Maraba Da Zuwa Hanya Mafi Kyau Ta Rayuwa!
“Ko mu rayu fa, ko mu mutu, na Ubangiji muke.”—ROM. 14:8.
1. Yesu ya koyar da menene game da hanyar rayuwar da ta fi kyau?
JEHOBAH yana son mu more hanyar rayuwa da ta fi kyau. Mutane suna iya rayuwa a hanyoyi dabam-dabam, amma hanya ɗaya ce ta fi kyau. Hanya mafi kyau na yin rayuwa ita ce mu yi rayuwar da ta jitu da Kalmar Allah kuma mu koya daga Ɗansa, Yesu Kristi. Yesu ya koya wa mabiyansa su bauta wa Allah cikin ruhu da gaskiya, kuma ya ba su umurni su yi almajirantarwa. (Mat. 28:19, 20; Yoh. 4:24) Ta wajen yin rayuwar da ta jitu da umurnin Yesu, muna faranta wa Jehobah rai kuma za mu more albarkarsa.
2. Yaya mutane da yawa suka aikata ga saƙon Mulki a ƙarni na farko, kuma menene yake nufi a kasance na “Tafarkin”?
2 Sa’ad da mutane masu tawali’u suka zama masu bi kuma suka yi baftisma, muna da dalilai masu kyau na gaya musu, “Maraba da zuwa hanya mafi kyau ta rayuwa!” A ƙarni na farko na Zamaninmu, mutane dubbai daga al’ummai dabam-dabam sun karɓi gaskiya kuma suka ba da shaida a fili na ibadarsu ga Allah ta wajen yin baftisma. (A. M. 2:41) Waɗannan almajirai na farko sun bi “Tafarkin.” (A. M. 9:2; 19:23) Wannan furcin ya dace domin waɗanda suka zama mabiyan Kristi suna bin tafarkin rayuwa da ta kasance bisa bangaskiya ga Yesu Kristi da kuma yin koyi da misalinsa.—1 Bit. 2:21.
3. Me ya sa mutanen Jehobah suke yin baftisma, kuma mutane nawa ne aka yi wa baftisma shekaru goma da suka shige?
3 Aikin almajirantarwa ya ƙaru a waɗannan kwanaki na ƙarshe kuma yanzu ana yinsa a fiye da ƙasashe 230. A cikin shekaru goma da suka shige, fiye da mutane 2,700,000 sun tsai da shawara su bauta wa Jehobah kuma a yi musu baftisma wajen nuna alamar keɓe kansu a gare shi. Wannan avireji ne na mutane fiye da 5,000 a kowane mako! Tsai da shawarar yin baftisma yana bisa ƙaunar Allah, sani na Nassosi, da kuma bangaskiya ga abin da suke koyarwa. Baftisma abu ce mai muhimmanci a rayuwarmu, domin tana nuna somawar dangantaka na kud da kud da Jehobah. Nuni ne kuma cewa muna da tabbaci zai taimaka mana mu bauta masa da aminci, kamar yadda ya taimaki bayinsa na dā su bi hanyarsa.—Isha. 30:21.
Me Ya Sa Za Ka Yi Baftisma?
4, 5. Ka ambata wasu albarka da amfani na yin baftisma.
4 Wataƙila ka koyi sanin Allah, ka yi canje-canje a rayuwarka, kuma yanzu kai mai shela ne da ya yi baftisma. Irin wannan ci gaba abin yabo ne. Amma ka keɓe kanka ga Allah cikin addu’a, kuma kana begen cewa za ka yi baftisma? Ta wurin nazarinka na Littafi Mai Tsarki, wataƙila yanzu ka san cewa ya kamata ka mai da hankali ga yabon Jehobah a rayuwarka, ba kawai faranta wa kanka rai ba ko kuma tara abubuwan mallaka ba. (Karanta Zabura 148:11-13; Luka 12:15) Saboda haka, waɗanne albarka da kuma amfani ake samu ta yin baftisma?
5 A matsayin Kirista da ya keɓe kansa, rayuwarka za ta kasance da manufa mafi girma. Za ka yi farin ciki domin kana yin nufin Allah. (Rom. 12:1, 2) Ruhu mai tsarki na Jehobah zai sa ka nuna halaye na ibada kamar su salama da bangaskiya. (Gal. 5:22, 23) Allah zai amsa addu’o’inka kuma ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcenka don ka daidaita rayuwarka da Kalmarsa. Hidimarka za ta zama na farin ciki, kuma yin rayuwa a hanyar da Allah ya amince da ita za ta ƙarfafa begenka na rai madawwami. Bugu da ƙari, keɓe kanka da yin baftisma za su nuna cewa kana son ka zama Mashaidin Jehobah.—Isha. 43:10-12.
6. Menene baftismarmu take sanar?
6 Ta wajen keɓe kanmu ga Allah da kuma yin baftisma, muna sanar a fili cewa mu na Jehobah ne. Manzo Bulus ya rubuta: “Daga cikinmu ba wanda ke rayuwa ga kansa ba, ba kuwa wanda ke mutuwa ga kansa. Gama ko muna rayuwa, ga Ubangiji muke rayuwa; ko mutuwa muke yi, ga Ubangiji muke mutuwa; ko mu rayu fa, ko mu mutu, na Ubangiji muke.” (Rom. 14:7, 8) Allah ya ɗaukaka mu ta wajen ba mu ’yancin zaɓe. Sa’ad da muka tsai da shawara mu biɗi wannan tafarkin rayuwa domin muna ƙaunar Allah, muna faranta zuciyarsa. (Mis. 27:11) Baftismarmu alamar keɓe kanmu ne ga Allah da kuma shela a fili cewa Jehobah ne Sarkinmu. Ya nuna cewa muna gefensa a batun ikon mallaka na sararin samaniya. (A. M. 5:29, 32) Jehobah kuma yana tare da mu. (Karanta Zabura 118:6.) Baftisma tana kuma buɗe mana hanyar samun albarka na ruhaniya masu yawa a yanzu da kuma nan gaba.
An Albarkace Su da ’Yan’uwanci da Ke Nuna Ƙauna
7-9. (a) Wane tabbaci ne Yesu ya ba waɗanda suka bar dukan abubuwa kuma suka bi shi? (b) Yaya alkawarin Yesu da ke rubuce a Markus 10:29, 30 yake cika?
7 Manzo Bitrus ya gaya wa Yesu: “Ga mu, mun bar abubuwa duka, mun bi ka; me za mu samu fa?” (Mat. 19:27) Bitrus yana son ya san abin da shi da sauran almajiran Yesu za su samu a nan gaba. Sun yi sadaukarwa masu yawa don su ba da kansu sosai ga aikin wa’azin Mulki. (Mat. 4:18-22) Wane tabbaci ne Yesu ya ba su?
8 A labarin da Markus ya rubuta, Yesu ya nuna cewa almajiransa za su kasance cikin sashen ’yan’uwanci na ruhaniya. Ya ce: “Babu mutum wanda ya bar gida, ko ’yan’uwa maza, ko ’yan’uwa mata, ko uwa, ko uba, ko ’ya’ya, ko gonaki, sabili da ni, da bishara, da ba za ya karɓi riɓi ɗari yanzu cikin wannan zamani, gidaje, da ’yan’uwa maza, da ’yan’uwa mata, da uwaye, da ’ya’ya, da gonaki, game da tsanani; a cikin zamani mai-zuwa kuma rai na har abada.” (Mar. 10:29, 30) Kiristoci na ƙarni na farko, kamar su Lidiya, Akila, Biriskilla, da Gayus suna cikin waɗanda suka yi tanadin “gidaje” kuma suka zama “’yan’uwa maza, da ’yan’uwa mata, da uwaye” ga ’yan’uwa masu bi, kamar yadda Yesu ya yi alkawari.—A. M. 16:14, 15; 18:2-4; 3 Yoh. 1, 5-8.
9 Abin da Yesu ya faɗa yana samun cika mafi girma a yau. “Gonaki” da mabiyansa suka bari suna nuni ga aikin biyan bukata da mutane da yawa, har da masu wa’azi a ƙasashen waje, waɗanda suke iyalin Bethel, bayi masu hidima a ƙasashen waje, da sauransu suka bari da yardan rai domin su faɗaɗa ayyukan Mulki a ƙasashe dabam-dabam. ’Yan’uwa da yawa sun bar gidajensu domin su sauƙaƙa rayuwarsu, kuma yana sa mu farin ciki mu ji labaransu da ke nuna yadda Jehobah ya kula da su da kuma yadda hidimarsu a gare shi ta sa su farin ciki. (A. M. 20:35) Bugu da ƙari, dukan bayin Jehobah da suka yi baftisma suna iya more albarkar ‘fara biɗan mulkin Allah, da adalcinsa’ a matsayin waɗanda suke cikin ’yan’uwanci na Kirista a dukan duniya.—Mat. 6:33.
Kāriya a “Cikin Mabuya”
10, 11. Menene “mabuyan Maɗaukaki,” kuma yaya za mu samu shiga cikinsa?
10 Keɓe kai da baftisma suna kawo wata albarka mai girma, wato, gatan zama a cikin “mabuyan Maɗaukaki.” (Karanta Zabura 91:1.) Wannan wuri ne na alama na kāriya da kwanciyar hankali, da kuma yanayi na kāriya daga lahani na ruhaniya. “Mabuya” ne domin mutanen da ba su da ruhaniya kuma ba sa dogara ga Allah ba su san wurin ba. Ta wurin yin rayuwar da ta jitu da keɓe kanmu da kuma kasancewa da cikakken tabbaci ga Jehobah, muna gaya masa: ‘Kai ne mafakata da marayata kuma; Allahna, a gareka na ke dogara.’ (Zab. 91:2) Jehobah Allah ya zama wurin zamanmu. (Zab. 91:9) Babu wurin da ya fi wannan kyau!
11 Samun shiga “mabuyan” Jehobah yana kuma nufin cewa an albarkace mu da gatan ƙulla dangantaka da shi. Hakan yana somawa da keɓe kai da yin baftisma. Bayan haka, muna ƙarfafa dangantakarmu da Allah ta wajen kusantarsa ta yin nazarin Littafi Mai Tsarki, yin addu’a da dukan zuciyarmu, da kuma cikakkiyar biyayya a gare shi. (Yaƙ. 4:8) Babu wanda ya fi Yesu kusantar Jehobah, kuma bai taɓa daina kasancewa da tabbaci ga Mahaliccin ba. (Yoh. 8:29) Saboda haka, kada mu taɓa yin shakkar Jehobah ko kuma muradinsa da iyawarsa na taimaka mana mu cika alkawarin keɓe kanmu. (M. Wa. 5:4) Tanadi na ruhaniya da Allah ya yi wa mutanensa tabbaci ne cewa yana ƙaunarmu da gaske kuma yana son mu yi nasara wajen bauta masa.
Ka Ɗauki Aljannarmu ta Ruhaniya da Tamani
12, 13. (a) Menene aljanna ta ruhaniya? (b) Ta yaya za mu taimaka wa sababbi?
12 Keɓe kai da baftisma suna kuma buɗe mana hanyar zama a cikin aljanna ta ruhaniya mai albarka. Wuri ne na ruhaniya da babu kamarsa da ’yan’uwa masu bi suke zama tare, inda suke zaman lafiya da Jehobah Allah da kuma juna. (Zab. 29:11; Isha. 54:13) Duniya ba ta da wani abu da za a gwada da aljannarmu ta ruhaniya. Ana ganin hakan musamman a taron ƙasashe inda ’yan’uwanmu daga ƙasashe da yawa, harsuna, da ƙabilai suke taruwa a yanayin salama, haɗin kai, da ƙauna ta ’yan’uwa.
13 Aljanna ta ruhaniya da muke morewa ta bambanta da mummunar yanayi a duniya ta yau. (Karanta Ishaya 65:13, 14.) Ta wajen shelar saƙon Mulki, muna da gatan miƙa wa mutane gayyatar shiga aljanna ta ruhaniya. Albarka ne mu taimaka wa waɗanda suka soma tarayya da ikilisiya kwanan nan kuma za su amfana daga koyarwa a hidima. Ta wurin ja-gorar dattawa, za a albarkace mu da gatan taimaka wa wasu sababbi, yadda Akila da Biriskilla “suka ƙara buɗe [wa Afolos] tafarkin Allah sosai.”—A. M. 18:24-26.
Ka Ci Gaba da Koyo Daga Yesu
14, 15. Waɗanne dalilai masu kyau muke da su na ci gaba da koyo daga Yesu?
14 Muna da dalilai masu kyau na ci gaba da koyo daga wurin Yesu. Kafin ya zo duniya, Yesu ya yi shekaru aru-aru yana aiki tare da Ubansa. (Mis. 8:22, 30) Ya san cewa hanyar rayuwa mafi kyau tana bisa bauta wa Allah da kuma ba da shaida ga gaskiya. (Yoh. 18:37) Yesu ya sani sarai cewa wata hanyar rayuwa da ta bambanta da wannan za ta zama na son kai da rashin basira. Ya san cewa za a gwada shi sosai kuma a kashe shi. (Mat. 20:18, 19; Ibran. 4:15) A matsayin wanda muke bin misalinsa, ya koya mana yadda za mu ci gaba da zama masu aminci.
15 Ba da daɗewa ba bayan da aka yi wa Yesu baftisma, Shaiɗan ya jarrabe shi ya yasar da hanyar rayuwa da ta fi kyau, amma ya ƙi. (Mat. 4:1-11) Wannan ya koya mana cewa ko da menene Shaiɗan ya yi, za mu iya kasancewa da aminci. Wataƙila zai mai da hankali ga waɗanda suke son su yi baftisma da kuma sababbi da suka yi baftisma. (1 Bit. 5:8) Waɗanda suke cikin iyalinmu suna iya hamayya da mu domin an gaya musu ƙarya game da Shaidun Jehobah kuma suna tunanin cewa suna kāre mu. Duk da haka, irin wannan gwajin yana ba mu zarafin nuna halaye masu kyau na Kirista, kamar su daraja da basira, sa’ad da muke amsa tambayoyi da kuma ba da shaida. (1 Bit. 3:15) Irin waɗannan gwaji suna iya shafan waɗanda suka saurare mu a hanyoyi masu kyau.—1 Tim. 4:16.
Ka Manne wa Hanyar Rayuwa Mafi Kyau
16, 17. (a) Waɗanne abubuwa guda uku ne masu muhimmanci da suke rubuce a Kubawar Shari’a 30:19, 20 ake bukata don a samu rai? (b) Yaya Yesu, Yohanna, da Bulus suka goyi bayan abin da Musa ya rubuta?
16 Shekaru 1,500 kafin Yesu ya zo duniya, Musa ya gargaɗi Isra’ilawa su zaɓi hanya mafi kyau ta rayuwa a lokacin. Ya ce: “Ina kira sama da ƙasa su shaida a kanku yau, na sa rai da mutuwa a gabanka, albarka da la’ana: ka zaɓi rai fa, domin ka rayu, da kai da zuriyarka: garin ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka, ka ji muryatasa, ka manne masa.” (K. Sha 30:19, 20) Isra’ila ta yi rashin aminci ga Allah, amma abubuwa uku masu muhimmanci da ake bukata don rayuwa da Musa ya ambata ba su canja ba. Yesu da wasu sun sake ambata su.
17 Na farko, ‘dole ne mu yi ƙaunar Ubangiji Allahnmu.’ Muna nuna cewa muna ƙaunar Allah ta wajen aikatawa cikin jituwa da hanyoyinsa na adalci. (Mat. 22:37) Na biyu, ‘dole ne mu saurari muryar Jehobah’ ta wajen nazarin Kalmar Allah da kuma yin biyayya ga umurninsa. (1 Yoh. 5:3) Hakan na bukatan mu riƙa halartan taron Kirista inda ake tattauna Littafi Mai Tsarki a kai a kai. (Ibran. 10:23-25) Na uku, ‘dole ne mu manne wa Jehobah.’ Ko da menene muke fuskanta, bari a koyaushe muna ba da gaskiya ga Allah kuma mu bi Ɗansa.—2 Kor. 4:16-18.
18. (a) Yaya Hasumiyar Tsaro ta kwatanta gaskiya a shekara ta 1914? (b) Yaya ya kamata mu ji game da hasken gaskiya a yau?
18 Ana samun albarka ta wajen yin rayuwar da ta jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki! A shekara ta 1914, an wallafa wannan furci mai muhimmanci a cikin Hasumiyar Tsaro: “Mu ba masu farin ciki ba ne da aka albarkace su? Allahnmu ba mai aminci ba ne? Idan akwai wanda ya san abin da ya fi wannan kyau, bari ya ɗauka. Idan akwai wani cikinku da ya samu abin da ya fi wannan kyau, muna fatan zai gaya mana. Ba mu san wani abin da ya fi kyau ko rabin kyaun abin da muka samu a cikin Kalmar Allah ba. . . . Ba zai yiwu ba a kwatanta salama, farin ciki da albarka da sani na Allah na gaskiya ya kawo cikin zuciyarmu da rayuwarmu ba. Labarin Hikimar Allah, Adalci, Iko, da Ƙauna ya gamsar da hankalinmu da kuma bukatunmu na sosuwar zuciya. Ba ma biɗan wani abu. Ba abin da muke so fiye da ƙara fahimtar wannan Labari mai ban al’ajabi a cikin zuciyarmu.” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Disamba, 1914, shafuffuka na 377-378) Ba za mu canja godiyarmu don haske na ruhaniya da kuma gaskiya. Hakika, yanzu muna da dalili mai girma na yin farin ciki cewa muna “tafiya cikin hasken Ubangiji.”—Isha. 2:5; Zab. 43:3; Mis. 4:18.
19. Me ya sa waɗanda suka cancanci yin baftisma za su yi hakan babu ɓata lokaci?
19 Idan kana son ka yi “tafiya cikin hasken Ubangiji” amma kai ba Kirista ba ne da ya keɓe kansa kuma ya yi baftisma, kada ka ɓata lokaci. Ka yi duk abin da ake bukata don ka cika farillai na Littafi Mai Tsarki don baftisma, hakan hanya ce ta musamman na nuna godiya ga abin da Allah da Kristi suka yi mana. Ka ba Jehobah dukiyarka na zahiri mafi tamani, wato, ranka. Ka nuna cewa kana son ka yi nufin Allah ta wajen bin Ɗansa. (2 Kor. 5:14, 15) Babu shakka, hakan hanya ce da ta fi kyau na yin rayuwa!
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene baftismarmu take nunawa?
• Keɓe kai ga Allah da baftisma suna kawo wace albarka?
• Me ya sa koyo daga Yesu yake da muhimmanci sosai?
• Menene zai taimaka mana mu manne wa hanyar rayuwa mafi kyau?
[Hoton da ke shafi na 25]
Baftismarka ta nuna cewa ka zaɓi hanyar rayuwa mafi kyau
[Hotuna da ke shafi na 26]
Ka sami kāriya a cikin “mabuyan”?