Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 1/1 pp. 4-5
  • Allah Yana Kula da Gaske Yadda Muka San da Hakan

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Allah Yana Kula da Gaske Yadda Muka San da Hakan
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Halitta ta Tabbatar da Ƙaunar Allah
  • Littafi Mai Tsarki Ya Tabbatar Mana da Ƙaunar Allah
  • Wane Ne Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Yadda Za a Gane Bauta Ta Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • “Ya Fara Kaunace Mu”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 1/1 pp. 4-5

Allah Yana Kula da Gaske Yadda Muka San da Hakan

TAMBAYAR nan tsohuwa ce amma tana da muhimmanci, tambaya ce da mutane suka neman amsar ta a shekaru da yawa: Idan Allah yana ƙaunarmu, menene ya sa akwai wahaloli da yawa? Babu shakka ka yarda cewa idan kana ƙaunar wani, ba za ka so ya sha wahala ba, kuma idan shi ko ita suna cikin matsala, za ka yi ƙoƙarin taimakawa. Da haka, mutane da yawa suna tunani cewa tun da akwai wahala da yawa a duniya, Allah ba ya kula da mu. Yana da muhimmanci, mu fara yin la’akari da tabbacin cewa Allah yana ƙaunarmu, wato, Allah yana kula da gaske.

Halitta ta Tabbatar da Ƙaunar Allah

Jehobah Allah shi ne ‘wanda ya yi sama da ƙasa da teku, da abin da ke cikinsu duka.’ (Ayyukan Manzanni 4:24) Yayin da muka yi tunani game da abin da Jehobah ya halitta, babu shakka za mu kammala cewa yana kula da mu. Alal misali, ka yi tunani game da abubuwan da suke sa ka farin ciki da annashuwa. Kana sha’awar abinci mai kyau? Jehobah zai iya halittan irin abinci guda kawai don mu dinga ci. Maimakon hakan, ya halicci abinci iri-iri masu ɗanɗano. Hakazalika, Jehobah ya kewaye duniya da itatuwa iri-iri, furanni, da kuma mahalli mai kyau da za su sa rayuwa ta yi daɗi.

Ka yi la’akari kuma da yadda aka halicce mu. Ingancinmu na yin dariya, jin daɗin waƙa, da kuma ingancinmu na son abu mai kyau ba don kawai ta sa mu rayu ba, amma duka baiwa ce daga Allah da suke kyautata rayuwarmu. Ka kuma yi tunani game da dangantakarmu da wasu. Wanene baya more dangantaka mai kyau da abokai ko kuma runguma daga wanda muke ƙauna sosai? I fa, ingancin yin ƙauna baiwa ce daga Allah wanda yake da ƙauna! Tun da Allah ya halicci ’yan Adam da ingancin yin ƙauna, wannan halin yana cikin mutumtakar Allah.

Littafi Mai Tsarki Ya Tabbatar Mana da Ƙaunar Allah

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah ƙauna ne. (1 Yohanna 4:8) Ƙaunarsa ba ta bayyana a halittarsa ba kawai amma ta bayyana a Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya lissafa abubuwan da ke ba da lafiyar jiki, ya ce mu yi kima a dukan abu, kuma ya yi gargaɗi game da shaye-shaye da haɗama.—1 Korintiyawa 6:9, 10.

Littafi Mai Tsarki ya kuma ba da shawara mai kyau game da dangantakar ’yan Adam, ya aririce mu mu ƙaunaci juna kuma mu bi da juna cikin girmamawa, mutunci, da kuma kirki. (Matta 7:12) Ya haramta ayyuka da kuma halayen da ke jawo wahala, kamar su, kwaɗayi, gulma, hassada, zina, da kisa. Idan kowa ya yi ƙoƙarin yin rayuwa cikin jituwa da kyakkyawar shawarar da ke cikin Nassosi, babu shakka wahalar da ke dukan duniya za ta ragu.

Alamar ƙaunar Jehobah mafi girma, ita ce ba da Ɗansa, Yesu, don ya fanshi ’yan Adam. Yohanna 3:16 ta ce: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” Da haka Jehobah ya riga ya yi shirin kawo ƙarshen mutuwa da kuma kowace irin wahala.—1 Yohanna 3:8.

Babu shakka, akwai tabbaci da yawa da suka nuna cewa Jehobah yana ƙaunarmu. Hakan ya nuna cewa, Allah ba ya so ya ga muna shan wahala. Zai ɗauki mataki don ya kawo ƙarshen wahala. Ba ma bukatan mu yi shakkar wannan zancen, domin Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana daidai yadda Allah zai kawar da wahala.

[Hoton da ke shafi na 4]

Ingancin yin ƙauna baiwa ce daga Allah da ke ƙauna

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba