Haɗin Kai na Kawo Ci Gaba na Ruhaniya
HAƊIN kai yana da muhimmanci ga waɗanda suke son su samu iyali da take ƙaunar Jehobah da kuma bauta masa. Sa’ad da Jehobah ya halicci ma’aurata na farko, ya nanata bukatar haɗin kai. Hauwa’u za ta yi aiki da Adamu a matsayin ‘mataimakiya.’ (Far. 2:18) Ya kamata aure ya zama tarayya, inda mata da miji za su tallafa wa juna. (M. Wa. 4:9-12) Cika hakkin da Jehobah ya ba iyaye da yara na bukatar haɗin kai.
Bauta ta Iyali
Barry da Heidi suna da yara biyar. Sun ga cewa yin aiki tare don su riƙa yin nazari na iyali a kai a kai na taimakonsu su samu ci gaba. Barry ya ce: “Ina ba yaran ƙananan ayyuka lokaci lokaci don nazari na iyali. Wani lokaci ina gaya musu su karanta wani talifi a Awake! kuma su gaya wa iyalin abin da suka karanta a talifin. Muna kuma gwada abin da za mu faɗa a hidimar fage don kowanne cikin yaran ya kasance a shirye ya san abin da zai faɗa. Heidi ta daɗa: “Dukanmu muna da tsarin makasudai na ruhaniya da muke son mu cim ma, kuma muna maimaita waɗannan a kai a kai a lokacin nazari na iyali don mu ga ci gaba da muke yi.” Wannan ma’aurata sun ga cewa keɓe wasu dare da ba za su kalli talabijin ba kowane mako na ba kowa zarafin yin karatu.
Taron Ikilisiya
Mike da Denise suna da yara huɗu. Yaya iyalinsu ta amfana ta wajen yin aiki tare? Mike ya ce: “A wani lokaci, ba ma yin nasara ko da yake muna tsara abubuwa da kyau, amma mun ga cewa haɗin kai na taimakonmu mu je taro a kan lokaci.” Denise ta ce: “Sa’ad da yaran suke girma, kowannensu yana da aikace-aikace da zai yi. ’Yarmu Kim, tana ba da taimako wajen dafa abinci da shirya teburin cin abincin.” Ɗansu Michael ya tuna: “Ranar Talata daddare muna taron ikilisiya a gidanmu. Mukan tsabtace ɗakin, mu share daɓen da na’urar yin shara, kuma mu jera kujerun.” Wani ɗansu da ake kira Matthew, ya daɗa: “Babanmu yana tabbata cewa ya dawo gida daga wajen aiki da wuri a duk ranar da ake taro don ya taimake mu mu yi shiri don taron.” Menene sakamakon?
Kwalliya Ce da ta Biya Kuɗin Sabulu
Mike ya ce: “A shekara ta 1987, ni da Denise muka soma hidimar majagaba. A lokacin, uku daga cikin yaranmu har ila basu bar gida ba. Biyu daga cikinsu suka zama majagaba, kuma sauran sun yi ayyukan gine-gine na Bethel. Ƙarin farin ciki ga iyalinmu shi ne cewa mun taimaki mutane arba’in su keɓe kansu kuma suka yi baftisma. Kuma a matsayin iyali mun samu gatar yin aikin gine-gine, har a wasu ƙasashe.”
Hakika, haɗin kai a iyali kwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu. Za ku iya samun ƙarin hanyoyi da za ku haɗa kai da juna a iyalinku? Ku kasance da tabbaci cewa halin haɗin kai zai taimaki iyalinku su samu ƙarin ci gaba na ruhaniya.
[Hotunan da ke shafi na 28]
Gwaji na sa a samu ci gaba a hidimar fage