Ƙaramar Yarinya Mai Karimci
BA DA daɗewa ba, wata yarinya mai shekara tara a Brazil da kanta ta raba kuɗi da ta ajiye zuwa kashi biyu, dalla 18 da kuma dalla 25. Ta saka dalla 18 a cikin akwati da ke cikin Majami’ar Mulki don ikilisiya ta yi amfani da shi. Sai ta aika dalla 25 zuwa ofishin reshe na Shaidun Jehobah, kuma ta rubuta ɗan ƙaramar wasiƙa. Ta faɗa a cikin wasiƙar: “Ina son na ba da wannan kyautar don aiki da ake yi a dukan duniya. Ina son na taimaka wa ’yan’uwa da yawa a dukan duniya su yi wa’azin bishara. Ina ba da wannan kuɗin don ina ƙaunar Jehobah sosai.”
Iyayen ƙaramar yarinyar sun koya mata cewa yana da muhimmanci ta yi iya ƙoƙarinta ta sa hannu a aikin wa’azi na Mulki. Sun kuma koya mata bukatar ‘girmama Ubangiji da wadatarta.’ (Mis. 3:9) Kamar wannan ƙaramar yarinya, bari dukanmu mu kasance da himma wajen ɗaukaka al’amura ta Mulki a yankinmu da kuma dukan duniya!