Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 1/1 pp. 5-7
  • Matsalar Dukan Duniya, Yadda Za a Magance Ta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matsalar Dukan Duniya, Yadda Za a Magance Ta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Mulkin Allah Zai Yi
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Za Mu Amfana Idan Muka Jimre Wahala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Dukan Wahala Za Ta Ƙare Ba Da Daɗewa Ba!
    Dukan Wahala Za Ta Ƙare Ba Da Daɗewa Ba!
  • Abubuwan da Allah Zai Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 1/1 pp. 5-7

Matsalar Dukan Duniya, Yadda Za a Magance Ta

ANA GANIN wahala a ko’ina, kuma mutane da yawa sun taimaka wa waɗanda ta shafa cikin tausayi. Alal misali, likitoci, sukan yi aiki tuƙuru don su taimaka wa waɗanda ba su da lafiya ko suka ji rauni. Masu kashe gobara, ’yan sanda, masu kafa doka, da masu jinyar gaggawa sukan ƙoƙarta don kawar ko kuma hana wasu su sha wahala. Irin waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarcen suna taimaka wa mutane, amma babu wani ko kuma ƙungiyar da za ta iya dakatar da shan wahala a duniya gabaki ɗaya. Akasin haka, Allah zai iya kuma zai kawo sauƙi a dukan duniya.

Mun samu tabbaci a littafi na ƙarshe a Littafi Mai Tsarki: “[Allah] zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Ka yi la’akari da yawan mutane da wannan alkawarin zai shafa. Ya bayyana ƙudurin Allah na kawo ƙarshe ga dukan wahala. Zai yi hakan ta cire dukan yaƙe-yaƙe, yunwa, cuta, da rashin gaskiya, tare da dukan miyagu daga duniya. Babu ɗan Adam da zai iya cim ma wannan.

Abin da Mulkin Allah Zai Yi

Allah zai yi amfani da mutum na biyu mafi ƙarfi a dukan sararin samaniya, wato, Yesu Kristi wanda aka ta da daga matattu don cika alkawarinsa. Lokaci na zuwa da Yesu zai yi sarauta ba tare da masu ƙiyayya ba a dukan duniya. ’Yan Adam ba za su sake samun sarakuna, shugabanni, da ’yan siyasa na ’yan Adam ba. Maimakon hakan, Sarki ɗaya da gwamnati ɗaya ce za ta sarauce su, wato, Mulkin Allah.

Wannan Mulkin za ya kawar da dukan gwamnatin ’yan Adam. Da daɗewa, Littafi Mai Tsarki ya annabta: “Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar wa wata al’umma ba; amma za ya parpashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.” (Daniel 2:44) Mutanen dukan duniya za su samu haɗin kai a ƙarƙashin gwamnati ɗaya ta adalci, Mulkin Allah.

Sa’ad da yake duniya a matsayin mutum, Yesu ya yi magana sau da yawa game da wannan Mulkin. Ya yi ƙaulinta a addu’ar misalinsa, ya umurce almajiransa su yi addu’a haka: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) Ka lura cewa Yesu ya nuna cewa wannan Mulkin ya yi nasaba da nufin Allah da zai kasance a cikin duniya, kuma nufin Allah ne ya kawar da wahala a duniya gabaki ɗaya.

Mulkin Allah zai kawo albarkar da gwamnatin ’yan Adam ba zai taɓa iya kawowa ba. Ka tuna cewa Jehobah ya ba da Ɗansa kamar fansa don ’yan Adam su samu rai na har abada. A ƙarƙashin sarautar Mulkin mai yalwa, mutane za su zama kamiltattu. Sakamakon? Jehobah ‘za ya haɗiye mutuwa har abada: Ubangiji Yahweh za ya share hawaye daga dukan fuskoki.’—Ishaya 25:8.

Wasu za su iya yin tambaya: ‘Me ya sa Allah bai ɗauki mataki ba kafin yanzu? Menene yake jira?’ Da Jehobah ya ɗauki mataki da daɗewa ko kuma da ya hana dukan wahala. Maimakon hakan, ya ƙyale ta ta ci gaba, ba don wani dalilin son kai ba, amma don amfanin ’ya’yansa na har abada a duniya. Iyaye masu ƙauna za su ƙyale yaransu su fuskanci wahala idan sun san cewa hakan zai kawo musu amfanin da zai daɗe. Hakazalika, akwai dalilai masu kyau da suka sa Jehobah ya ƙyale ’yan Adam su sha wahala na ɗan lokaci, kuma an bayyana waɗannan dalilan cikin Littafi Mai Tsarki. Sun ƙunshi abubuwa kamar su ’yancin zaɓi, zunubi, da kuma batun ikon mallaka na Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya kuma bayyana cewa, a ɗan lokaci, an ƙyale mugun ruhu ya yi sarautar duniyar nan.a

Ko da ba za mu iya bayyana dukan dalilan a ’yan waɗannan shafofi ba, akwai tabbaci biyu da suka ba mu bege da ƙarfafa. Na farkon shi ne wannan: Jehobah zai albarkace mu fiye da dukan wahalar da muka taɓa sha. Bugu da ƙari, Allah ya tabbatar da mu: “Ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba.” (Ishaya 65:17) Allah zai cire kaito da wahalar da ke faruwa saboda ƙyale mugunta da aka yi na ɗan lokaci ɗungum da kuma dindindin.

Gaskiya ta biyu ita ce wannan: Allah ya keɓe lokaci wanda ba za a iya canjawa ba da zai kawo ƙarshen wahala. Ka tuna cewa annabi Habakkuk ya tambayi har yaushe Jehobah zai ƙyale mugunta da husuma. Jehobah ya amsa: “Ru’yan har yanzu da ayanannen lokacinta . . . ba za ta yi jinkiri ba.” (Habakkuk 2:3) Kamar yadda za mu gani a talifi na gaba, wannan ‘ayanannen lokaci’ ya kusa.

[Hasiya]

a Don cikakken bayani game da dalilin da ya sa Allah ya ƙyale wahala, ka duba shafi na 11 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Akwati da ke shafi na 7]

Nassosi da Suka Yi Magana Game da Gaba Mai Ban Al’ajabi

BABU SAURAN YAƘE-YAƘE:

“Ku zo, ku duba ayyukan Ubangiji, Irin rushewa da ya yi cikin duniya. Ya sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya; Ya karya baka, ya daddatse māshi; Ya ƙoƙone karusai cikin wuta.”—Zabura 46:8, 9.

ƘAUNATATTU ZA SU TASHI DAGA MATATTU:

“Za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.”—Ayyukan Manzanni 24:15.

ABINCI DON KOWA:

“Za a yi albarkar hatsi a ƙasa a bisa ƙwanƙolin duwatsu.”—Zabura 72:16.

BA ZA A ƘARA CIWO KUMA BA:

“Wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.”—Ishaya 33:24.

MIYAGUN MUTANE BA ZA SU WANZU BA:

“Amma za a datse miyagu daga cikin ƙasan, za a tumɓuke masu-cin amana kuma.”—Misalai 2:22.

ADALCI ZA TA KASANCE:

“Duba, wata rana wani sarki [Yesu Kristi] za ya yi mulki cikin adalci, hakimai kuma za su yi mulki da shari’a.”—Ishaya 32:1.

[Hotuna da ke shafi na 7]

Mulkin Allah zai kawo ƙarshen kowacce irin wahalar da muka taɓa sha

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba