin tunkaya, mai shi zai kashe bijimin domin ya tsare lafiyar sauran mutanen. Domin ba za ya ci ko kuma sayar da naman ga wasu domin abinci ba, kashe wancan dabbar babbar hasara ce. Amma a ce bayan da bijimin ya ji wa mutum rauni, mai shi bai riƙe dabbar ba. Menene zai faru? Idan wancan bijimin ya sake kashe wani, da bijimin da mai shi za a kashe su. Wannan dokar ta sa dukan wanda yake da halin sakaci a kan dabbobinsa ya sake tunani.—Fit. 21:28, 29.
Dokar ta sake ƙarfafa yin amfani da kayan aiki a hanyar da ta dace. Isra’ilawa da yawa suna amfani da gatari domin sare ice. Idan kan gatarin ya kuɓuce daga ƙotar kuma ya kashe wani da ke tsaye a wurin, mai sare icen zai gudu zuwa birnin mafaka. An bukace shi ya zauna a wurin sai babban firist ya mutu, wadda yake nufin cewa mai kisan kai ba da saninsa ba za ya rabu da iyalinsa da gida na shekaru. Wannan shirin ya koyas da al’umar cewa rai yana da tsarki ga Jehobah. Mutum da yake da ra‘ayi irin na Allah yana ajiye kayan aikinsa da kyau kuma yin amfani da su a hanyar kiyaye lafiya.—Lit. Lis. 35:25; K. Sha 19:4-6.
Da waɗannan dokoki, Jehobah ya nuna sarai cewa yana son mutanensa su kiyaye lafiyar ciki a cikin gida da waje. Waɗanda suka jawo mutuwa ko rauni ga wasu, ko ta wurin hatsari, suna da hakki a gabansa. Tunanin Jehobah a al’amarin kiyaye lafiya ba ta sāke ba. (Mal. 3:6) Har ila yana son mutane su guje wa ji wa kansu da kuma wasu rauni. Wannan musamman gaskiya ne yayin da muke gina da kuma kula da gine-gine da aka keɓe domin bautar gaskiya.
Kiyaye Lafiya a Tsarin Gini
Muna daukan gini da kuma kula da Majami’un Mulki, Majami’un taro, da kuma su rassa kamar gata ce babba. Za a iya faɗin haka kuma game da aiki da muke yi a tsarin taimakon masu bala’i. A dukan lokatai, muna so mu yi aiki mai kyau domin rashin iyawa ko ma a yin ayyuka masu sauƙi, za su iya jawo mana da kuma wasu hatsari. (M. Wa. 10:9) Sarai fa, ta wurin gina hali na yin aiki tare da kiyaye lafiya, za mu guje wa haɗarurruka.
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Fahariyar samari ƙarfinsu ne, jamalin tsofaffi kuma furfura ne.” (Mis. 20:29) Ana bukatar ƙarfin ƙuruciya domin a yi ayyuka masu nauyi. Amma ma’aikata masu furfura, waɗanda suka ƙware a sana’ar gine-gine suna yi kuma gama aiki da kyau da hannayensu da kuma kayan aikinsu. Kuma a wani lokaci, waɗanda yanzu sun manyanta suna amfani da ƙarfinsu na matasa don su yi aiki mai ƙarfi. Idan kai sabon mai aiki ne, ka lura da yadda gogaggun ma’aikata suke aikinsu, ka kuma bi ja-gorarsu. Idan kana so ka koya, ’yan’uwa gogaggu a gine-gine za su koya maka abubuwa da yawa. Waɗannan sun haɗa da yadda za a yi amfani da kayan aiki masu haɗari da kuma ɗaga kaya masu nauyi. Da haka za ka yi aiki mai amfani, lafiya, da kuma da farin ciki.
Ya kamata ma’aikata a filin gine-gine su zama a shirye a kowanne lokaci. Yanayoyi suna canjawa da wuri. Wurin da a dā ƙasa take da ƙarfi, yanzu za ta iya samun rami. Wasu a rukunin wataƙila sun kau da tsani, katako, ko kuma bokitin fenti. Idan ba ka mai da hankali ba, za ka yi saurin jin rauni. Dokokin kiyaye lafiya yawanci na bukatar cewa ma’aikata a fili su yi amfani da kayan tsaro na kai. Tabaran kāre idanu, hular kwano, da kuma takalman da suka dace zai iya tsare ka daga haɗarurruka a filin gine-gine. Amma za ka sami tsaro kaɗai idan ka ajiye kayan aiki da kyau kuma ka saka su.
Ko da wasu kayan aiki za su bayyana da sauƙin yin aiki da su, sarrafa su da kyau tana bukatar koyo da kuma gwaji. Idan ba ka san yadda za ka yi amfani da wani kayan aiki da ka ke bukata ba, ka gaya wa ɗan’uwa da ke lura da aikin. Zai shirya a koya maka sosai. Filako ko kuma sanin kasawarka, inganci ne da ake bukata. Alhali, bukata ce idan za ka kauce wa ji wa kanka rauni da kuma wasu a filin gine-gine.—Mis. 11:2.
