Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 5/15 pp. 3-5
  • “Lokacin Yin Shuru”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Lokacin Yin Shuru”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Alamar Ladabi
  • Tabbaci na Hankali da Fahimi
  • Taimako Wajen Yin Bimbini
  • Bari Furucinka Ya Kasance da Dadin Ji
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • A Wane Lokaci Ne Ya Dace Ka Yi Magana?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ka Tuna?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Kasance da Karfin Zuciya da Basira Kamar Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 5/15 pp. 3-5

“Lokacin Yin Shuru”

“YIN magana azurfa ce, yin shuru kuma zinariya ce.” In ji wani tsohon ƙarin magana da aka ce na mutanen Asiya na gabas ne. Wani ƙamus ɗin Hausa ya ce: “Kurum ta raba ka da kowa.” Kuma Sarki Sulemanu mai hikima na Isra’ila ta dā ya rubuta: “Ga kowane abu akwai nasa kwanaki, akwai lokaci kuma domin kowane abu a ƙarƙashin sama . . . lokacin shuru da lokacin magana.”—M. Wa. 3:1, 7.

Wane lokaci ne ya dace mu yi shuru maimakon yin magana? Kalmomin nan “shuru” ko kuma “yin shuru” sun bayyana a wurare da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki. Wuraren da aka yi amfani da waɗannan kalmomin sun nuna cewa ya dace a yi shuru a wurare uku na rayuwa. Bari mu bincika yadda yin shuru yake nuna ladabi, hikima da fahimi kuma taimakawa a wajen yin bimbini.

Alamar Ladabi

Yin shuru alama ce ta ladabi ko daraja. Annabi Habakkuk ya ce: “Ubangiji yana cikin haikalinsa mai-tsarki; bari dukan duniya ta yi shuru a gabansa.” (Hab. 2:20) Masu bauta ta gaskiya za su “saurari ceton Ubangiji a natse.” (Mak. 3:26) Mai zabura ya rera waƙa cewa: “Ka huta kurum cikin Ubangiji, ka yi haƙuri kana sauraronsa: Kada ka dami ranka saboda wanda ya ke albarka a cikin tafarkinsa.”—Zab. 37:7.

Za mu iya yabon Jehobah ne ba tare da yin amfani da kalmomi ba? A wasu lokatai muna mamaki sa’ad da muke kallon kyaun halitta da ba za mu iya yin magana ba. Yin tunanin irin waɗannan abubuwa masu ban al’ajabi wata hanya ce ta yabon Mahalicci a zuciyarmu, ko ba haka ba? Mai zabura Dauda ya soma wata waƙa cikin waƙoƙinsa yana cewa: “Yabo yana dakonka, ya Allah, cikin Sihiyona: A gareka kuma za a cika wa’adi.”—Zab. 65:1.

Kamar yadda Jehobah ya cancanci mu daraja shi, hakan ma kalamansa. Alal misali, sa’ad da annabin Allah Musa ya yi maganarsa na ban kwana ga al’ummar Isra’ila, shi da firistoci sun ƙarfafa dukan waɗanda suke wajen, cewa: “Ka yi shuru . . . ka ji muryar Ubangiji Allahnka fa.” Har yara Isra’ilawa suna bukatar su saurara sosai sa’ad da Isra’ilawa suka taru don su karanta Dokar Allah. Musa ya ce: ‘Ka tattara jama’a, maza da mata da ƙanana, domin su koya.’—K. Sha 27:9, 10; 31:11, 12.

Ya dace masu bauta wa Jehobah a wannan zamanin su saurari umurnin da ake ba da wa a taron Kirista har da manyan taro! Sa’ad da ake sanar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki a kan dakalin magana, za mu nuna rashin daraja ga Kalmar Allah da kuma ƙungiyarsa idan muna tattaunawa da juna, ko ba haka ba? Sa’ad da ake ba da jawabi, lokaci ne da ya kamata mu yi shuru mu saurara.

Sa’ad da mutane biyu suke magana, saurarawa da kyau yana nuna cewa mu masu ladabi ne. Alal misali, Ayuba uban iyali ya gaya wa masu zarginsa cewa: “Ku koya mani, ni ma in yi shuru.” Ayuba ya yi shuru yana saurararsu sa’ad da suke magana. Kuma sa’ad da lokaci ya kai da zai yi magana, ya ce: “Ku yi shuru: bar ni kurum, in yi magana”—Ayu. 6:24; 13:13.

Tabbaci na Hankali da Fahimi

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda ya iya ma bakinsa aikin hikima ya ke yi.” “Mutum mai-fahimi ya kan yi shuru.” (Mis. 10:19; 11:12) Ka yi la’akari da yadda Yesu ya nuna hikima da fahimi ta wajen yin shuru. Sa’ad da ya fahimci cewa yi wa magabtansa da suke ƙiyayya da shi magana ba zai kasance da amfani ba, “Yesu ya yi shuru.” (Mat. 26:63) Daga baya, sa’ad da aka kai shi gaban Bilatus, Yesu “ba ya amsa da komi ba.” Cikin hikima ya zaɓi halinsa ya yi magana.—Mat. 27:11-14.

Mu ma za mu nuna hikima idan muka yi shuru, musamman sa’ad da aka ɓata mana rai. “Mai-jinkirin fushi yana da fahimi mai-girma” in ji wani karin magana, “amma mai-garaje a rai ya kan ɗaukaka wauta.” (Mis. 14:29) Yin magana da garaje a yanayi mai wuya zai kawo baƙar magana wadda za ta iya sa a yi da na sani. A irin wannan yanayin, furcinmu zai iya shirme ga mutumin. Bayan haka muna iya yin da na sani a kan abin da ya faru, kuma hankalinmu ya ƙi kwantawa.

Za mu kasance masu hikima idan muka mai da hankali ga abubuwan da ke fita daga bakinmu sa’ad da muke gaban miyagun mutane. Sa’ad da muka sadu da masu ba’a a hidimarmu, yin shuru zai fi dacewa. Bugu da ƙari, zai fi kyau wani lokaci mu yi shuru don kada mu nuna cewa mun amince da abokan makarantarmu ko kuma abokan aiki sa’ad da suke faɗin abubuwa da ba su dace ba ko batsa. (Afis. 5:3) Mai zabura ya rubuta: “Zan rufe bakina da takunkumi, muddar mai-mugunta yana gabana.”—Zab. 39:1.

Mutum “mai-fahimi” ba ya cin amana. (Mis. 11:12) Kirista na gaskiya ba zai faɗi kalmomi na asiri ta yin magana da garaje ba. Ya kamata dattawa Kirista musamman su mai da hankali a wannan batun don waɗanda suke cikin ikilisiya su ci gaba da amincewa da su.

Ko da yake ba a furta kalmomi sa’ad da aka yi shuru, hakan yana iya kasancewa da sakamako mai kyau. Sydney Smith, marubucin Turanci na ƙarni na sha tara ya rubuta game da ɗaya daga cikin abokansa: “Yadda yake yin shuru wani lokaci yana sa maganarsa ta kasance mai ma’ana sosai.” Hakika, ya abokai biyu da suke tattaunawa da juna su ƙyale junansu su yi magana. Dole ne wanda ya iya magana ya zama mai saurarawa da kyau.

Sulemanu ya ba da gargaɗi: “A cikin yawan maganganu ba a rasa saɓo ba: amma wanda ya iya ma bakinsa aikin hikima ya ke yi.” (Mis. 10:19) Saboda haka, idan ba ma yawan magana, da kyar ne mu faɗi abin da bai dace ba. Hakika, “ko wawa, lokacinda ya kame bakinsa, a kan maishe shi mai-hikima: sa’anda ya rufe leɓunansa kuma, ana ganinsa mai-hankali ne.” (Mis. 17:28) Saboda haka, bari mu yi addu’a mu roƙi Jehobah ya ‘tsare ƙofar leɓunanmu.’—Zab. 141:3.

Taimako Wajen Yin Bimbini

Nassosi sun gaya mana game da mutumin da ke bin hanyar adalci cewa, “cikin shari’arsa [Allah] ya kan riƙa tunani dare da rana.” (Zab. 1:2) Wane yanayi ne ya fi kyau don yin irin wannan bimbini?

Ishaƙu, ɗan uban iyali Ibrahim, “ya tafi waje garin ya yi tunani cikin saura da maraice.” (Far. 24:63) Ya zaɓi lokacin da babu surutu da kuma wurin yin bimbini. Lokacin da ko’ina ya yi shuru daddare ne Sarki Dauda yake yin bimbini. (Zab. 63:6) Yesu kamiltacce ya yi iya ƙoƙarinsa don ya gamsar da bukatarsa ta kaɗaitawa da yin bimbini, ya bar inda mutane suke surutu, ya tafi kan duwatsu, hamada, da wasu wurare da babu kowa.—Mat. 14:23; Luk 4:42; 5:16.

Wurin da babu surutu yana da kyau. Yakan kawo yanayi da ya dace don mutum ya bincika kansa, wadda hakan ce za ta taimake shi ya yi gyara. Wurin da babu surutu ya kan kawo kwanciyar rai. Yin bimbini a lokacin da babu surutu zai sa mu zama masu filako da tawali’u kuma ya sa mu ƙara nuna godiya don abubuwa da suka fi muhimmanci a rayuwa.

Ko da yake yin shuru yana da kyau, da akwai “lokacin magana.” (M. Wa. 3:7) Masu bauta ta gaskiya a yau sun shagala da wa’azin bisharar Mulkin Allah “cikin iyakar duniya.” (Mat. 24:14) A sakamakon hakan, ana jin surutu na farin ciki yayin da masu bauta suke ƙaruwa. (Mi. 2:12) Ko ta yaya, bari mu kasance cikin waɗanda suke shelar bisharar Mulki da himma da kuma faɗin ayyuka masu ban al’ajabi na Allah. Sa’ad da muke yin wannan aikin mai muhimmanci, bari salon rayuwarmu ya nuna cewa muna daraja yin shuru a lokacin da ya dace.

[Hotunan da ke shafi na 3]

A lokacin taronmu na Kirista, ya kamata mu saurara kuma mu koya

[Hotunan da ke shafi na 4]

Yin shuru yana iya zama abin da ya dace ga zargi da ake yi mana a hidima

[Hotunan da ke shafi na 5]

Wurin da babu surutu ya dace don yin bimbini

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba