Rahoto Daga Masu Shelar Mulki
Latvia ta Karɓi Bishara
LITTAFI MAI TSARKI ya nuna a bayyane cewa nufin Allah ne “dukkan [iri irin] mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.” (1 Timoti 2:4) Waɗanda aka hana su damar sauraron bishara shekaru da yawa yanzu suna saurara! A Latvia, kamar wasu ɓangarorin duniya, mutane daga dukan tsararraki da kuma al’adu suna karɓan saƙon, kamar yadda labaran da suke gaba suka nuna.
• A Rēzekne, wani gari ne a gabashin Latvia, wata mata da ’yarta budurwa suka tambayi wata mata hanya a kan titi. Bayan ta nuna musu, matar wadda ta kasance Mashaidiyar Jehovah ce, ta gayyace su zuwa taron Shaidu.
Tun da matar da ’yarta masu son addini ne, suka shawarta za su je taron. A kan hanya suka yi shawarar cewa idan suka ga wani abin da bai dace ba a wajen, za su fice babu ɓata lokaci. Amma dai, taron ya yi daɗi sosai da ba su ma yi tunanin tafiya ba. Suka yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su, kuma suka fara halartar taro a kai a kai. A cikin wata uku kawai, suka furta muradinsu na son fita aikin wa’azi kuma suna sauraron lokacin da za su yi baftisma.
• A wani birni a yammacin Latvia, wani Mashaidi ya haɗu da Anna mai shekara 85, wadda ta nuna marmari na gaske kuma ta yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. ’Yarta da danginta suka yi hamayya da ita ƙwarai. Amma Anna ba ta ƙyale wannan ba ko ma tsufanta da kuma rashin lafiyarta su hana ta ci gaba da nazarinta na Littafi Mai Tsarki ba.
Wata rana Anna ta gaya wa ’yarta za ta yi baftisma. “Idan ki ka yi baftisma, za mu aika ki gidan kula da tsofaffi,” in ji ’yar Anna. Amma dai, wannan burgar ba ta hana Anna ba. Domin yanayinta, an yi mata baftisma a gidanta.
Me ’yar Anna ta yi? Ta canja ra’ayin ta, ta dafa wa mamarta abinci na musamman bayan ta yi baftisma. Sai ta tambayi mamarta, “Yanzu da ki ka yi baftisma, yaya ki ke ji?” Me Anna ta ce? “Kamar jaririya!”
• A Disamba na 1998, Shaidu biyu suka haɗu da wani babban sojan Rasha da ya yi murabus. Tun da ya gaskata da Mahalicci, ya yarda da nazarin Littafi Mai Tsarki, matarsa ma ta shiga daga baya. Suka ci gaba sosai, ba da daɗewa ba suka zama masu shela da ba su yi baftisma ba. Da shekara ta zagayo, babban soja na dā ɗin ya yi baftisma. Ƙaunar wannan ma’aurata ta ƙwarai a abubuwan ruhaniya ta kasance abin ƙarfafa ga dukan mutane a cikin ikilisiya. Ƙari ga haka, suka ba da kansu ga aikin sake gina wani gida ya zama Majami’ar Mulki.