Faɗowa sune manyan sanadi na jin rauni a ayyukan gine-gine. Kafin a hau tsani ko kuma sikafir, a tabbata cewa kayan aikin yana da dukan fuskoki kuma an kafa ta a yanayi mai kyau. Idan za ka yi aiki a kan sikafir ko kuma a rufin ɗaki, ja-gorar za ta bukaci a saka gami ko kuma garkuwa da za ya tare mutum daga faɗowa. Ka tambayi mai kula da aikin idan kana da tambayoyi game da yin aiki a wurare masu tsawo.a
Yayin da adadin masu bauta wa Jehobah suke ƙaruwa a dukan duniya, haka kuma bukatar gina Majami’un Mulki da kuma wasu rassa da ake amfani da su domin ci gaban bautar Allah ta gaskiya ke ƙaruwa. An ba waɗanda suke lura da aiki a filayen gine-gine na Majami’ar Mulki da kuma wasu makamancinsu hakkin kāre tumakin Jehobah masu tamani da suke aiki a ƙarƙashin ja-gorarsu. (Isha. 32:1, 2) Idan kana da gatan yin ja-gorar ’yan’uwanka maza da mata a tsarin gini, kada ka manta da muhimmancin kiyaye lafiya. Ka tabbata cewa filin yana da tsabta da marar abin haɗari. Da kirki amma da ƙarfi ka bayana yadda za a yi aiki babu haɗari ga waɗanda suke bukatar tunasarwa. Kada ka yarda yara ko kuma ma’aikata marasa basira su shiga wurare masu haɗari. Ka hangi haɗari da ma’aikatan za su fuskanta, kuma ka shirya su domin su yi aiki lafiya. Ka tuna, makasudinmu shi ne mu gama aiki babu haɗari.
Matsayin Ƙauna
Gina Majami’un Mulki da kuma wasu gine-gine da ake amfani da su a bautar gaskiya ta ƙunshi aiki da zai iya zama da haɗari. Saboda haka, waɗanda suke saka hannu a irin waɗannan ayyuka sai su mai da hankali. Ta wurin yin biyayya da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, yin biyayya ga ja-gorar da aka kafa domin yin aikin, da kuma yin amfani da hikima, za ka guje wa haɗari da kuma kiyaye ’yan’uwa masu aiki daga lahani kuma.
Wane babban dalili ne muke da shi na kiyaye lafiyarmu? Ƙauna ce. Hakika, ƙauna ga Jehobah yana motsa mu mu daraja rai, kamar yadda yake yi. Kuma ƙauna ga mutane tana hana mu yin abu da halin babu ruwana da zai iya yi musu la’ani. (Mat. 22:37-39) Saboda haka, bari mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu sa waɗanda suke aiki a tsarin gine-ginenmu su kasance “lafiya.”
[Hasiya]
a Ka duba akwatin nan “Yadda Za a Yi Aiki Lafiya a Kan Tsanuka” a shafi na 30.
[Akwati/Hoton da ke shafi na 30]
Yadda Za a Yi Aiki Lafiya a Kan Tsanuka
A shekarun bayan nan a ƙasar Amirka, masu aiki fiye da 160,000 sun ji rauni sa’ad da suka faɗi daga tsanuka. Ƙari ga haka, mutane 150 sun mutu daga irin wannan faɗuwa. Duk inda kake da zama kuma kana aiki, ga wasu ƙa’idodi da za su iya taimaka maka ka guji faɗuwa daga kan tsani.
◇ Kada ka yi amfani da tsani mai rawa ko kuma da ya lalace, kuma kada ka gyara irin wannan tsanin. Ka halaka shi.
◇ Dukan tsanuka suna da ainihin nauyin kaya da aka tsara su su ɗauka. Ka tabbata cewa nauyinka da na kayan aikinka ba su wuce nauyin tsani da kake son ka yi amfani da shi ba.
◇ Ka kafa tsaninka a ƙasa marar gargada. Kada ka kafa shi a kan wani abu mai rawa, kamar dakali ko kuma a kan bokiti da akwatuna.
◇ A koyaushe ka sa tsanin a gabanka sa’ad da kake hawa ko kuma sauka.
◇ Kada ka tsaya ko kuma ka zauna a kan matakala biyu na sama na kowane tsani.
◇ Ka yi amfani da tsani idan ya wuce aƙalla kafa uku daga ƙasa ko kuma a kan bangon inda yake. Ka hana tsanin zamewa ta wajen ɗaure ƙafafunsu a ƙasa ko kuma saka filanki a gabansa. Idan ba za ka iya yin waɗannan abubuwa ba, ka sa wani ya riƙe shi sa’ad da kake aiki a kansa. Ka ɗaure tsanin daga sama don kada ya zame.
◇ Kada ka kafa tsani guda biyu don ka ɗaura filanki a kan matakalar tsanin domin magini ya hau kan filankin.
◇ Sa’ad da ka miƙa ƙafafunka ko kuma hannunka sa’ad da kake aiki, kana iya sa tsanin ya yi rawa. Ka guji irin wannan miƙewa mai haɗari. Ka riƙa ƙaura da tsanin a kowane lokaci yadda bukata ta kama don ka yi kusa da inda kake aiki.
◇ Idan ya zama dole za ka yi aiki a kan tsanin da ke gaban kofa da ke rufe, ka sa alamar faɗakarwa a ƙofar kuma ka kulle ta. Idan ba zai yiwu ba ka kulle ƙofar, ka sa alama don ka faɗakar da waɗanda za su wuce ta ƙofar.
◇ Mutum ɗaya ne zai hau tsani sai dai an yi tsanin ya ɗauki mutane biyu.b
[Hasiya]
b Za a iya samun ƙarin bayanai game da yin aiki a kan tsanuka a fitowar Awake! na 8 ga Agusta, 1999, shafuffuka na 22-24.
[Hoton da ke shafi na 29]
Dokar Musa ta bukaci a saka rawani bisa gidan bene