Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 2/15 p. 29
  • “Hakkin Yaro ga Ci Gabansa na Ruhaniya”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Hakkin Yaro ga Ci Gabansa na Ruhaniya”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Gina Iyali Mai Ƙarfi A Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Taimako Don Fahimtar Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Abin da Yara Suke Bukata Daga Wurin Iyaye
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Iyaye Ku Kāre Kyautarku Mai Tamani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 2/15 p. 29

“Hakkin Yaro ga Ci Gabansa na Ruhaniya”

A RANAR 9 ga Disamba, na shekara ta 2008, Makarantar Kāre ’Yancin Yara na Ƙasar Sweden ta yi taron ƙara wa juna sani na musamman mai jigo “Hakkin Yaro ga Ci Gabansa na Ruhaniya.” Masu jawabi da ke wakiltar Cocin Sweden, sauran addinai na Kiristendom, Musulunci, da ƙungiyar da ta gaskata cewa mutane za su iya yin rayuwa ba tare da addini ba kuma su yi farin ciki, duk sun gabatar da ra’ayoyi da yawa.

Wani limami cikin masu jawaban ya ce: “Da wuya mutum ya kwatanta irin muhimmancin yadda labaran da ke cikin Littafi Mai Tsarki suke shafan ruhaniyar yara.” Yaya ayoyi na Nassi suke biyan bukatu na ruhaniyar yara?

“Ayoyi da kuma labaran suna ba yara abin yin tunani da bimbini a kai,” in ji limamin. Ya lissafa “labarin Adamu da Hauwa’u, na Kayinu da Habila, na Dauda da Goliyat, na haihuwar Yesu, na Zakka mai karɓan haraji, almarar ɗa almubazzari, na Basamariye mai halin maƙwabta.” An ambata waɗannan a matsayin “wasu cikin labarai masu kyau da za su ja-goranci tunanin [yaro] game da batutuwa masu muhimmanci a rayuwar ɗan Adam, kamar su cin amana, yin gafara, kafara, ƙiyayya, yanayin ban kunya, sulhuntawa, ƙauna na rashin son kai ga ’yan’uwa.” Ya daɗa: “Waɗannan ayoyin sun nuna yadda hakan zai iya shafan rayuwar mutum, ayyukansa, kuma su zama labarai masu amfani.”

Hakika, yana da kyau a ƙarfafa mutane su karanta Littafi Mai Tsarki. Amma, yara za su iya yin “bimbini na kansu” kuwa game da abin da suka karanta daga Nassosi kuma su kai ga kammalawar da ta dace?

Manya ma suna bukatan a bayyana musu ayoyi na Nassi. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da wani mutumin da ya kasa samun ruhaniya na gaskiya ta hanyar yin “bimbini na kansa.” Mutumin nan ma’aikacin Habasha ne. Yana karanta annabcin Ishaya amma bai fahimci abin da yake karantawa ba. Tun da yake yana son ya fahimci saƙon annabin, ya amince da bayanin da almajiri Filibus ya yi masa. (A. M. 8:26-40) Ba Bahabashen kawai ba ne yake bukatan bayani. Dukanmu, musamman yara, muna bukatan a bayyana mana ayoyi na Nassi.

Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu: “Wauta tana nan ƙunshe a zuciyar yaro.” (Mis. 22:15) Yara suna bukatan ja-gora, kuma iyayensu suna da hakkin koya musu ɗabi’a da kuma ruhaniya, bisa Littafi Mai Tsarki da kuma game da abin da ake koyarwa a cikin ikilisiyar Kirista. Yara suna da hakkin samun irin wannan koyarwa. Tun suna ƙanana, suna bukatan taimako don su kafa tushe da ke bisa Littafi Mai Tsarki don su samu ci gaba na ruhaniya kuma su zama “isassun mutane . . . waɗanda suna da hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.”—Ibran. 5:14.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba