Ka Ci Gaba Da Ƙara Nuna Ƙaunar ’Yan’uwa
“Ku yi tafiya cikin ƙauna, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunace ku.”—AFIS. 5:2.
1. Menene Yesu ya faɗa zai zama abu na musamman da za a san mabiyansa da shi?
AN SAN Shaidun Jehobah da yin wa’azin bisharar Mulkin Allah na gida gida. Duk da haka, Kristi Yesu ya zaɓi wani fanni dabam na Kiristanci don a san almajiransa na gaskiya da shi. Ya ce: “Sabuwar doka na ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna. Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.”—Yoh. 13:34, 35.
2, 3. Yaya ƙaunarmu ta ’yan’uwa take shafan waɗanda suke halartan taronmu na Kirista?
2 Babu wani da yake nuna ƙauna kamar wadda take tsakanin ’yan’uwancinmu na Kirista na gaskiya. Kamar yadda maganaɗisu yake jan ƙarfe, haka ne ƙauna take sa bayin Jehobah su kasance da haɗin kai kuma tana jawo masu son gaskiya zuwa bauta ta gaskiya. Alal misali, Marcelino, wani mutum a Kamaru ya yi hasarar idanunsa a wajen aiki. Bayan tsausayin da ya same shi, aka yaɗa jita-jita cewa ya makanta domin shi maye ne. Maimakon su yi masa ta’aziyya, fasto da waɗanda suke cikin cocinsu suka kore shi daga cikin ikilisiya. Sa’ad da wani Mashaidin Jehobah ya gayyace shi zuwa taro, Marcelino ya yi jinkiri. Ba ya son a sake ƙin sa.
3 Marcelino ya yi mamaki da abin da ya faru a Majami’ar Mulki. Waɗanda suke cikin ikilisiya sun marabce shi sosai, kuma ya samu ta’aziyya daga koyarwar Littafi Mai Tsarki da ya ji. Ya soma halartan dukan tarurrukan ikilisiya, ya samu ci gaba a nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma aka yi masa baftisma a shekara ta 2006. Yanzu yana yi wa iyalinsa da maƙwabtansa wa’azi kuma ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa. Marcelino yana son waɗanda yake nazarin Littafi Mai Tsarki da su su shaida irin ƙaunar da mutanen Allah suka nuna masa.
4. Me ya sa za mu yi biyayya da gargaɗin Bulus mu “yi tafiya cikin ƙauna”?
4 Wannan ƙauna ta ’yan’uwa tana da ban sha’awa, kuma ya kamata mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu ci gaba da nuna ta. Ka yi tunanin wuta da mutane suke ɗumama kansu da ita da daddare. Idan waɗanda suke jin daɗin ɗuminta ba su ci gaba da saka mata itace ba, wutar za ta mutu. Hakan nan ma, gami na ƙauna da ke cikin ikilisiya zai yi sanyi, idan mu Kiristoci ba mu ci gaba da ƙarfafa shi ba. Ta yaya za mu iya yin hakan? Manzo Bulus ya ba da amsar: “Ku yi tafiya cikin ƙauna, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunace ku, ya bada kansa kuma domin ku, abin miƙawa da hadaya ga Allah domin shesheƙi na ƙamshi mai-daɗi.” (Afis. 5:2) Tambayar da muke son mu bincika ita ce, A waɗanne hanyoyi ne zan ci gaba da yin tafiya cikin ƙauna?
“Ku Buɗe Zuciyarku”
5, 6. Me ya sa Bulus ya aririci Kiristoci da ke Koranti su ‘buɗe zuciyarsu’?
5 Manzo Bulus ya rubuta ga Kiristoci da ke Koranti na dā: “Bakinmu a buɗe ya ke gare ku, ku Korintiyawa, zuciyarmu a faɗaɗe ta ke. Ba mu, muka ki ƙaunarku ba; amma cikin zukatanku ba ku karɓe mu ba. Yanzu fa, domin a yi musaya daidai ina magana kamar ga yara sai ku buɗe zuciyarku haka nan.” (2 Kor. 6:11-13) Me ya sa Bulus ya aririci Kiristoci su buɗe zuciyarsu wajen nuna ƙauna?
6 Ka yi la’akari da yadda ikilisiya ta Koranti ta dā ta soma. Bulus ya isa Koranti a kusan ƙarshen shekara ta 50 A.Z. Ko da yake sa’ad da ya soma wa’azi a wajen wasu mutane sun yi hamayya da shi, manzon bai ja da baya ba. A ɗan lokaci, mutane da yawa a cikin wannan birnin suka ba da gaskiya ga wa’azin bishara. Bulus ya zauna “shekara guda da wata shidda” yana koyar da kuma ƙarfafa sabuwar ikilisiyar. A bayyane yake cewa yana ƙaunar Kiristoci da ke Koranti sosai. (A. M. 18:5, 6, 9-11) Suna da kowane dalili na ƙaunarsa da kuma nuna masa ladabi. Amma, wasu a cikin ikilisiyar sun guje shi. Wataƙila kalilan ba sa son yadda yake yi musu gargaɗi kai tsaye. (1 Kor. 5:1-5; 6:1-10) Mai yiwuwa wasu sun saurari tsegumin “mafifitan manzanni.” (2 Kor. 11:5, 6) Bulus yana so dukan ’yan’uwansa maza da mata su yi ƙaunarsa. Saboda haka, ya roƙe su su ‘buɗe zuciyarsu’ ta wajen kusantarsa da kuma sauran ’yan’uwa masu bi.
7. Ta yaya za mu ‘buɗe zuciyarmu’ wajen nuna ƙauna ta ’yan’uwa?
7 Mu kuma fa? Ta yaya za mu ‘buɗe zuciyarmu’ ta wajen nuna ƙauna ta ’yan’uwa? Yana iya yi wa mutane tsara ɗaya ko kuma waɗanda suka fito daga ƙabila ɗaya sauƙi su nuna ƙauna ga juna. Kuma waɗanda suke son nishaɗi irin ɗaya sau da yawa sukan kasance tare. Amma idan abubuwa da muke so tare da wasu Kiristoci suna sa mu ware kanmu daga wasu, muna bukatar mu ‘buɗe zuciyarmu.’ Zai yi kyau mu tambayi kanmu: ‘Yana yi mini wuya na fita hidima ko kuma yi wasu ayyuka da ’yan’uwa maza da mata da ba abokaina ba? A Majami’ar Mulki, ina saka iyaka a tarayya ta da sababbi, da tunanin cewa za su nuna sun cancanci yin abuta da ni? Ina gai da tsofaffi da matasa a cikin ikilisiya kuwa?’
8, 9. Ta yaya gargaɗin Bulus da ke rubuce a Romawa 15:7, zai iya taimaka mana mu gai da juna a hanyar da za ta kyautata ƙaunarmu ta ’yan’uwa?
8 A batun gai da juna, kalmomin Bulus zuwa ga Romawa za su iya taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace ga ’yan’uwanmu masu bi. (Karanta Romawa 15:7.) Kalmar Hellenanci da aka fassara “karɓi” tana nufin “yin alheri ko kuma karimci, mutum ya amince da jam’iyya da yake ciki da kuma yin abuta.” Sa’ad da mai gida mai karimci a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki ya karɓi abokai a cikin gidansa, yana sanar da su cewa yana farin ciki sosai da ganinsu. A alamance, Kristi ya karɓe mu haka nan, kuma an gargaɗe mu mu yi koyi da shi wajen karɓan ’yan’uwanmu masu bi.
9 Sa’ad da muke gai da ’yan’uwanmu a Majami’ar Mulki da kuma wasu wurare, muna iya mai da hankali ga waɗanda ba mu gani ba ko kuma waɗanda muka yi magana da su da daɗewa. Zai dace ka ba da ’yan mintoci don yin hira da su. Muna iya yin hakan da wasu kuma a taro na gaba. Ba da daɗewa ba, za mu yi hira masu daɗi da yawancin ’yan’uwanmu. Bai kamata mu damu ba idan ba mu yi magana da kowa ba a rana guda. Bai kamata wani ya yi fushi idan ba mu iya gai da shi a kowanne taro ba.
10. Wane zarafi ne mai tamani dukanmu a cikin ikilisiya muke da shi, kuma yaya za mu yi amfani da shi sosai?
10 Gai da mutane shi ne mataki na farko na karɓan su. Mataki ne da zai kai ga hira mai daɗi da abuta na dindindin. Alal misali, sa’ad da waɗanda suka halarci tarurrukan gunduma da manyan tarurruka suka gabatar da kansu ga wasu kuma suka soma magana, suna begen sake ganin juna kuma. Masu gina Majami’ar Mulki da waɗanda suke aikin ba da agaji sau da yawa suna zama abokai na ƙwarai domin sukan san halayen juna masu kyau ta wurin abubuwa da suka fuskanta tare. Zarafin ƙulla abuta na dindindin suna da yawa a cikin ƙungiyar Jehobah. Idan mun ‘buɗe zuciyarmu’ abokanmu za su ƙaru, hakan zai daɗa ga ƙauna da ke haɗa mu a bauta ta gaskiya.
Ka Sa Mutane su Kusace Ka
11. Kamar yadda aka nuna a Markus 10:13-16, wane misali ne Yesu ya kafa?
11 Dukan Kiristoci suna iya yin ƙoƙari mutane su kusace su, yadda Yesu ya yi. Ka yi la’akari da yadda Yesu ya aikata sa’ad da almajiransa suka yi ƙoƙari su hana iyaye kawo yaransu zuwa wurinsa. Ya ce: “Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni; kada ku hana su: gama na irin waɗannan mulkin Allah ya ke.” Sai ya “rungume su, ya sa masu albarka, ya ɗibiya masu hannuwa.” (Mar. 10:13-16) Babu shakka waɗannan yaran sun yi farin ciki sosai sa’ad da Babban Malami ya mai da musu hankali da kyau!
12. Menene zai iya hana tattaunawa da wasu?
12 Ya kamata kowane Kirista ya tambayi kansa, ‘Ina sa mutane su kusace ni ne ko kuwa sau da yawa ina nuna kamar ina da aiki da yawa?’ Halaye da ba laifi ba ne, a wani lokaci suna iya hana mutane hira da mu. Alal misali, idan a kowane lokaci muna amfani da waya ta selula ko kuma muna saurarar kaɗe-kaɗe a inda mutane suke, suna iya ganin cewa ba ma son tarayyarsu. Idan sau da yawa mutane suna ganin mun shaƙu da kallon kwamfuta na hannu, suna iya kammala cewa ba ma son mu yi magana da su. Hakika, da akwai “lokacin shuru.” Amma idan mutane suna tare da mu, sau da yawa “lokacin magana” ne. (M. Wa. 3:7) Wasu suna iya faɗan cewa, “Na fi son kada na yi magana da kowa” ko kuwa “Ba na jin yin magana da safe.” Duk da haka, yin hira ko a lokacin da ba ma jin yin hakan, tabbaci ne na ƙauna da “ba ta biɗa ma kanta.”—1 Kor. 13:5.
13. Wane ra’ayi ne game da ’yan’uwa Bulus ya ƙarfafa Timotawus ya kasance da shi?
13 Bulus ya ƙarfafa Timotawus matashi ya daraja dukan waɗanda suke cikin ikilisiya. (Karanta 1 Timotawus 5:1, 2.) Ya kamata mu bi da Kiristoci tsofaffi a matsayin mamarmu da babanmu kuma matasa a matsayin ’yan’uwanmu, wato, yaran iyayenmu. Idan muna da wannan halin, ’yan’uwanmu ƙaunatattu ba za su yi tunanin cewa su baƙi ne ba a wajenmu amma za su kusace mu.
14. Waɗanne amfani ne ke akwai na yin tattaunawa mai ƙarfafawa da wasu?
14 Yayin da muke hira da mutane, muna daɗa ga lafiyarsu ta ruhaniya da kuma na motsin rai. Wani ɗan’uwa da yake aiki a ofishin reshe yana tuna da tsofaffi da yawa da suke hidima a Bethel da suke keɓe lokaci a kai a kai su yi magana da shi a shekarunsa na farko a Bethel. Kalamansu na ban ƙarfafa sun sa ya ji cewa iyalin Bethel suna ƙaunarsa. Yanzu yana ƙoƙari ya yi koyi da su ta wajen yin hira da ’yan’uwansa masu bi da suke Bethel.
Tawali’u Yana Taimaka Mana Mu Kasance da Salama
15. Menene ya nuna cewa muna jayayya?
15 Afodiya da Sintiki, ’yan’uwa mata biyu a Filibi na dā, mai yiwuwa suna da matsala wajen magance jayayya da ta taso tsakaninsu. (Filib. 4:2, 3) Mutane sun san cewa Bulus da Barnaba sun yi jayayya sosai kuma hakan ya sa kowa ya kama gabansa na ɗan lokaci. (A. M. 15:37-39) Waɗannan labaran sun nuna cewa wani lokaci jayayya takan taso tsakanin masu bauta na gaskiya. Jehobah ya yi mana tanadin taimako don mu magance jayayya kuma mu dawo da abuta. Amma yana bukatar mu yi wani abu.
16, 17. (a) Me ya sa tawali’u yake da muhimmanci wajen magance faɗace-faɗace? (b) Ta yaya labarin yadda Yaƙub ya sadu da Isuwa ya kwatanta amfanin tawali’u?
16 A ce kai da abokinka za ku yi tafiya da mota. Kafin ku soma tafiya, za ka sa makulli a makunnin motar kuma ka kunna injin motar. Ana soma magance jayayya da makulli. Makullin shi ne tawali’u. (Karanta Yaƙub 4:10.) Kamar yadda misali na gaba da ke cikin Nassi ya nuna, wannan makullin yana sa waɗanda suke fushi da juna su soma yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.
17 Shekaru ashirin sun wuce tun lokacin da Isuwa ya yi fushi don hasarar damarsa na ɗan fari ga tagwayensa, Yaƙubu, kuma ya so ya kashe shi. Tagwayen za su sadu kuma bayan waɗannan shekaru, “Yaƙub ya ji tsoro ƙwarai, ransa kuma ya karaya.” Yana jin cewa yana yiwuwa Isuwa ya tasam masa. Amma da suka sadu, Yaƙub ya yi wani abu da Isuwa bai yi tsammani zai yi ba. “Ya yi ta rusunawa har ƙasa” har ya kai kusa da ɗan’uwansa. Menene ya faru kuma? “Isuwa kuwa ya sheƙo a guje domin ya tarbe shi, ya kuwa rungume shi, ya fāɗa wa wuyansa, ya yi masa sumba: suka yi kuka.” Hakan ya sa ba a yi faɗa ba. Tawali’un Yaƙub ya taimaka wajen sha kan kowacce ƙiyayya da Isuwa yake da ita.—Far. 27:41; 32:3-8; 33:3, 4.
18, 19. (a) Sa’ad da jayayya ta taso, me ya sa yake da muhimmanci mu yi amfani da gargaɗin Nassi? (b) Me ya sa bai kamata mu karaya ba idan ɗayan mutumin bai aikata yadda ya dace ba da farko?
18 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da gargaɗi mafi kyau don magance faɗace-faɗace. (Mat. 5:23, 24; 18:15-17; Afis. 4:26, 27)a Amma, idan ba mu yi amfani da wannan gargaɗin ba, yin salama zai yi mana wuya. Jira wani ya nuna tawali’u ba zai magance matsalar ba yayin da ya kamata mu ma mu nuna tawali’u.
19 Idan mun yi ƙoƙari mu yi salama amma ba mu yi nasara ba don wani dalili, bai kamata mu fid da rai ba. Mutumin mai yiwuwa yana bukatar lokaci ya daidaita yadda yake ji. ’Yan’uwan Yusufu sun ci amanarsa. Ya daɗe sosai kafin su gan shi, amma yanzu shi ne firayim minista na ƙasar Masar. Amma, daga baya, sun canja zuciyarsu kuma sun roƙi gafara. Yusufu ya gafarta musu, kuma ’ya’yan Yaƙubu suka zama al’umma da take da gatar ɗauke da sunan Jehobah. (Far. 50:15-21) Ta wajen kasancewa da salama da ’yan’uwanmu, za mu daɗa ga haɗin kai da farin ciki na ikilisiyar.—Karanta Kolosiyawa 3:12-14.
Bari Mu Nuna Ƙauna da “Aiki da Gaskiya Kuma”
20, 21. Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda Yesu ya wanke ƙafafun manzanninsa?
20 Ba da daɗewa ba kafin mutuwarsa, Yesu ya gaya wa manzanninsa: “Gama na yi muku kwatanci, domin ku kuma ku yi kamar yadda na yi muku.” (Yoh. 13:15) Bai jima da gama wanke ƙafafun manzanni goma sha biyu ba. Abin da Yesu ya yi ba al’ada kawai ba ce ko kuma alheri. Kafin ya ba da labarin wanke ƙafafu, Yohanna ya rubuta: “Tun da [Yesu] ya yi ƙaunar nasa da ke cikin duniya, ya ƙaunace su har matuƙa.” (Yoh. 13:1) Ƙaunar da yake yi wa almajiransa ne ta motsa Yesu ya yi hidimar da bawa yake yi. Yanzu dole ne su yi abubuwa masu kyau ga juna. Hakika, tabbataciyar ƙauna ta ’yan’uwa ya kamata ta motsa mu mu kula kuma mu damu don dukan ’yan’uwanmu Kiristoci.
21 Manzo Bitrus wanda Ɗan Allah ya wanke ƙafafunsa, ya fahimci ma’anar abin da Yesu ya yi. Ya rubuta: “Da ya ke kun tsarkake rayukanku cikin biyayyarku ga gaskiya zuwa ga sahihiyar ƙauna ta ’yan’uwa, sai ku yi ƙaunar junanku daga zuciya mai-gaskiya.” (1 Bit. 1:22) Manzo Yohanna, wanda shi ma Ubangiji ya wanke ƙafafunsa ya rubuta: “’Ya’yana ƙanƙanana, kada mu yi ƙauna da baki ko kuwa da harshe; amma da aiki da gaskiya kuma.” (1 Yoh. 3:18) Bari mu nuna ƙaunarmu ta ’yan’uwa ta wurin ayyuka.
[Hasiya]
a Ka duba littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will, shafuffuka na 144-150.
Ka Tuna?
• A waɗanne hanyoyi ne za mu iya ‘buɗe zuciyarmu’ wajen nuna ƙauna ga juna?
• Menene zai taimaka mana mu keɓe lokaci don wasu mutane?
• Yaya tawali’u yake taimaka wajen yin salama?
• Me ya kamata ya motsa mu mu kula da ’yan’uwa masu bi?
[Hotunan da ke shafi na 21]
Ka karɓi ’yan’uwa masu bi sosai
[Hotunan da ke shafi na 23]
Kada ka yi hasarar zarafi keɓe lokaci don mutane