“Har Yaushe . . . Zan Yi Kira?”
“Ina dai son azabar ta ƙare!” Jayne ta furta hakan da kuka. Tana da ciwon daji, kuma yana yaɗuwa a cikin jikinta. Iyalinta da abokanta sun ji kamar su samu ikon cire mata ciwon da kuma azabar! Sun yi wa Allah addu’a ya taimaka mata. Zai amsa kuwa? Ya kula kuwa?
ALLAH yana sane da yanayin ’yan Adam. Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan talikai suna nishi suna naƙuda tare da mu har yanzu.” (Romawa 8:22) Allah ya san cewa akwai miliyoyin mutane waɗanda kamar Jayne, suna cikin azaba kullum, ko na zahiri, ko na motsin rai, ko kuma na tunani. Allah yana ganin mutane miliyan ɗari takwas da suke kwana ba tare da cin abinci ba duk dare, da kuma miliyoyin waɗansu da suke shan azaba na nuna ƙarfi a gida, da kuma iyaye da yawa da suke damuwa game da gaba da kuma lafiyar yaransu. Ka taba tunani ko Allah zai ɗauki mataki kuwa? Hakika, idan muna son mu taimaka wa ƙaunatattunmu, shin Allah ma ba zai so ya taimaka wa ’yan Adam, halittunsa ba?
Idan ka yi waɗannan tambayoyin, ba ka kaɗaita ba. Fiye da shekaru dubu biyu da ɗari shida da suka shige, wani mutum amintacce, Habakkuk, ya ji kamar yadda mutane da yawa a yau suke ji, sai ya tambayi Allah: ‘Ya Ubangiji, har yaushe zan yi kira, kai kuwa ba ka yarda ka ji ba? Ina tada murya gareka saboda zafin mugunta, kai kuwa ka ƙi yin ceto. Don me ka ke nuna mini saɓo, ka sa ni in duba shiririta kuma? gama ɓarna da mugunta suna gabana; akwai husuma, jayayya kuma ta taso?’ (Habakkuk 1:2, 3) Habakkuk, annabi na Yahudawa, ya shaida mugunta da cin zali a zamaninsa. A yau, irin waɗannan ayyukan suna faruwa ne kullum kuma suna ɓata wa masu juyayi rai.
Shin Allah ya rena damuwar Habakkuk kuwa? A’a. Ya saurari tambayar da Habakkuk ya yi da dukan zuciya sai ya ƙarfafa mutumin da ke cikin wahala. Jehobah Allah ya ƙarfafa bangaskiyar Habakkuk ta yin alkawarin cewa Zai kawo ƙarshen wahalar. Saƙon Allah na bege zai iya ƙarfafa ka, kamar yadda ya ƙarfafa Jayne da iyalinta. Talifofi na gaba za su amsa waɗannan tambayoyin: Ta yaya za mu tabbata cewa Allah yana kula da mu da gaske? Menene Allah zai yi don ya kawo ƙarshen wahala, kuma yaushe zai faru?