Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 7/15 pp. 24-27
  • Na Soma ‘Tuna Mahaliccina’ Shekaru Casa’in Da Suka Shige

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Na Soma ‘Tuna Mahaliccina’ Shekaru Casa’in Da Suka Shige
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Na Soma Hidimata ta Cikakken Lokaci
  • Wa’azin Mulki a Ƙasar Waje
  • Ta da Hayaniya da Kuma Jin Saƙon
  • Aiki a Ɓoye
  • Gata da Albarka a Arewacin Ireland
  • Na Koma Jihohin Baltic
  • ‘Jehobah Bai Bar Ni Ba’
  • Albarkun da Muka Samu da Kuma Darussan da Muka Koya a Hidimarmu ga Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • “Alkawarin Aljanna a Duniya Ya Canja Rayuwata”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Latvia ta Karɓi Bishara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 7/15 pp. 24-27

Na Soma ‘Tuna Mahaliccina’ Shekaru Casa’in Da Suka Shige

Ne ya ba da Labarin Edwin Ridgwell

A RANAR 11 ga Nuwamba, a shekara ta 1918, an tara yara a makarantarmu ba zato ba tsammani su yi bikin ƙarshen Yaƙi Mai Girma, wanda ake kira Yaƙin Duniya na ɗaya. Ina ɗan shekara biyar kawai kuma ban fahimci abin da ake bikinsa ba. Duk da haka, daga abin da iyayena suka koya mini game da Allah na san cewa bai kamata na sa hannu a wannan bikin ba. Na yi addu’a ga Allah, amma ban iya riƙe kaina ba sai na soma kuka. Duk da haka, ban sa hannu a wannan bikin ba. A wannan lokacin ne na soma ‘tuna da Mahaliccina.’—M. Wa. 12:1.

’Yan watanni kafin wannan abu ya faru a makaranta, mun ƙaura zuwa kusa da birnin Glasgow a ƙasar Scotland. A wannan lokacin, Babanmu ya halarci wani jawabi da aka yi ga jama’a, mai jigo “Millions Now Living Will Never Die” (Mutane da Yawa da Suke Rayuwa Yanzu ba Za Su Taɓa Mutuwa Ba.) Wannan jawabin ya canja rayuwarsa. Babanmu da Mamarmu suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma sau da yawa sukan yi magana game da Mulkin Allah da albarka da za a samu nan gaba. Na gode wa Allah cewa tun daga lokacin iyayena sun koya mini na ƙaunaci Allah kuma na dogara gare shi.—Mis. 22:6.

Na Soma Hidimata ta Cikakken Lokaci

Sa’ad da nake ɗan shekara goma sha biyar na isa shiga babban makaranta, amma ainihi ina son na yi hidima na cikakken lokaci. Baba yana ganin cewa ni yaro ne, sai na yi aiki a wani ofishi na ɗan lokaci. Amma, muradina na son bauta wa Jehobah a hidima na cikakken lokaci yana da ƙarfi sosai, shi ya sa wata rana na rubuta wasiƙa zuwa ga ɗan’uwa J. F. Rutherford wanda yake kula da aikin wa’azi a dukan duniya a lokacin. Na tambaye shi ra’ayinsa game da shirye shiryen. Ɗan’uwa Rutherford ya amsa: “Idan ka isa yin aiki, ka isa yin hidimar Ubangiji. . . . Na gaskata cewa Ubangiji zai albarkace ka idan ka yi iyakar ƙoƙarinka ka bauta masa da aminci.” Wannan wasiƙar ta ranar 10 ga Maris, ta shekara ta 1928 ce ta ƙarfafa iyalinmu. Ba da daɗewa ba, Baba, Mama, yayata da ni muka soma hidima ta cikakken lokaci.

A shekara ta 1931, a wani taro da aka yi a Landan, Ɗan’uwa Rutherford ya yi kira ga ’yan’uwa su ba da kansu su yi bishara a ƙasashen waje. Na ba da kaina kuma aka tura ni zuwa birnin Kaunas tare da Andrew Jack, wurin ne babban birnin ƙasar Lithuania a lokacin. Ina ɗan shekara goma sha takwas a lokacin.

Wa’azin Mulki a Ƙasar Waje

A wannan lokacin, Lithuania ƙasa ce marar ni’ima a batun noma, kuma yin wa’azi a karkara ba shi da sauƙi. Samun masauki yana da wuya, kuma ba za mu taɓa manta wasu wurare da muka sauka ba. Alal misali, a wani dare ni da Andrew muka tashi domin ba mu ji daɗin barcin ba. Bayan mun kunna fitilar ƙwai, muka ga cewa gadon ya cika da kuɗin cizo. Sun cije mu daga kai zuwa ƙafa! Kowane safe har mako guda, nakan tafi wani kogi da ke kusa, na sa jikina daga wuya har kafa cikin ruwa mai sanyi don zafin ya ragu. Duk da haka, mun ƙudiri aniya mu ci gaba a hidimar. Ba da daɗewa ba, muka magance matsalar masauki sa’ad da muka sadu da wasu ma’aurata da suka karɓi gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Sun karɓe mu mu zauna a gidansu, wanda ba shi da girma amma yana da tsabta. Da farin ciki mukan kwanta a ƙasa, kuma hakan ya sa mun samu sauƙi!

A lokacin, Cocin Katolika da Cocin Orthodox na Rasha ne suke Lithuania. Mawadata ne kaɗai suke iya sayan Littafi Mai Tsarki. Ainihin manufarmu ita ce mu yi wa’azi sosai a dukan yankin yadda zai yiwu kuma mu raba littattafai na Littafi Mai Tsarki ga waɗanda suke so. Da farko mukan nemi masauki a cikin gari. Sai mu yi wa’azi a wurare masu nisa da basira, kuma mu zo mu gama garin da sauri. Ta wannan hanya, mukan gama aikinmu kafin firistoci na yankin su ta da wahala.

Ta da Hayaniya da Kuma Jin Saƙon

A shekara ta 1934, an tura Andrew ya je ya yi aiki a ofishin reshe da ke Kaunas, kuma John Sempey ya zama abokin hidimata. Da akwai wasu abubuwa da suka faru da ba za mu taɓa mantawa. Wata rana da na je ofishin wani lauya a wani ƙaramin gari. Mutumin ya yi fushi, kuma ya fito da ƙaramar bindiga daga durowansa, kuma ya umurce ni na fita. Na yi addu’a a cikin zuciyata kuma na tuna maganar Littafi Mai Tsarki: “Mayasda magana da taushi ya kan juyarda hasala.” (Mis. 15:1) Sai na ce, “Na zo da saƙon bishara a matsayin aboki, kuma na gode maka da kame kanka.” Mutumin bai ɗana bindigar ba, na fita da baya daga ofishinsa a hankali.

Sa’ad da na sake saduwa da John, ya gaya mini cewa shi ma ya fuskanci matsala. An kai shi ofishin ’yan sanda domin ana zarginsa da cewa ya saci takardar banki mai muhimmanci sosai daga wata mata. A ofishin, an tilasta wa John ya tuɓe kayansa don su caje shi. Hakika, bai ɗauki takardar bankin ba. Daga baya aka kama ainihin ɓarawon.

Dukan abubuwan da suka faru sun ta da hayaniya a wannan garin mai lumana amma sun sa mutane su san aikinmu sosai!

Aiki a Ɓoye

Aiki ne mai haɗari a kai littattafan Littafi Mai Tsarki cikin ƙasar Latvia da ke kusa, inda aka hana aikinmu na wa’azi. Muna tafiya zuwa Latvia da jirgin ƙasa na dare sau ɗaya a wata. A wasu lokatai, bayan mun ajiye littattafan, sai mu tafi ƙasar Estonia don mu ɗauko ƙarin littattafai, kuma mu ajiye a ƙasar Latvia sa’ad da muke dawowa.

Akwai lokacin da aka gaya wa wani ɗan kwastan game da aikinmu kuma ya ce mu bar jirgin mu kai wa shugabansa littattafan. Ni da John muka yi wa Jehobah addu’a ya taimake mu. Abin mamaki, ɗan kwastan ɗin bai gaya wa shugabansa abin da muka ɗauko, abin da kawai ya ce shi ne, “Waɗannan mutane suna da wani abu da za su sanar da kai.” Ina “sanar” da abin da nake kira littattafai da za su taimaki mutane a makarantu da kwaleji su fahimci ma’anar abin da yake faruwa a duniyarmu da ta wahala. Ɗan kwastan ɗin ya ƙyale mu, kuma muka isar da littattafan babu matsala.

Yayin da yanayin siyasa na jihohin Baltic suka daɗa muni, mutane suka daɗa tsananta wa Shaidun Jehobah kuma aka hana aikinmu na wa’azi a Lithuania. Aka kore Andrew da John daga ƙasar, kuma da yake Yaƙin Duniya na biyu na kan hanya, an gargaɗi dukan mutanen da suka zo daga ƙasar Britaniya su bar ƙasar. Na yi baƙin ciki domin ni ma zan bar ƙasar.

Gata da Albarka a Arewacin Ireland

A lokacin, iyayena sun riga sun ƙaura zuwa Ireland ta arewa, kuma na bi su a shekara ta 1937. An hana mu yin amfani da littattafanmu a Ireland ta Arewa domin yadda mutane suke ji game da yaƙin, amma mun ci gaba da wa’azi a duk lokacin yaƙin. Bayan Yaƙin Duniya na Biyu, muka soma aikinmu kuma ban da hani na doka. Herold King, wani majagaba da ya manyanta da daga baya ya yi hidima a Sin, ya yi ja-gora wajen shirya jawabai a fili ga jama’a. Ya ce: “Wannan Asabar zan ba da jawabi a fili ga jama’a a lokaci na farko.” Sai ya kalle ni ya ce, “Kai za ka ba da jawabi Asabar mai zuwa.” Na yi mamaki ƙwarai.

Na tuna jawabi na na farko sosai. Ɗarurruwan mutane na wajen. Na tsaya a kan akwati ina ba da jawabin kuma ina magana ban da taimakon kayayyakin sauti. A ƙarshen jawabin, wani mutum ya zo wajena, muka gaisa, kuma ya ce sunansa Bill Smith ne. Ya ce ya lura cewa jama’a sun taru, sai ya tsaya ya ga abin da yake faruwa. Ya zama cewa babana ya yi wa Bill wa’azi a dā amma sun daina nazari sa’ad da Baba da matarsa suka ƙaura zuwa Dublin don su yi aikin majagaba a wajen. Muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Da shigewar lokaci, mutane tara daga iyalin Bill suka zama bayin Jehobah.

Daga baya na yi wa’azi a wata unguwa da ke da manyan gidaje a bayan birnin Belfast, inda na sadu da wata mata ’yar Rasha da take Lithuania a dā. Sa’ad da na nuna mata wasu littattafai, sai ta nuna wani littafi kuma ta ce: “Ina da wannan. Kawuna wanda farfesa ne a jami’ar da ke Kaunas ne ya ba ni.” Ta nuna mini littafin nan Creation da aka rubuta da harshen Poland. An yi rubuce-rubuce da yawa a gefen littafin. Ta yi mamaki sosai sa’ad da na gaya mata cewa ni ne na ba kawunta littafin sa’ad da na sadu da shi a Kaunas!—M. Wa. 11:1.

Sa’ad da John Sempey ya ji cewa za ni Arewacin Ireland, ya gaya mini na ziyarci ƙanwarsa, Nellie, da yake ta nuna tana son ta koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Ni da yayata Connie muka gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Nellie ta sami ci gaba sosai kuma ta keɓe kanta ga Jehobah. Da shigewar lokaci muka soma zawarci kuma muka yi aure.

Ni da Nellie mun yi shekaru hamsin da shida muna yi wa Jehobah hidima tare, kuma muna da gatan taimaka wa mutane fiye da ɗari su sami sanin gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Mun yi bege cewa za mu yi rayuwa tare har cikin Armageddon zuwa sabuwar duniya ta Jehobah, amma mutuwa, mugun maƙiyi ta ƙwace ta a shekara ta 1998. Hakan ba ƙaramin bala’i ba ne, kuma yana ɗaya daga cikin gwaje-gwaje mafi wuya da na taɓa fuskanta a rayuwata.

Na Koma Jihohin Baltic

Misalin shekara guda bayan mutuwar Nellie, na samu albarka mai girma. An gayyace ni na ziyarci ofishin reshe da ke birnin Tallinn a ƙasar Estonia. Wasiƙar da ’yan’uwan da ke ƙasar Estonia suka rubuta, ta ce: “A cikin ’yan’uwa goma da aka tura Jihohin Baltic a tsakanin shekara 1920 da 1929 da kuma farkon shekarun 1930, kai kaɗai ne kake da rai.” Wasiƙar ta ci gaba da cewa ofishin reshe yana shirya tarihin ayyukan da aka yi a ƙasashen Estonia, Latvia, da Lithuaia, sai kuma ta ce: “Za ka iya zuwa?”

Gata ne mai girma na ba da labarin abubuwan da ni da abokan hidimata muka fuskanta a waɗannan shekaru da suka shige! A Latvia na nuna wa ’yan’uwan gida na farko da aka yi amfani da shi a matsayin ofishin reshe da kuma saman jinka inda muka ɓoye littattafanmu, da ’yan sanda ba su taɓa sani ba. A Lithuania, an kai ni wani ƙaramin gari mai suna Šiauliai, inda na yi hidima. A wani taro da aka yi a wajen, wani ɗan’uwa ya gaya mini: “Shekaru da yawa da suka shige, ni da mamata mun sayi wani gida a gari. Da muke share datti daga saman gidan, na ga littattafan nan The Divine Plan of the Ages da kuma The Harp of God. Sa’ad da na karanta su, na fahimci cewa na samu gaskiya. Mai yiwuwa kai ne ka bar waɗannan littattafai a wannan gidan shekaru da yawa da suka shige!”

Na kuma halarci taron da’ira a wani gari inda na yi hidimar majagaba. Na halarci babban taro a wajen, shekaru sattin da biyar da suka shige. A lokacin, mutane talatin da biyar ne kawai suka halarta. Amma abin farin ciki ne na ga fiye da mutane dubu da ɗari biyar da suka halarta! Babu shakka, Jehobah ya sa albarka a aikin!

‘Jehobah Bai Bar Ni Ba’

Ba da daɗewa ba na samu albarka da ban yi tsammaninsa ba sa’ad da wata ’yar’uwa Kirista mai kyau, mai suna Bee ta yarda ta zama matata. Mun yi aure a watan Nuwamba a shekara ta 2006.

Zan iya ba kowane matashi da yake tunanin abin da zai yi da rayuwarsa shawara cewa abar hikima ce sosai ya yi biyayya ga hurarrun kalmomin nan: ‘Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin ƙuruciyarka.’ Yanzu zan iya yin farin ciki, yadda mai zabura na Littafi Mai Tsarki ya yi: “Ya Allah, tun ina yaro kā koya mani; har wa yau fa ina bayyana ayyukanka masu-ban al’ajibi. I, har lokacin da na tsufa na yi furfura, kada ka yashe ni, ya Allah; sai dai na bayyana ikonka ga tsara mai-zuwa, ƙarfinka kuma ga dukan wanda ya ke zuwa.”—Zab. 71:17, 18.

[Taswira da ke shafi na 25]

(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)

Aiki mai haɗari na kai littattafai zuwa Latvia

ESTONIA

TALLINN

Gaɓar tekun Riga

LATVIA

RIGA

LITHUANIA

VILNIUS

Kaunas

[Hotunan da ke shafi na 26]

Na soma hidimar majagaba sa’ad da nake shekara goma sha biyar a Scotland

[Hotunan da ke shafi na 26]

Ni da Nellie a ranar aurenmu a shekara ta 1942

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba