Tambayoyi Daga Masu Karatu
A wane yanayi ne za a yi tunanin sake yin baftisma?
A wasu yanayi, wanda ya yi baftisma zai yi tunanin tabbacin baftismarsa kuma zai iya yin tunanin sake yin baftisma. Alal misali, wataƙila a lokacin baftisma, yana zama a yanayi ko kuma yana yin wani abu a ɓoye da zai iya sa a yi masa yankan zumunci idan ya riga ya yi baftisma. Zai iya keɓe kansa ga Allah a irin wannan yanayin kuwa? Keɓe kai da mutumin ya yi zai kasance tabbatacce ne kawai ga Jehobah idan ya riga ya daina wannan halin da ya saɓa wa nassi. Saboda haka, mutumin da ya yi baftisma da irin wannan zunubi mai tsanani yana iya yin tunanin sosai game da sake yin baftisma.
Mutumin da ba ya yin zunubi a lokacin baftismarsa amma ya yi wani abu bayan baftismarsa da ke bukatan a kafa kwamiti na shari’a kuma fa? A ce ya yi da’awar cewa bai fahimci abin da yake yi sosai a lokacin da ya yi baftisma kuma ya ce baftismarsa ba tabbataciya ba ce. Sa’ad da suka sadu da wanda ya yi laifi, bai kamata dattawa su nuna cewa baftismarsa ba tabbatacciya ba ce kuma su tambaye shi ko yana jin cewa keɓe kansa da baftismarsa tabbatattu ne. Balle ma, ai ya ji jawabi na Nassi game da muhimmancin baftisma. Ya amsa tambayoyin da aka yi game da keɓe kai da baftisma da babbar murya. Sa’annan ya canja tufafinsa kuma aka nitsar da shi cikin ruwa. Saboda haka, ya dace a gaskata cewa ya fahimci muhimmancin abin da yake yi. Saboda haka, dattawa za su bi da shi a matsayin mutumin da ya yi baftisma.
Idan mutumin ya ta da batun tabbacin baftismarsa, dattawa suna iya jawo hankalinsa ga Hasumiyar Tsaro na 1 ga Maris, 1960, shafuffuka na 159 da 160, da kuma 15 ga Fabrairu, 1964, shafuffuka na 123 zuwa 126, inda aka tattauna batun sake baftisma dalla-dalla. Sake baftisma a wasu yanayi (kamar rashin cikakken fahimi na Littafi Mai Tsarki sa’ad da aka yi wa mutum baftisma) batu ne na kai.
Waɗanne abubuwa ne ya kamata Kiristoci su yi la’akari da su sa’ad da suke son su zauna a gida ɗaya tare da wasu?
Kowa yana bukatan gidan da zai zauna. Amma, a yau mutane da yawa ba su da gidan kansu. Yanayin tattalin arziki na mutum, rashin lafiya, ko kuma wasu abubuwa suna iya sa ya zauna tare da wasu dangogi. A wasu ɓangarorin duniya, dangogi da yawa suna iya zama a ɗaki ɗaya kuma hakan zai sa mutum ba zai iya samu lokacin da zai kaɗaita ba.
Ba hakkin ƙungiyar Jehobah ba ce ta tsara dokoki masu yawa game da gidan zama da ya dace ga dukan ikilisiyoyin da ke dukan duniya ba. An ƙarfafa Kiristoci su yi tunani bisa ƙa’idodin Nassi domin su san ko Allah ya amince da yanayin gidan zamansu ko bai amince da shi ba. Menene wasu cikin waɗannan ƙa’idodin?
Za mu yi la’akari musamman yadda zama tare da wasu mutane zai shafe mu da kuma ruhaniyarmu. Waɗanne irin mutane ne su? Suna bauta wa Jehobah ne? Suna yin rayuwar da ta jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki ne? Manzo Bulus ya rubuta: “Kada ku yaudaru: zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.”—1 Kor. 15:33.
Nassosi ya bayyana cewa Jehobah ya hana fasikanci da zina. (Ibran. 13:4) Bai dace ba mutane biyu da ba su auri juna ba su kwana a ɗaki ɗaya domin Allah bai amince da hakan ba. Kirista ba zai so ya zauna a inda aka amince da lalata ba.
Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki ya aririci dukan waɗanda suke son su samu amincewar Allah su “guje wa fasikanci.” (1 Kor. 6:18) Saboda haka, zai zama abin hikima Kiristoci su guji tsarin zaman gida da mutane da zai sa a gwada su su yi lalata. Alal misali, ka yi la’akari da yanayin da Kiristoci da yawa suke kwanciya a gida ɗaya. Shin irin wannan shirin zai kawo yanayi da zai sa ka cikin jaraba? Idan mutane biyu da ba su auri juna ba babu zato suka samu kansu su kaɗai domin mutanen da ya kamata su kasance a gidan ba sa nan na ɗan lokaci kuma fa? Hakazalika, zai kasance da lahani marasa aure da suke son juna su zauna a gida ɗaya. Abin hikima ne a guji irin wannan yanayin. Hakanan ma, ya kamata mutane biyu da ba su yi aure ba su guji zama su kaɗai a gida inda masu wa’azi a ƙasashen waje suke zama.
Ba zai dace ba waɗanda suka kashe aure su ci gaba da zama tare a gida ɗaya. Da yake sun saba yin jima’i da juna hakan zai kai su ga yin lalata.—Mis. 22:3.
Wani abu da ya kamata a yi la’akari da shi da yake da muhimmanci shi ne yadda mutanen unguwa za su ɗauki zaɓin da muka yi. Abin damuwa ne idan zama gida tare da wasu da Kirista yake gani babu wata matsala yana sa mutane da ke zama a unguwa su riƙa baƙar magana. Ba ma son halinmu ya sa a zargi sunan Jehobah. Bulus ya ce: “Kada ku kafa sanadin tuntuɓe, ko ga Yahudawa, ko ga Helenawa, ko ga ikilisiya ta Allah: kamar yadda ni da kaina a cikin al’amura duka ina aikin yarda ga dukan mutane, ba biɗa wa kaina amfani na ke yi ba, amma abin da zai amfana masu-yawa, su tsira.”—1 Kor. 10:32, 33.
Samun gida da kuma mutanen da ya dace a zauna da su zai iya zama ƙalubale sosai ga waɗanda suke so su ɗaukaka mizanan Jehobah na adalci. Amma, dole ne Kiristoci su ci gaba da “gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji.” Suna bukatan su tabbata cewa babu wani abu marar kyau da ke faruwa a gidansu. (Afis. 5:5, 10) Hakan yana bukatan Kiristoci su yi addu’a don samun ja-gorar Allah kuma su yi iyakar ƙoƙarinsu su kāre zaman lafiya na zahiri da na ɗabi’a na juna da kuma suna mai kyau na Jehobah.