Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 1/15 pp. 21-23
  • Ka Yi Amfani da Kowace Rana a Rayuwarka don Girmama Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Amfani da Kowace Rana a Rayuwarka don Girmama Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Cika Alkawarinmu
  • Ka Yi La’akari da Wasu
  • Tsarkakkar Hidima “Dare da Rana”
  • ’Yan’uwa Maza, Ku Yi Shuka Ga Ruhu Kuma Ku Yi Burin Samun Hakki!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ka Rika Yin La’akari da Mutane Kamar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Ka Ɗauki Hakkinka A Cikin Ikilisiya Da Tamani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Kiristoci Suna Samun Farin Ciki A Bayarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 1/15 pp. 21-23

Ka Yi Amfani da Kowace Rana a Rayuwarka don Girmama Allah

MAI zabura Dauda ya yi addu’a ga Jehobah, “ka jishe ni rahamarka da safe . . . Ka sa in san tafarkin da zan bi.” (Zab. 143:8) Sa’ad da ka tashi da safe kuma ka gode wa Jehobah don sabuwar rana a rayuwarka, kamar Dauda kana roƙon Jehobah ya yi maka ja-gora sa’ad da kake tsai da shawarwari da kuma ɗaukan tafarki da ya fi kyau? Babu shakka kana hakan.

A matsayin bayin Jehobah da suka keɓe kansu, ‘ko [muna] ci, ko muna sha, ko kuwa iyakar abin da muke yi,’ muna ƙoƙari mu “yi duka domin a girmama Allah.” (1 Kor. 10:31) Mun fahimci cewa yadda muke yin rayuwarmu ta yau da kullum zai ɗaukaka Jehobah ko kuma ba zai ɗaukaka shi ba. Mun kuma tuna cewa Kalmar Allah ta ce Shaiɗan yana zargin ’yan’uwan Kristi, da kuma dukan bayin Allah a duniya, “dare da rana.” (R. Yoh. 12:10) Saboda haka, mun ƙuduri aniya mu ba da amsa ga zargin Shaiɗan kuma mu faranta zuciyar Jehobah ta wajen yin tsarkakar hidima ga Ubanmu na samaniya “dare da rana.”—R. Yoh. 7:15; Mis. 27:11.

Bari mu ɗan bincika hanyoyi biyu masu muhimmanci da za mu iya yin amfani da kowace rana a rayuwarmu don girmama Allah. Hanya ta farko ta ƙunshi kafa abubuwa da suka fi muhimmanci, kuma na biyu yin la’akari da mutane.

Cika Alkawarinmu

Ta wajen keɓe kanmu ga Jehobah, mun nuna cewa muna son mu bauta masa da dukan zuciyarmu. Mun kuma yi wa Jehobah alkawari cewa za mu bi tafarkinsa “kowace rana,” hakika, har abada. (Zab. 61:5, 8) To, ta yaya za mu yi rayuwa da ta jitu da wannan alkawarin? Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarmu a kowace rana?

Kalmar Allah ta bayyana dalla-dalla hakkin da Jehobah yake son mu cika. (K. Sha 10:12, 13) An tsara da yawa a cikin akwati mai jigo “Hakkokin da Allah Ya ba Da,” a shafi na 22. Allah ne ya ba mu waɗannan ayyuka saboda haka suna da muhimmanci. Ta yaya za mu san wanda ya fi muhimmanci sa’ad da ɗaya ko kuma fiye da hakan suke bukatan mu mai da musu hankali a lokaci ɗaya?

Tsarkakkar hidimarmu ta fi muhimmanci, hakan ya ƙunshi nazarin Littafi Mai Tsarki, addu’a, taron Kirista, da hidima. (Mat. 6:33; Yoh. 4:34; 1 Bit. 2:9) Duk da haka, ba za mu wuni muna ayyuka na ruhaniya ba. Muna bukatar mu haɗa aiki, makaranta da aikace-aikacen gida da yawa a cikin tsarinmu. Duk da haka, muna iyakar ƙoƙarinmu mu shirya aiki da wasu ayyuka yadda ba za su hana mu tsarkakkar hidima ba, kamar halartar taron Kirista. Alal misali, sa’ad da muke shirin zuwa hutu, mu tabbata cewa za mu halarci ziyarar mai kula da da’ira, ranar taro na musamman, taron da’ira, ko kuma taron gunduma. A wasu lokatai, muna iya haɗa wasu cikin hakkinmu. Alal misali, muna iya sa share Majami’ar Mulki ya zama aikin da kowa a cikin iyali zai sa hannu ko kuma mu yi amfani da lokacin cin abinci a wajen aiki ko kuma a makaranta don mu yi wa’azi ga abokan aikinmu ko kuma abokan makaranta. Hakika, duk lokacin da muke bukatar mu yi zaɓi a rayuwarmu, kamar neman aiki, zaɓan makaranta, ko kuma zaɓan abokai, ya kamata mu tsai da shawarwari bisa abin da ya fi muhimmanci a rayuwa, wato, bauta wa Jehobah, Ubanmu mai ƙauna.—M. Wa. 12:13.

Ka Yi La’akari da Wasu

Jehobah yana son mu nuna muna damuwa da wasu kuma mu yi musu nagarta. A wani ɓangare kuma, Shaiɗan yana ɗaukaka son kai. Duniyarsa tana cike da mutane “masu-son kansu” da “mafiya son annishuwa” da kuma waɗanda suke “shuka ga jiki.” (2 Tim. 3:1-5; Gal. 6:8) Mutane da yawa ba sa tunani yadda ayyukansu ke shafan wasu. Ana ganin “ayyukan jiki” a ko’ina.—Gal. 5:19-21.

Halin waɗanda ruhu mai tsarki na Jehobah yake musu ja-gora dabam ne, suna nuna ƙauna, alheri, nagarta a sha’aninsu da mutane! (Gal. 5:22) Kalmar Allah ta gaya mana mu mai da hankali ga bukatun wasu fiye da namu. Saboda haka, muna yin abubuwa da suke nuna cewa muna damuwa da juna, ko da yake muna mai da hankali kada mu yi shishigi ga abubuwa da ba su shafe mu ba. (1 Kor. 10:24, 33; Filib. 2:3, 4; 1 Bit. 4:15) Muna yin la’akari musamman da ’yan’uwa masu bi. Duk da haka, muna ƙoƙari mu taimaka wa marasa bi. (Gal. 6:10) Za ka iya neman zarafi a yau ka nuna alheri ga wani da ka sadu da shi.—Ka duba akwati “Ka Yi La’akari da Su,” a shafi na 23.

Ba a wani lokaci ko kuma yanayi na musamman kawai za mu yi la’akari da mutane ba. (Gal. 6:2; Afis. 5:2; 1 Tas. 4:9, 10) Maimakon haka, a kowace rana muna ƙoƙari mu san yanayin wasu kuma mu kasance a shirye mu taimaka idan bukata ta kama, ko a lokacin da yin hakan yake da wuya. Ya kamata mu zama masu karimci da duk abin da muke da shi, yana iya zama lokacinmu, dukiyarmu, iyawarmu, da kuma basirarmu. Jehobah ya tabbatar mana cewa idan mun kasance da karimci ga wasu, zai nuna mana karimci.—Mis. 11:25; Luk 6:38.

Tsarkakkar Hidima “Dare da Rana”

Zai yiwu da gaske a yi wa Jehobah hidima “dare da rana” kuwa? Hakika, ta wajen kasancewa da ƙwazo a dukan fannonin bautarmu da kuma yin hakan a kai a kai. (A. M. 20:31) Za mu iya cika rayuwarmu da tsarkakkar hidima ta wajen karatu da kuma yin bimbini game da Kalmar Allah a kowace rana, ta yin addu’a ba fasawa, ta wajen yin ƙoƙari mu halarci dukan taro, da kuma yin amfani da kowane zarafi don ba da shaida.—Zab. 1:2; Luk 2:37; A. M. 4:20; 1 Tas. 3:10; 5:17.

Muna yin irin wannan tsarkakkiyar hidima ga Jehobah kuwa? Idan haka ne, za mu nuna a dukan fannonin rayuwarmu na kullum cewa muna son mu faranta masa rai da kuma ba da amsa ga zargin Shaiɗan. Muna ƙoƙari mu girmama Jehobah a dukan abubuwa da muke yi da kuma duk yanayi da muka samu kanmu. Muna barin ƙa’idodinsa su yi wa furcinmu da halinmu ja-gora da kuma shawarwari da muke tsai da wa. Muna nuna godiya don kulawarsa ta ƙauna da kuma goyon baya ta wajen kasancewa da tabbaci a gare shi da kuma yin amfani da ƙarfinmu a hidimarsa. Kuma muna yin na’am da gargaɗinsa da horo, sa’ad da domin ajizancinmu, muka kasa bin mizanansa.—Zab. 32:5; 119:97; Mis. 3:25, 26; Kol. 3:17; Ibran. 6:11, 12.

Bari mu ci gaba da yin rayuwa kowace rana don girmama Allah. Ta yin hakan, za mu wartsake rayukanmu kuma za mu more kulawa ta ƙauna ta Ubanmu na samaniya har abada.—Mat. 11:29; R. Yoh. 7:16, 17.

[Akwati/Hotuna da ke shafi na 22]

Hakkokin da Allah Ya Ba Da

• Yin addu’a a kai a kai.—Rom. 12:12.

• Karanta da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki, muna yin amfani da shi ga kanmu.—Zab. 1:2; 1 Tim. 4:15.

• Bauta wa Jehobah a cikin ikilisiya.—Zab. 35:18; Ibran. 10:24, 25.

• Yin tanadin abin biyan bukatan iyalinmu, na ruhaniya, da kuma na motsin rai.—1 Tim. 5:8.

• Yin wa’azin bisharar Mulki da kuma almajirantarwa.—Mat. 24:14; 28:19, 20.

• Kulawa da lafiyarmu ta zahiri, ta ruhaniya, da ta motsin rai, wadda ta haɗa da shirya yin nishaɗi mai kyau.—Mar. 6:31; 2 Kor. 7:1; 1 Tim. 4:8, 16.

• Kula da hakkokin ikilisiya.—A. M. 20:28; 1 Tim. 3:1.

• Kula da gidanmu da kuma Majami’ar Mulki.—1 Kor. 10:32.

[Akwati/Hoton da ke shafi na 23]

Ka Yi La’akari da Su

• Ɗan’uwa tsoho ko kuma ’yar’uwa tsohuwa.—Lev. 19:32.

• Wani da yake ciwo na zahiri ko na motsin rai.—Mis. 14:21.

• Wani da yake cikin ikilisiya da yake da bukata ta gaggawa na wani abin da za ka iya tanadinsa.—Rom. 12:13.

• Wanda yake cikin iyalinka.—1 Tim. 5:4, 8.

• Wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa mai bi da abokiyar aurensa ko nata ya mutu.—1 Tim. 5:9.

• Dattijo mai aiki tuƙuru a cikin ikilisiyarku.—1 Tas. 5:12, 13; 1 Tim. 5:17.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba