Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 11/15 pp. 24-29
  • Nuna Halin Kirki A Matsayin Masu Hidima Ta Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Nuna Halin Kirki A Matsayin Masu Hidima Ta Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah da Ɗansa, Misalan Halin Kirki Ne
  • Gai da Mutane da Kuma Yi Musu Magana
  • Nuna Hali Mai Kyau a Yanayi Mai Wuya
  • Hanya Mafi Kyau na Koyan Halin Kirki
  • Halin Kirki na Sa Mu Kasance Dabam
  • Nuna Ladabi Yana da muhimmanci Kuwa?
    Tambayoyin Matasa
  • Ku Koya wa Yaranku Yin Ladabi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Abubuwan da Bai Kamata a Yi Ba a Wa’azi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 11/15 pp. 24-29

Nuna Halin Kirki A Matsayin Masu Hidima Ta Allah

“Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu.”—AFIS. 5:1.

1, 2. (a) Me ya sa halin kirki yake da muhimmanci? (b) Menene za a tattauna a wannan talifin?

GAME da halin kirki, mawallafiya Sue Fox ta rubuta: “Ya kamata mu riƙa nuna halaye masu kyau a koyaushe. Halin kirki yana da kyau a ko’ina, a dukan lokaci.” Sa’ad da mutane suka sa nuna hali mai kyau ya zama halinsu, za su rage samun matsala da mutane kuma sau da yawa ba za su ƙara yin jayayya ba. Amma yi wa mutane rashin hankali yana kawo faɗa, ƙiyayya, da kuma baƙin ciki.

2 A galibi, mutane da suke cikin ikilisiyar Kirista masu halin kirki ne. Duk da haka, dole ne mu mai da hankali kada mu koyi mummunar halin da ke ko’ina a duniya ta yau. Bari mu ga yadda bin ƙa’idodi na Littafi Mai Tsarki a batun halin kirki zai kāre mu kuma ya jawo mutane zuwa bauta ta gaskiya. Don mu fahimci abin da nuna halin kirki ya ƙunsa, ka yi la’akari da misalan Jehobah Allah da Ɗansa.

Jehobah da Ɗansa, Misalan Halin Kirki Ne

3. Wane misali na halin kirki ne Jehobah Allah ya kafa?

3 Jehobah Allah ya kafa misali mafi kyau na halin kirki. Duk da cewa, yana da matsayi mai girma na Mamallakin sararin samaniya, yana bi da mutane cikin alheri da daraja. A yare na asali, sa’ad da yake magana ga Ibrahim da Musa, Jehobah ya yi amfani da kalmar Ibrananci da ke sa umurni ya zama kamar roƙo.” (Far. 13:14; Fit. 4:6) Sa’ad da bayinsa suka yi kuskure, Jehobah mai ‘juyayi ne mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya.’ (Zab. 86:15) Dabam yake da wasu mutane da suke fushi sosai sa’ad da wasu suka kasa yin abin da suke tsammani.

4. Ta yaya za mu yi koyi da Jehobah sa’ad da wasu suke magana da mu?

4 Muna iya koya game da halin kirki daga yadda Allah yakan saurari mutane. Sa’ad da Ibrahim ya yi tambayoyi game da mutanen Saduma, Jehobah ya amsa kowanne da haƙuri. (Far. 18:23-32) Bai ɗauki damuwar Ibrahim cewa yana ɓata Masa lokaci ba. Jehobah yana saurarar addu’o’in bayinsa da kuma kukan masu zunubi da suka tuba. (Karanta Zabura 51:11, 17.) Ya kamata mu yi koyi da Jehobah ta wajen saurarawa sa’ad da wasu suke magana da mu.

5. Ta yaya yin koyi da hali mai kyau na Yesu zai kyautata dangantakarmu da mutane?

5 Halin kirki yana cikin abubuwa masu yawa da Yesu Kristi ya koya daga Ubansa. Ko da yake a wani lokaci hidimarsa yana ɗaukan lokacinsa da kuzari, a koyaushe Yesu yana yin haƙuri da alheri. Yesu da son rai yana shirye ya taimaka wa kutare, makafi da za su yi roƙo kafin su biya bukatarsu, da sauran mabukata. Bai yi banza da su ba ko da yake ba su gaya masa tun da wuri cewa suna zuwa ba. Sau da yawa yakan daina abin da yake yi don ya taimaka wa wanda yake cikin matsanancin hali. Yesu yana yin la’akari sosai ga waɗanda suka ba da gaskiya a gare shi. (Mar. 5:30-34; Luk 18:35-41) A matsayin Kiristoci, muna bin misalin Yesu ta wajen yin alheri da kuma ba da taimako. Danginmu, maƙwabta, da kuma wasu suna ganin irin wannan halin. Bugu da ƙari, irin wannan halin na ɗaukaka Jehobah kuma yana sa mu farin ciki.

6. Wane misali ne na daɗaɗawa da abokantaka Yesu ya kafa?

6 Yesu ya kuma daraja mutane ta wajen yin amfani da sunayensu. Shugabanan addinai na Yahudawa suna daraja mutane hakan kuwa? A’a. Suna ɗaukan waɗanda ba su san Dokar ba a matsayin “la’anannu” kuma suna bi da su hakan. (Yoh. 7:49) Ɗan Allah bai bi da mutane hakan ba. Ya kira Martha, Maryamu, Zakka, da mutane da yawa da sunansu. (Luk 10:41, 42; 19:5) Ko da yake al’ada da yanayi suna iya nuna yadda muke bi da mutane a yau, bayin Jehobah suna ƙoƙari su kasance da fara’a ga mutane.a Ba sa barin bambanci ya sa su rage daraja abokansu masu bi da wasu ba.—Karanta Yaƙub 2:1-4.

7. Ta yaya ne mizanan Littafi Mai Tsarki suke taimakawa wajen daraja ’yan Adam a ko’ina?

7 Hanya mai kyau da Allah da Ɗansa suke bi da mutane na dukan al’ummai da ƙabilai ta nuna cewa suna daraja irin waɗannan mutane kuma yana jawo waɗanda suke da zuciyar kirki zuwa gaskiya. Hakika, abin da ke nuna halin kirki ya bambanta dangana da wurare. Saboda haka, ba ma bin tsarin dokoki masu wuya game da hali. Maimakon haka, muna barin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki su sa mu riƙa daidaitawa wajen daraja mutane a ko’ina. Bari mu bincika yadda bi da mutane da halin kirki zai sa mu ƙara ba da ’ya’ya a hidima na Kirista.

Gai da Mutane da Kuma Yi Musu Magana

8, 9. (a) Wane hali ne ba shi da kyau? (b) Me ya sa za mu bar kalaman Yesu da ke rubuce a Matta 5:47 su shafi yadda muke bi da mutane?

8 A rayuwar yau da mutane sun shagala da ayyuka a ko’ina a wurare da yawa, sau da yawa mutane biyu sukan wuce juna ba tare da cewa “sannu” ko kuma “yaya kake ba?” Hakika, ba a bukatar mutum ya yi magana ga kowa da ke wucewa a hanya da mutane suke da yawa. Amma, a wasu yanayi da yawa, ya dace kuma yana da kyau a gai da mutane. Halinka ne ka gai da mutane? Ko kuwa sau da yawa kana wucewa ba tare da yin murmushi ko kuma magana mai daɗi ba? Ba tare da mugun nufi ba, mutum yana iya koyan halin da ba shi da kyau.

9 Yesu ya tunasar da mu sa’ad da ya ce: “Idan kuwa kuna gaida ’yan’uwanku kaɗai, ina fifikonku waɗansu? ko al’ummai ba haka su ke yi ba?” (Mat. 5:47) Saboda haka, Donald Weiss ya rubuta: “Mutane sukan yi fushi sa’ad da wasu suka wuce su ba tare da yin gaisuwa ba. Babu hujja mai kyau da za ka ba da don yin banza da mutum. Maganin yana da sauƙi: Ka gai da mutane. Ka yi musu magana.” Idan ba mu bar ƙin tarayya ko kuma rashin fara’a ya shafi yadda muke sha’ani da mutane, za mu samu sakamako mai kyau.

10. Ta yaya halin kirki zai taimaka mana mu ba da ’ya’ya a hidima? (Ka duba akwati “Ka Soma da Yin Murmushi da Gaisuwa Cikin Fara’a.”)

10 Ka yi la’akari da ma’aurata Kirista masu suna Tom da Carol, da suke da zama a babban birnin Arewacin Amirka. Sun sa tattaunawa mai daɗi da maƙwabtansu ya zama sashen hidimarsu. Yaya suke yin hakan? Da yake nuni ga Yaƙub 3:18, Tom ya ce: “Muna ƙoƙari mu kasance da fara’a da kuma salama da mutane. Muna tuntuɓar mutane da muke gani a waje da gidansu da kuma waɗanda suke aiki a yankin. Muna murmushi kuma mu gai da su. Muna magana game da abin da suke so, wato, yaransu, karensu, gidansu, da kuma aikinsu. Da shigewar lokaci suna ɗaukanmu a matsayin abokansu.” Carol ta daɗa: “Idan mun sake ziyararsu, muna ba su sunayenmu kuma mu ce su ba mu nasu. Muna gaya musu abin da muke yi a unguwar amma ba ma dogon tattaunawa. Daga baya sai mu yi musu wa’azi.” Tom da Carol sun sa maƙwabtansu da yawa su amince da su. Da yawa cikinsu sun karɓi littattafai da ke bisa Littafi Mai Tsarki, kuma kalilan sun nuna suna son su koya gaskiya.

Nuna Hali Mai Kyau a Yanayi Mai Wuya

11, 12. Me ya sa za mu yi tsammani cewa za a wulakanta mu sa’ad da muke wa’azin bishara, yaya ya kamata mu aikata?

11 A wasu lokatai, muna fuskantar halin da bai dace ba sa’ad da muke wa’azin bishara. Mun san cewa hakan zai faru, gama Yesu Kristi ya gargaɗi almajiransa: “Idan suka tsananta mini, zasu tsananta muku kuma.” (Yoh. 15:20) Amsawa da baƙar magana ba ta kawo sakamako mai kyau. Yaya ya kamata mu aikata? Manzo Bitrus ya rubuta: “Cikin zukatanku ku tsarkake Kristi kamar Ubangiji: kullum a shirye kuke ku amsa ma kowane mai-tambayarku dalilin begen da ke cikinku, amma dai da ladabi da tsoro.” (1 Bit. 3:15) Nuna hali mai kyau, mai da martani cikin natsuwa da ladabi, zai iya canja halin waɗanda suke zaginmu.—Tit. 2:7, 8.

12 Muna a shirye mu fuskanci baƙar magana a hanyar da Allah zai amince da ita? E. Bulus ya ce: ‘Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, gyartacce da gishiri, domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.’ (Kol. 4:6) Idan muka sa ya zama halinmu mu aikata da ladabi ga waɗanda suke cikin iyalinmu, abokan aiki, waɗanda suke cikin ikilisiya, da kuma maƙwabtanmu, za mu fi kasancewa a shirye mu fuskanci ba’a da zagi a hanyar da ta cancanci Kirista.—Karanta Romawa 12:17-21.

13. Ka ba da misali da ya nuna yadda halin kirki zai iya sa masu hamayya da mu su daina.

13 Nuna halin kirki a yanayi mai wuya yana kawo sakamako mai kyau. Alal misali, a Japan, wani Mashaidi ya fuskanci ba’a daga wani mai gida da baƙonsa. Ɗan’uwan ya bar ƙofar cikin ladabi. Sa’ad da ya ci gaba da yin wa’azi a yankin, ya lura cewa baƙon yana kallonsa daga ɗan nesa. Sa’ad da ɗan’uwan ya taho kusa da shi, mutumin ya ce: “Ɗan Allah ka yi haƙuri da abin da ya faru. Ko da yake mun yi maka baƙar magana, na lura cewa ka ci gaba da yin murmushi. Menene zan yi don na riƙa yin hakan?” Domin wannan mutumin ya yi rashin aikinsa kuma mamarsa ta rasu ba da daɗewa ba, yana ganin ba zai ƙara yin farin ciki kuma ba. Mashaidin ya ce ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma mutumin ya yarda. Ba da daɗewa ba ya soma nazari sau biyu a mako.

Hanya Mafi Kyau na Koyan Halin Kirki

14, 15. Yaya bayin Jehobah a lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki suka yi renon yaransu?

14 Iyaye masu ibada a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki sun tabbata cewa yaransu sun koya nuna ladabi a gida. Ka yi la’akari da yadda Ibrahim da ɗansa suka yi magana da juna cikin ladabi a Farawa 22:7. Yusufu ma ya nuna cewa iyayensa sun yi renonsa da kyau. Sa’ad da aka saka shi a cikin fursuna, ya nuna ladabi har ga sauran fursunoni. (Far. 40:8, 14) Kalamansa ga Fir’auna sun nuna cewa ya koya hanyar da ta dace na yin magana ga wanda yake da matsayi mai girma.—Far. 41:16, 33, 34.

15 Dokoki goma da aka ba ’ya’yan Isra’ila sun ƙunshi wannan umurnin: “Ka bada girma ga ubanka da uwarka: domin kwanakinka su yi tsawo cikin ƙasa wadda Ubangiji Allahnka ke ba ka.” (Fit. 20:12) Hanya ɗaya da yara za su ba da girma ga iyayensu ita ce ta wajen nuna halaye masu kyau a gida. ’Yar Jephthah ta nuna ladabi na musamman ga ubanta ta wajen amincewa da alkawarin da ya yi a yanayi mai wuya.—Alƙa. 11:35-40.

16-18. (a) Menene za a yi don a koya wa yara halin kirki? (b) Menene amfanin koya wa yaran halin kirki?

16 Renon yaranmu su zama masu yin ladabi yana da muhimmanci sosai. Don su yi dangantaka mai kyau da mutane idan sun yi girma, yara suna bukatar su koya hanyar da ta dace su gai da baƙi, su amsa tarho, kuma su ci abinci da wasu. Ya kamata a taimake su su fahimci abin da ya sa yake da kyau su tashi daga wajen zamansu don manyan su zauna, su nuna wa tsofaffi da masu ciwo alheri, kuma su taimaka wa waɗanda suka ɗauki kaya masu nauyi. Suna bukatar su fahimci muhimmancin faɗan “don Allah,” “na gode” “sannu da zuwa,” “bari in taimake ka,” da kuma “ka yi haƙuri.”

17 Koyar da yara su riƙa nuna ladabi bai kamata ya kasance da wuya ba. Hanyar da ta fi kyau ita ce nuna misali mai kyau. Kurt, ɗan shekara ashirin da biyar ya faɗa yadda shi da ’yan’uwansa uku suka koya su nuna ladabi: “Muna lura da kuma saurarar yadda Baba da Mama suke wa juna magana da ladabi kuma suna bi da mutane da haƙuri kuma suna la’akari da su. A Majami’ar Mulki, Baba yakan tafi da ni kafin a soma taro da kuma bayan taro mu yi magana da ’yan’uwa tsofaffi. Na ji yadda yake gai da su kuma yadda yake nuna musu ladabi.” Kurt ya ci gaba da cewa: “Da shigewar lokaci, na koya halinsa. Nan da nan na soma bi da mutane da ladabi. Ba yadda dole za ka aikata ba, amma yadda za ka so ka aikata.”

18 Menene zai faru idan iyaye suka koya wa yaransu halin kirki? Yaran za su iya samun abokai kuma su kasance da salama da mutane. Za su kasance a shirye sosai su yi aiki da shugaban aikinsu da kuma abokan aikinsu. Bugu da ƙari, yara masu halin kirki, da kuma adalci za su sa iyayensu su samu gamsuwa kuma su yi farin ciki.—Karanta Misalai 23:24, 25.

Halin Kirki na Sa Mu Kasance Dabam

19, 20. Me ya sa za mu ƙudiri aniya mu yi koyi da Allahnmu mai alheri da kuma Ɗansa?

19 Bulus ya rubuta, “ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu.” (Afis. 5:1) Yin koyi da Jehobah Allah da Ɗansa ya ƙunshi bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, kamar waɗanda aka tattauna a wannan talifin. Ta wajen yin haka, za mu guji munafuncin nuna halin kirki don mu samu amincewar wani mai matsayi mai girma ko kuma mu samu abin mallaka.—Yahu. 16.

20 A kwanaki na ƙarshe na mugun sarautarsa, Shaiɗan ya ƙuduri aniya ya kawar da mizanan halin kirki da Jehobah ya kafa. Amma Iblis ba zai iya kawar da halin kirki na Kiristoci na gaskiya ba. Bari kowanenmu ya ƙuduri aniyar bin misalan Allahnmu mai alheri da kuma Ɗansa. Sa’an nan furcinmu da halinmu a koyaushe zai yi dabam da ayyukan waɗanda suka zaɓa su kasance da mugun hali. Za mu sa a yabi sunan Allahnmu Jehobah, wanda ya kafa kamiltaccen misali na halin kirki kuma za mu jawo mutane masu zuciyar kirki zuwa bauta ta gaskiya.

[Hasiya]

a A wasu al’adu rashin hankali ne mutum ya kira wanda ya girme shi da sunansa na fari sai dai ko mutumin ne ya gaya masa ya yi hakan. Yana da kyau Kiristoci su daraja irin waɗannan al’adu.

Ka Tuna?

• Menene muka koya daga Jehobah da Ɗansa game da nuna halin kirki?

• Me ya sa gai da mutane da kyau zai sa mu kasance da sunan kirki a matsayin Kiristoci?

• Ta yaya halin kirki zai sa hidimarmu ta ba da ’ya’ya?

• Wane hakki ne iyaye suke da shi wajen koya wa yaransu halin kirki?

[Akwati da ke shafi na 27]

Ka Soma da Yin Murmushi da Gaisuwa Cikin Fara’a

Mutane da yawa suna jinkirin soma taɗi da wanda ba su sani ba. Amma, domin suna ƙaunar Allah da kuma maƙwabtansu, Shaidun Jehobah suna iya ƙoƙarinsu su koya yadda ake taɗi domin su gaya wa mutane gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Menene zai taimake ka ka yi gyara a wannan batun?

An ambata wata ƙa’ida mai kyau a Filibiyawa 2:4, wadda ta ce: “Ba dai kowa yana lura da nasa abu ba, amma kowane a cikinku yana lura da na waɗansu kuma.” Ka yi tunanin waɗannan kalmomin a wannan hanyar: Idan ba ka taɓa saduwa da mutum a dā ba, zai ɗauke ka a matsayin baƙo. Yaya za ka sa ya saki jiki? Yin murmushi da kuma gaisuwa cikin fara’a zai taimaka. Duk da haka, da akwai ƙarin abubuwa da za ka yi la’akari da su.

Ta wajen yin ƙoƙari ka soma tattaunawa da wani, mai yiwuwa ka katse masa tunani. Idan ka yi ƙoƙari ka sa ya tattauna abin da ke zuciyarka ba tare da damuwa da abin da ke nasa zuciya ba, wataƙila ba zai saurare ka ba. Saboda haka, idan za ka iya sanin abin da mutumin yake tunaninsa, ka yi amfani da wannan ka soma tattaunawa da shi. Abin da Yesu ya yi ke nan sa’ad da ya sadu da wata mata a bakin rijiya a Samariya. (Yoh. 4:7-26) Tana tunanin ɗiban ruwa. Yesu ya soma tattaunawa da abin da take tunaninsa, kuma ba da daɗewa ba ya mai da shi tattaunawa na ruhaniya mai kyau.

[Hotunan da ke shafi na 26]

Kasancewa da halin abokantaka da mutane zai sa mu ba da shaida mai kyau

[Hotunan da ke shafi na 28]

Halin kirki yana da kyau a koyaushe

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba