Ku Taimaka wa Yaranku Su Bi da Ƙalubalensu Masu Yawa
MATASANMU suna fuskantar matsi sosai. Ruhun muguwar duniya na Shaiɗan yana rinjayarsu, kuma dole ne su yi fama da “sha’awoyin ƙuruciya.” (2 Tim. 2:22; 1 Yoh. 5:19) Bugu da ƙari, domin suna ƙoƙari su ‘tuna da Mahaliccinsu,’ suna jimre wa ba’a har ma matsi daga waɗanda suke hamayya da imaninsu. (M. Wa. 12:1) Sa’ad da ya tuna lokacin da yake girma, wani ɗan’uwa mai suna Vincent ya ce: “A koyaushe wani yakan matsa mini, zalunta ni, ko kuma ya nemi yin faɗa da ni domin ni Mashaidi ne. Sau da yawa matsin yakan yi tsanani sosai har ba na son na je makaranta.”a
Ƙari ga matsi daga wasu mutane, yaranmu maza da mata suna iya yin fama da sha’awarsu na son su zama kamar tsaransu. “Ba shi da sauƙi a ga ka yi dabam,” in ji Cathleen, wata ’yar’uwa mai shekara goma sha shida. Wani matashi mai suna Alan ya ce, “Sau da yawa ana gayyata na na fita yawon shaƙatawa da abokan makarantarmu a ƙarshen mako, kuma ƙwarai ina son na je.” Bugu da ƙari, sha’awar matasa na yin wasanni a makaranta, wanda zai iya kai ga samun mugayen tarayya, yana da ƙarfi sosai. “Ina son wasanni,” in ji wata ’yar’uwa matashiya mai suna Tanya. “Masu koyar da wasanni a makaranta a koyaushe suna ƙoƙari su sa na yi wasa a ƙungiya. Yana da wuya na ƙi yin hakan.”
Ta yaya za ku taimaka wa yaranku su bi da ƙalubale masu yawa da suke fuskanta? Jehobah ya ba iyaye umurni su yi ja-gorar yaransu. (Mis. 22:6; Afis. 6:4) Makasudin iyaye masu jin tsoron Allah shi ne su sa yaransu su yi sha’awar yi wa Jehobah biyayya da dukan zuciyarsu. (Mis. 6:20-23) Ta hakan, yara za su motsa su ƙi matsi na duniya har sa’ad da iyayensu ba sa tare da su.
Yana da wuya iyaye su samu abin biyan bukatun rayuwa, kuma su kula da iyalinsu da ayyukan ikilisiya a lokaci ɗaya. Wasu suna yin hakan a matsayin iyaye gwauraye ko kuma sa’ad da suke fuskantar hamayya daga aboki ko abokiyar aure wanda ba mai-bi ba. Duk da haka, Jehobah yana bukatar iyaye su keɓe lokaci don su koyar da kuma taimaka wa yaransu. Saboda haka, menene za ku iya yi don ku taimaka wa yaranku su kāre kansu daga matsi na tsara, gwaji, da tsanantawa da suke fuskanta a kowace rana?
Dangantaka da Jehobah
Na farko, yaranmu suna bukatar su san Jehobah a matsayin wanda yake wanzuwa. Suna bukatar taimako don su ga “wanda ba shi ganuwa.” (Ibran. 11:27) Vincent, wanda aka ambata ɗazu, ya tuna yadda iyayensa suka taimaka masa ya ƙulla dangantaka da Jehobah. Ya ce: “Sun koya mini muhimmancin yin addu’a. Na tuna cewa tun ina ƙarami ina yin addu’a ga Jehobah kowane dare kafin na yi barci. Jehobah ya kasance da gaske a gare ni.” Kuna addu’a da yaranku? Me ya sa ba za ku saurari abin da suke gaya wa Jehobah a cikin addu’o’insu ba? Suna maimaita kalamai da sun haddace ne? Ko kuwa suna furta yadda suke ji game da Jehobah a cikin addu’o’insu? Ta wajen saurarar addu’o’insu, za ku fahimci ko suna samun ci gaba na ruhaniya.
Karatun Kalmar Allah a kai a kai wata hanya ce mai muhimmanci da matasa za su kusaci Jehobah. Cathleen, da aka ambata ɗazu ta ce: “Karanta Littafi Mai Tsarki sa’ad da nake matashiya ya taimake ni. Ya sa na kasance da tabbaci cewa ko idan mutane suna matsa mini, Jehobah yana goyon baya na.” Shin yaranku suna da nasu tsarin karatun Littafi Mai Tsarki?—Zab. 1:1-3; 77:12.
Hakika, yara sun bambanta a yadda suke aikatawa ga ja-gorar iyayensu. Kuma ci gabansu na ruhaniya zai iya dangana ga shekarunsu. Duk da haka, idan babu ja-gora, zai yi wa matasa wuya su san Jehobah a matsayin mutum na gaske. Ya kamata iyaye su koya wa yaransu kalaman Allah don yaran su ji Jehobah yana magana a duk inda suke, a alamance. (K. Sha 6:6-9) Ya kamata yaranku su gaskata cewa Jehobah yana kula da su.
Yadda Za a Sa Sadarwa ta Kasance da Ma’ana
Sadarwa wata hanya ce mai muhimmanci na taimaka wa yaranku. Hakika, sadarwa da kyau ba yin magana kawai da yaranku ba. Ya ƙunshi yin tambayoyi da kuma saurara wa amsoshinsu da haƙuri ko da amsoshin sun yi dabam da abin da za ku so ku ji. Anne, wata uwa mai yara maza biyu, ta ce: “Nakan yi tambayoyi har sai na ga cewa na fahimci abin da suke nufi da kuma abin da suke fama da shi a rayuwarsu.” Yaranku suna jin cewa kuna sauraron su sa’ad da suke magana kuwa? Tanya, wadda aka ambata a baya ta ce: “Iyayena sun saurare ni da kyau kuma sun tuna abin da muka tattauna. Sun san sunayen abokan aji na. Sukan yi tambaya game da su da kuma wasu yanayi da muka tattauna a dā.” Saurarawa da kuma tunawa suna da muhimmanci ga sadawa mai kyau.
Iyalai da yawa sun gane cewa lokacin cin abinci yana ba da zarafi mai kyau na tattaunawa da kyau. “Cin abinci tare yana da muhimmanci a iyalinmu,” in ji Vincent. “Ana bukatar mu kasance a wurin cin abinci tare da iyalin duk lokacin da ya yiwu. Ba a yarda a kalli talabijin, a saurari rediyo, ko kuma a yi karatu a lokacin cin abinci ba. Tun da yake yawancin lokaci taɗin ba mai muhimmanci ba ne, yana ba da lokacin lumana kowace rana da ke taimaka mini na bi da ɗimauci da matsi da nake fuskanta a makaranta.” Ya daɗa: “Saba yin magana da iyayena a lokacin cin abinci ya kuma taimaka mini na saki jiki sa’ad da nake yin magana da su a lokacin da nake bukatan taimako a batutuwa masu tsanani.”
Ku tambayi kanku, ‘Sau nawa a kowane mako ne muke cin abinci tare a matsayin iyali?’ Shin yin gyara a wannan wurin zai ba ku zarafin sadarwa da kyau da yaranku?
Abin da Ya Sa Yin Gwaji Yake da Amfani Sosai
Bautar Iyali ta Yamma a kowane mako yana kuma taimaka wa duka a cikin iyali su saki jiki sa’ad da suke magana da juna kuma yana taimaka wa matasa su bi da takamammun matsaloli. Alan, da aka ambata ɗazu, ya ce: “Iyayena sun yi amfani da lokacin nazari na iyali don su san abin da yake cikin zuciyarmu. Sun tattauna batutuwa da suka dace da abin da muke fuskanta.” Mahaifiyar Alan ta ce: “Mukan yi amfani da wasu lokacin nazari don yin gwaji. Wannan gwaji ya taimaki yaranmu su koya yadda za su kāre bangaskiyarsu kuma su nuna cewa abin da suka gaskata gaskiya ne. Hakan ya ba su gaba gaɗin da suke bukata don su bi da ƙalubale da suke fuskanta.”
Hakika, sa’ad da suke fuskantar matsi na tsara, sau da yawa yara suna bukatan su yi wasu abubuwa ba kawai faɗan a’a kuma su yi tafiyarsu ba. Suna bukatan su amsa tambaya kamar me ya sa. Suna bukatan su kasance da gaba gaɗi game da abin da za su yi sa’ad da aka yi musu ba’a domin imaninsu. Idan ba za su iya goyon bayan imaninsu ba, zai yi musu wuya su kasance da gaba gaɗi don bauta ta gaskiya. Yin gwaji zai iya taimaka musu su kasance da gaba gaɗi.
Akwati da ke shafi na 18 ya tsara wasu yanayi da za a iya gwada a lokacin Bauta ta Iyalinku da Yamma. Ka sa waɗannan gwaji su kasance na gaske ta wajen yin musun amsoshin da yaranka suka ba da. Tare da irin wannan gwaji, ka yi la’akari da wasu darussa masu kyau da misalan Littafi Mai Tsarki suka koya mana. Babu shakka, irin wannan koyarwa a gida zai shirya yaranku su bi da ƙalubale da suke fuskanta a makaranta da kuma wani waje.
Gida, Wurin Kwanciyar Hankali Ne Kuwa?
Shin gidanku wuri ne da yaranku suke ɗokin komawa idan an tashi daga makaranta kowace rana? Idan wurin kwanciyar hankali ne zai taimaka wa yaranku su bi da ƙalubale da suke fuskanta kowace rana. Wata ’yar’uwa da yanzu tana iyalin Bethel ta ce: “Sa’ad da nake girma, wani abin da ya taimaka mini sosai shi ne cewa gidanmu wurin kwanciyar hankali ne. Ko yaya yanayin ya yi muni a makaranta, na san cewa idan na dawo gida, kome zai yi daidai.” Yaya yanayin gidanku yake? Wuri ne inda ake “hasala, tsatsaguwa, [da] rabuwa,” ko kuwa an san gidanku da “ƙauna ne, farinciki, [da] salama”? (Gal. 5:19-23) Idan sau da yawa babu salama, kuna ƙoƙari ku san canje-canje da kuke bukatan ku yi domin ku sa gidanku ya zama wurin kwanciyar rai don yaranku?
Wata hanya da za ku taimaka wa yaranku su bi da ƙalubale ita ce ta wurin yi musu tanadin abokai masu ƙarfafawa. Alal misali, za ku iya haɗa wasu ’yan’uwa masu ruhaniya daga ikilisiya cikin ayyukan nishaɗi na iyalinku? Ko kuma za ku iya shirya cin abinci a gidanku tare da mai kula da da’ira ko wasu da suke hidima na cikakken lokaci? Kun san wani mai wa’azi a ƙasar waje ko kuma wanda yake hidima a Bethel da yaranku za su ƙulla abuta da, ko ta wurin rubuta wasiƙu, aika saƙo ta kwamfuta, ko kuma yin waya a wani lokaci? Irin wannan abuta zai taimaka wa yaranku su bi miƙaƙƙun hanyoyi domin sawayensu kuma su kafa makasudai na ruhaniya. Ku yi tunani yadda manzo Bulus ya kasance da tasiri mai kyau ga matashi, Timotawus. (2 Tim. 1:13; 3:10) Tarayya na kud da kud da Bulus ya taimaka wa Timotawus ya mai da hankali ga makasudai na ruhaniya.—1 Kor. 4:17.
Ku Yabi Yaranku
Jehobah yana farin cikin ganin matasa sun manne wa abin da ke daidai duk da matsi daga duniyar Shaiɗan. (Zab. 147:11; Mis. 27:11) Babu shakka, ku ma kuna farin cikin ganin matasa suna zaɓan tafarki mai kyau. (Mis. 10:1) Ku sa yaranku su san yadda kuke ji game da su, kuma ku yaba musu cikin ƙauna a koyaushe. Jehobah ya kafa misali mai kyau ga iyaye. A lokacin baftismar Yesu, Jehobah ya ce: “Kai ne Ɗana ƙaunatace, raina yana jin daɗin ka sosai.” (Mar. 1:11) Babu shakka, tabbacin Ubansa ya ƙarfafa Yesu ya bi da ƙalubale masu yawa da zai fuskanta! Hakazalika, ku sa yaranku su san cewa kuna ƙaunarsu, kuma ku amince da abin da suke cim ma wa.
A bayyane yake cewa ba za ku iya tsare yaranku gabaki ɗaya daga matsi, tsanantawa, da kuma ba’a ba. Duk da haka, za ku iya yin abubuwa da yawa don ku taimaka musu. A waɗanne hanyoyi? Ku taimaka musu su ƙulla dangantaka da Jehobah. Ku ƙafa yanayi da zai iya sa tattauna ya kasance mai amfani. Ku sa Bautar Iyali ta Yamma ta zama mai amfani, kuma ku sa gidanku ya zama wajen kwanciyar hankali. Babu shakka, yin hakan zai taimaka wa yaranku su bi da ƙalubalensu masu yawa.
[Hasiya]
a An canja wasu sunaye a wannan talifin.
[Akwati/Hoton da ke shafi na 18]
GWAJI ZAI TAIMAKA
Ga wasu misalai na yanayi da matasanmu suke fuskanta. Ka gwada wasu cikin waɗannan yanayi a lokacin Bauta ta Iyali na yamma.
▸ Mai koyar da wasa ya gaya wa ’yarka ta shiga ƙungiya na ’yan wasa na makaranta.
▸ An ba ɗanka sigari sa’ad da yake dawowa daga makaranta.
▸ Wasu yara sun yi wa ɗanka barazana cewa za su yi masa dūka idan sun sake ganin shi yana wa’azi.
▸ Lokacin da ’yarka take hidimar ƙofa ƙofa, sai ta sadu abokiyar makarantarta.
▸ A gaban aji, an tambayi ’yarka dalilin da ya sa ba ta sara wa tuta.
▸ Wani yaro a koyaushe yana yi wa ɗanka ba’a domin shi Mashaidi ne.
[Hoton da ke shafi na 17]
Shin yaranku suna da nasu tsarin karatun Litafi Mai Tsarki?
[Hoton da ke shafi na 19]
Kuna haɗa ’yan’uwa masu ruhaniya a ayyukanku na nishaɗi kuwa?