Kana Bin Kristi Sosai Kuwa?
“Kuna kuwa yin tafiya haka nan . . . ku yalwata gaba gaba a ciki.”—1 TAS. 4:1.
1, 2. (a) Waɗanne muhimman abubuwa ne mutane da yawa a zamanin Yesu suka shaida? (b) Me ya sa zamanin mu ma yake da muhimmanci?
KA TAƁA yin tunanin yadda zai iya zama abin ban mamaki ka kasance a raye lokacin da Yesu yake duniya? Kana iya yin tunanin samun warkarwa daga Yesu kuma ka tsira daga wahala na wasu ciwo. Ko kuma za ka yi la’akari da farin cikin gani da kuma saurarar Yesu, wato mu iya koya daga wurinsa ko kuma mu gan shi yana wasu mu’ujizai. (Mar. 4:1, 2; Luk 5:3-9; 9:11) Da zai zama babban gata mu kasance a raye lokacin da Yesu yake dukan waɗannan ayyuka! (Luk 19:37) Babu wata tsara tun daga lokacin da ta taɓa shaida irin waɗannan abubuwa, kuma ba za a maimaita abin da Yesu ya cim ma a duniya ta hanyar “hadayar kansa.”—Ibran. 9:26; Yoh. 14:19.
2 Amma, a zamaninmu ma an yi aukuwa masu muhimmanci. Me ya sa hakan? Muna cikin lokacin da Nassosi suka annabta a matsayin “kwanaki na ƙarshe.” (Dan. 12:1-4, 9; 2 Tim. 3:1) A cikin wannan lokacin, an jefo da Shaiɗan daga sama. Ba da daɗewa ba, za a ɗaure da kuma jefa shi “cikin rami marar-matuƙa.” (R. Yoh. 12:7-9, 12; 20:1-3) A wannan lokacin ne kuma muke da gata mai girma na shelar “bishara kuwa ta mulki” a dukan duniya, muna gaya wa mutane game da bege na Aljanna da take zuwa, wannan aiki ne da ba za a sake yinsa ba.—Mat. 24:14.
3. Kafin ya hau sama, menene Yesu ya gaya wa mabiyansa su yi, kuma menene wannan ya ƙunsa?
3 Kafin ya hau sama, Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Za ku zama shaiduna kuma cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya, har kuma iyakan duniya.” (A. M. 1:8) Wannan aiki zai ƙunshi ayyuka na koyarwa da za a yi a dukan duniya. Menene za a cim ma ta wannan aikin? Za a samu almajirai, wato, ƙarin mabiya na Kristi kafin ƙarshen ya zo. (Mat. 28:19, 20) Menene za mu yi idan muna son mu yi nasara wajen cika umurni na Kristi?
4. (a) Furcin Bitrus da ke 2 Bitrus 3:11, 12 ya nanata wane bukata? (b) A kan menene muke bukata mu kasance a faɗake?
4 Ka yi la’akari da wannan furci na manzo Bitrus: “Waɗanne irin mutane ya kamata ku zama cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma, kuna sauraron ranar Allah, kuna kuwa marmarin zuwanta ƙwarai!” (2 Bit. 3:11, 12) Kalmomin Bitrus ya nanata bukatar yin tsaro a waɗannan kwanaki na ƙarshe kuma mu tabbata cewa rayuwarmu ta dangana ga yin ayyuka na ibada. Irin waɗannan ayyuka sun haɗa da yin wa’azin bishara. Saboda haka, abin farin ciki ne mu lura da himma da ’yan’uwanmu a dukan duniya suke cika umurnin Kristi na yin wa’azi! Duk da haka, mun fahimci cewa muna bukatan mu mai da hankali kada matsi na yau da kullum na duniyar Shaiɗan da kuma namu sha’awoyi na jiki da muka gāda su rage himmarmu ga hidimar Allah. Saboda haka, bari mu lura da yadda za mu tabbata cewa mun ci gaba da bin Kristi.
Ka Karɓi Hakkin da Allah Yake Bayarwa
5, 6. (a) Game da menene Bulus ya yaba wa ’yan’uwansa masu bi a Urushalima, kuma ya yi musu gargaɗi game da menene? (b) Me ya sa bai kamata mu yi wasa da hakkin da Allah ya ba mu ba?
5 A cikin wasiƙarsa zuwa ga Kiristoci a Urushalima, manzo Bulus ya yaba wa ’yan’uwansa masu bi don haƙurinsu na dā cikin aminci har sa’ad da suke fuskantar tsanantawa. Ya ce: “Ku tuna da kwanakin dā, inda kuka sha kokuwa mai-zafi ta wahala, bayan da kuka sami haske.” Hakika, Jehobah ya tuna da tafarkinsu na aminci. (Ibran. 6:10; 10:32-34) Babu shakka, kalmomin yabo na Bulus masu daɗaɗa rai sun ƙarfafa waɗannan Kiristoci Ibraniyawa sosai. Amma dai, a cikin wannan wasiƙar, Bulus ya yi musu gargaɗi game da halin ’yan Adam da idan ba a mai da hankali ba, zai iya rage himmar mutum a hidimar Allah. Ya faɗa cewa Kiristoci za su yi hankali kada su “ƙi yarda,” ko kuma ba da hujja, bin umurnin Allah.—Ibran. 12:25.
6 Wannan gargaɗi game da ‘ƙin yarda’ yin ayyuka da Allah ya ba da ya shafi Kiristoci ma a yau. Muna bukatan mu ƙudura aniyar cika hakkinmu na Kirista sosai kuma mu ci gaba da kasancewa da himma a hidimar Allah. (Ibran. 10:39) Ballantana ma, yin tsarkakkar hidima batu ne na rai da kuma mutuwa.—1 Tim. 4:16.
7, 8. (a) Me zai taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da himma a hidimar Allah? (b) Idan mun yi hasarar himmar da muke da shi a dā, menene ya kamata mu tuna game da Jehobah da kuma Yesu?
7 Menene zai taimaka mana mu guji ba da hujja ga cika farillanmu ga Allah? Hanya ɗaya mai muhimmanci na yin yaƙi da wannan hali ita ce yin bimbini a kai a kai game da ma’anar alkawarin keɓe kanmu. Hakika, mun yi wa Jehobah alkawari cewa za mu saka yin nufinsa farko a rayuwarmu, kuma muna son mu cika wannan alkawarin. (Karanta Matta 16:24.) Saboda haka, wani lokaci muna bukatan mu tambayi kanmu: ‘Shin har ila, ina ƙuduri aniyar yin rayuwa da ta jitu da keɓe kaina ga Allah yadda nake da shi a lokacin baftisma ta? Ko kuma na yi rashin himma da nake da shi a dā da shigewar shekaru?’
8 Idan binciken kanmu ya nuna mana cewa mun rage himmarmu a hidimar Jehobah, zai yi kyau mu tuna da kalmomin ƙarfafa na annabi Zafaniya. Ya ce: “Kada ki yi kasala. Ubangiji Allahnki yana cikin tsakiyarki. Mai-iko ne wanda za ya yi ceto. Za ya yi farinciki a bisa kanki da murna.” (Zaf. 3:16, 17) An fara yin amfani da waɗannan kalmomi masu ban ƙarfafa ga Isra’ila ta dā wadda ta dawo daga bauta a Babila. Amma dai, wannan ƙarfafa har ila tana da amfani ga mutanen Allah a yau. Tun da shike aikin da muke yi na Jehobah ne, ya kamata mu tuna cewa Jehobah da Ɗansa suna goyon bayanmu da kuma ƙarfafa mu mu cika hakkin da Allah ya ba mu. (Mat. 28:20; Filib. 4:13) Idan mun yi ƙoƙari mu ci gaba da yin aikin Allah da himma, zai albarkace mu kuma ya taimaka mana mu samu ci gaba a ruhaniya.
Ka ‘Fara Biɗan Mulkin’ da Himma
9, 10. Menene almarar Yesu game da babban biki yake nufi, kuma wane darasi za mu koya a ciki?
9 Yayin da yake cin abinci a gidan wani shugaban Farisawa, Yesu ya ba da misali game babban biki. A cikin wannan misali, ya kwatanta zarafi da aka miƙa wa mutane dabam-dabam don su shiga hanyar samun Mulki na samaniya. Ya kuma ba da misalin abin da yake nufi a “kawo dalilai.” (Karanta Luka 14:16-21.) Baƙi da aka gayyata sun ba da dalilai na rashin halartan bikin. Wani ya ce ya sayi fili kuma yana son ya je ya duba. Wani kuma ya ce ya sayi shanu kuma yana son ya gwada su. Har illa wani ya ce: ‘Ba zan iya zuwa ba. Na auro mace.’ Waɗannan dalilai ba na ƙwarai ba ne. Wanda ya sayi fili ko garke yana gwada su kafin ya saya, saboda haka babu wani bukata ta gaggawa na gwada su bayan hakan. Kuma me ya sa sabon aure zai hana wani daga karɓan wannan gayyatar mai muhimmanci? Ba abin mamaki ba ne mai masauki a misalin ya yi fushi sosai!
10 Dukan mutanen Allah za su iya koyi darasi daga almarar Yesu. Wane darassi ne muka koya? Bai kamata mu ƙyale al’amura na kanmu, kamar waɗanda aka ambata a kwatancin Yesu, su fi hidimarmu ga Allah muhimmanci ba. Idan Kirista bai ajiye al’amura na kai a inda suka dace ba, himmarsa a hidima za ta rage a hankali. (Karanta Luka 8:14.) Don mu hana hakan faruwa, za mu bi gargaɗin Yesu: “Ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara muku su.” (Mat. 6:33) Abin ƙarfafa ne mu ga cewa bayin Allah, wato, yara da manya suna amfani da wannan shawara mai muhimmanci! Hakika, mutane da yawa sun ɗauki matakai don su sauƙaƙa salon rayuwarsu don su ƙara ba da lokaci sosai a hidima. Sun koya daga abin da suka fuskanta cewa kasancewa da himma wajen ‘fara biɗan mulkin’ zai kawo mana farin ciki na gaske da kuma gamsuwa mai girma.
11. Wane labari na Littafi Mai Tsarki ya kwatanta muhimmancin kasancewa da himma da kuma bauta wa Allah da zuciya ɗaya?
11 Don a nuna muhimmanci kasancewa da himma a hidimar Allah, ka lura da wani abin da ya faru a rayuwar Sarki Jehoash na Isra’ila. Don yana damuwa cewa Suriya za ta ci Isra’ila a yaƙi, Jehoash ya zo yana yi wa Elisha kuka. Annabin ya umurce shi ya harba kibiya a tagar da ta fuskanci Suriya, wadda take nuna nasara ta wurin hannun Jehobah a kan wannan al’umma. Wannan babu shakka ya kamata ya ƙarfafa sarkin. Elisha ya sake gaya wa Jehoash ya ɗauki kibiyoyin ya bugi ƙasa da su. Jehoash ya bugi ƙasa sau uku. Elisha ya yi fushi da wannan, don buga ƙasar sau biyar ko shida zai nuna zai “buga Syria har [ya] cinye ta.” Amma yanzu sau uku kawai Jehoash zai ci yaƙi. Domin ya aikata da rashin himma, Jehoash ya sami nasara kaɗan. (2 Sar. 13:14-19) Wane darasi za mu iya koya daga wannan labari? Jehobah zai albarkace mu a yalwace idan mun yi aikinsa da zuciya ɗaya da kuma himma.
12. (a) Me zai taimaka mana mu riƙe himmarmu a hidimar Allah yayin da muke jimrewa da kaluɓale na rayuwa? (b) Ka faɗa yadda kake amfana daga shagalawa a cikin hidima.
12 Kaluɓale na rayuwa suna gwada himmarmu da kuma ibadar mu a hidimar Allah. ’Yan’uwa da yawa suna jimre da gwaji da yanayi na tattalin arziki. Wasu sun yi sanyin gwiwa domin ciwo mai tsanani ya rage abin da za su iya yi a hidimar Jehobah. Har ila, kowannenmu zai iya ɗaukan matakai don mu tabbata cewa mun riƙe himmarmu kuma mun ci gaba da bin Kristi sosai. Don Allah ka lura da wasu shawarwari da nassosi da aka lissafta a cikin akwati “Menene Zai Taimaka Maka Ka Ci Gaba da Bin Kristi?” Ka yi la’akari da yadda za ka yi amfani da su daidai iyawarka. Idan ka yi hakan, za ka girbe fa’idodi na ainihi. Shagalawa a cikin hidima tana ƙarfafa mu, yana kyautata rayuwarmu, kuma yana kawo mana salama mafi girma da kuma farin ciki. (1 Kor. 15:58) Ƙari ga haka, yin hidima ga Jehobah da zuciya ɗaya tana taimaka mana mu riƙa “sauraron ranar Allah, [muna] marmarin zuwanta ƙwarai.”—2 Bit. 3:12.
Ka Bincika Yanayinka da Kyau
13. Ta yaya za mu iya sanin abin da hidima da dukan zuciya take nufi a gare mu?
13 Yana da kyau mu tuna cewa, yin hidima da dukan zuciya ba batun yawan lokaci da muke yi a hidima ba ne. Yanayin mutane ya bambanta. Mutumin da yake yin sa’a ɗaya ko biyu a hidimar fage kowace wata zai gamsar da Allah sosai idan hakan ne lafiyarsa ta ƙyale shi ya yi. (Gwada Markus 12:41-44.) Saboda haka, don mu tabbata abin da hidima ga Allah da zuciya ɗaya take nufi a gare mu, muna bukatar mu bincika iyawarmu da kuma yanayinmu da kyau. A matsayin masu bin Kristi, muna kuma bukatar mu daidaita ra’ayinmu da na shi. (Karanta Romawa 15:5; 1 Kor. 2:16) Menene Yesu ya saka da farko a rayuwarsa? Ya gaya wa taron jama’a a Kafarnahum: “Dole in kai Bishara ta mulkin Allah . . . gama saboda wannan aka aiko ni.’ (Luk 4:43; Yoh. 18:37) Da himmar Yesu a hidima a zuci, ka bincika yanayinka ka ga ko za ka iya faɗaɗa hidimarka.—1 Kor. 11:1.
14. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya faɗaɗa hidimarmu?
14 Bincika yanayinmu sosai zai iya sa mu kammala cewa za mu iya ƙara yawan lokaci da muke yi a hidima. (Mat. 9:37, 38) Alal misali, matasa da yawa da suka gama makaranta kwanan nan sun faɗaɗa hidimarsu kuma yanzu suna moran farin ciki da ake samu daga yin hidimar majagaba da himma. Za ka so ka more irin wannan farin cikin? Wasu ’yan’uwa maza da mata sun bincika yanayinsu kuma sun shawarta cewa za su iya ƙaura zuwa wani wuri a ƙasarsu, ko kuma ƙasar waje, inda akwai bukata mai girma na masu shelar Mulki. Har illa, wasu sun koyi wani yare don su taimaka wa mutane da suke wani yare. Ko da yake faɗaɗa hidimarmu tana iya zama kaluɓale, tana kawo albarka masu yawa, kuma muna iya taimaka wa mutane da yawa “su kawo ga sanin gaskiya.”—1 Tim. 2:3, 4; 2 Kor. 9:6.
Misalan Littafi Mai Tsarki da Za a Bi
15, 16. Misalansu su wanene za mu yi koyi da shi wajen zama mabiyan Kristi masu himma?
15 Yaya wasu da suka zama manzanni suka aikata sa’ad da Yesu ya kira su su zama mabiyansa? Game da Matta, labarin ya ce: “Shi kuwa ya bar abu duka, ya tashi ya bi shi.” (Luk 5:27, 28) Game da Bitrus da Andarawus, waɗanda suke kama kifi, mun karanta: “Nan da nan suka bar tarori, suka bi shi.” Daga nan kuma Yesu ya wuce sai ya ga Yakub da Yohanna, suna gyaran tarorinsu tare da ubansu. Ta yaya suka aikata ga gayyatar Yesu? “Nan da nan suka bar jirgi da ubansu, suka bi shi.”—Mat. 4:18-22.
16 Wani misali kuma mai kyau shi ne na Shawulu, wanda ya zama manzo Bulus. Ko da yake ya tsananta wa mabiyan Kristi sosai, ya canja tafarkinsa kuma ya zama “santali zaɓaɓe” don ya yi shaidar sunan Kristi. “Nan da nan kuwa [Bulus] ya yi ta wa’azin Yesu cikin majami’u, shi Ɗan Allah ne.” (A. M. 9:3-22) Ko da shike ya jimre wahala da kuma tsanani, Bulus bai taɓa rashin himmarsa ba.—2 Kor. 11:23-29; 12:15.
17. (a) Menene muradinka a batun bin Kristi? (b) Waɗanne albarka muke morewa domin yin nufin Jehobah da dukan zuciyarmu da kuma ƙarfinmu?
17 Babu shakka, ya kamata mu yi koyi da misalai masu kyau na waɗannan almajiran kuma mu aikata nan da nan babu son kai ga gayyata na zama mabiyan Kristi. (Ibran. 6:11, 12) Waɗanne albarka za mu more yayin da muka ci gaba da ƙoƙari don mu bi Kristi da himma da kuma sosai? Muna samun farin ciki na gaske yayin da muke yin nufin Allah kuma muna moran gamsuwa da take zuwa daga karɓan ƙarin gata na hidima da kuma hakki a cikin ikilisiya. (Zab. 40:8; karanta 1 Tasalonikawa 4:1.) Hakika, yayin da muke yin ƙoƙari sosai a bin Kristi, za mu more irin wannan albarka na dindindin kamar kwanciyar hankali, gamsuwa, wadar zuci, amincewar Allah, da kuma begen samun rai har abada.—1 Tim. 4:10.
Ka Tuna?
• Wane aiki ne mai muhimmanci aka ba mu, kuma yaya ya kamata mu ɗauke ta?
• Wane hali na ’yan Adam ya kamata mu guji, kuma me ya sa?
• Wane binciken kanmu ya kamata mu yi?
• Menene zai taimaka mana mu ci gaba da bin Kristi?
[Akwati/Hoton da ke shafi na 27]
Menene Zai Taimaka Maka Ka Ci Gaba da Bin Kristi?
▪ Karatun Kalmar Allah kullum, da kuma yin bimbini a kan abin da ka karanta.—Zab. 1:1-3; 1 Tim. 4:15.
▪ Ka riƙa addu’a kullum don tallafawar da kuma ja-gorar ruhun Allah.—Zech. 4:6; Luk 11:9, 13.
▪ Ka yi tarayya da waɗanda suke nuna himma da dukan zuciyarsu don hidima.—Mis. 13:20; Ibran. 10:24, 25.
▪ Ka gane gaggawar lokaci da muke ciki.—Afis. 5:15, 16.
▪ Ku mai da hankali ga mugun sakamakon “kawo dalilai.—Luk 9:59-62.
▪ Ka yi tunani a kai a kai game da alkawarin keɓe kanka da kuma albarka masu yawa da ake samu daga bauta wa Jehobah da bin Kristi da dukan zuciya.—Zab. 116:12-14; 133:3; Mis. 10:22.