Ka Tuna?
Ka ji daɗin karanta Hasumiyar Tsaro na kwanan baya? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:
• Akwai begen tashi daga matattu ga jaririn da ya mutu a cikin mahaifar mamar shi?
Rayuwa tana somawa ne tun daga ciki. Jehobah yana iya ta da mutane a kowane lokaci na rayuwa domin “ga Allah abubuwa duka ya yiwu.” (Mar. 10:27) Amma Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba kai tsaye ko za a ta da jarirai da suka mutu a cikin mahaifar mamar su.—4/15, shafuffuka na 12, 13.
• Menene za mu iya koya ta wajen lura da tururuwa, rema, fari da kuma tsaka?
Waɗannan halittu huɗu sun nuna hikima sosai. Da hakan, sun ɗaukaka hikimar Allah. (Mis. 30:24-28)—4/15, shafuffuka na 16-19.
• Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce ya dace a yi shuru?
Ya nuna cewa yin shuru yana iya zama alamar ladabi, yana taimakawa wajen yin bimbini, kuma tabbaci ne na hankali da fahimi. (Zab. 37:7; 63:6; Mis. 11:12)—5/15, shafuffuka na 3-5.
• Sarakunan Yahuda nawa ne suka nuna himma na musamman don bautar Allah?
Sarakuna goma sha tara ne suka yi sarauta bisa masarautar Yahuda ta kudu, kuma guda huɗu sun yi fice don himmarsu, su ne Asa, Jehoshaphat, Hezekiya, da Yosiya.—6/15, shafuffuka na 7-11.
• Dukan Kiristoci shafaffu ne suke sa hannu wajen yin tanadin abinci na ruhaniya?
A’a. Dukan waɗanda ruhun Allah ya shafa su da ruhu suna cikin rukunin bawan nan mai aminci, mai hikima, amma waɗanda suke cikin Hukumar Mulki ne suke kula da abinci na ruhaniya.—6/15, shafuffuka na 22-24.
• Me ya sa za a ce ƙauna ce ainihin abin da ya sa Yesu ya bambanta da shugabannin addinai?
Maimakon su ƙaunaci talakawa, waɗannan shugabannin sun rena su. Bugu da ƙari, ba su ƙaunaci Allah ba. Yesu ya ƙaunaci Ubansa kuma ya yi juyayin mutanen. (Mat. 9:36) Yana da fara’a, yana da tausayi, kuma ya yi musu alheri.—7/15, shafi na 15.