Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 2/15 pp. 15-19
  • Zantattukan Yesu Suna Shafan Addu’arka Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Zantattukan Yesu Suna Shafan Addu’arka Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kada Ka Yi Addu’a Kamar Masu Riya
  • Yesu Ya Koya Mana Yadda Ake Addu’a
  • ‘Ku Roƙa, Ku Nema, Ku Ƙwanƙwasa’
  • Ka Ci Gaba da Amfana Daga Zantattukan Yesu
  • Yadda Za Mu Yi Adduꞌa—Maimaita Adduꞌar Ubangiji Ne Ya Fi?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Game da Addu’ar da Allah Yake Sauraro
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Kada Ka Yi Wasa da Gatan da Kake da Shi na Yin Addu’a
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 2/15 pp. 15-19

Zantattukan Yesu Suna Shafan Addu’arka Kuwa?

“Sa’anda Yesu ya gama waɗannan zantattuka, taron mutane suka yi mamaki da koyarwansa.”—MAT. 7:28.

1, 2. Me ya sa taron jama’a suka yi mamaki game da yadda Yesu yake koyarwa?

YA KAMATA mu amince da zantattukan Yesu Kristi, Ɗan Allah makaɗaici, kuma mu yi amfani da su a rayuwarmu. Babu ɗan adam da ya taɓa koyarwa kamarsa. Shi ya sa mutane suka yi mamaki game da yadda ya koyar a Huɗuba na kan Dutse!—Karanta Matta 7, 28, 29.

2 Ɗan Jehobah bai koya mana kamar yadda marubuta suka yi ba, waɗanda dogon jawabin da suke yi koyarwa ce ta ’yan adam ajizai. Kristi ya koyar “kamar mai-hukunci,” domin abin da yake faɗa ya fito ne daga wajen Allah. (Yoh. 12:50) Saboda haka, bari mu ga yadda zantattukan Yesu na Huɗuba a kan Dutse za su iya shafan addu’o’inmu.

Kada Ka Yi Addu’a Kamar Masu Riya

3. Ka faɗi muhimmancin kalmomin Yesu da ke rubuce a Matta 6:5.

3 Addu’a sashe ne mai muhimmanci na bauta ta gaskiya, kuma ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah a kai a kai. Amma ya kamata zantattukan Yesu a Huɗuba na kan Dutse su shafi addu’o’inmu. Ya ce: “Sa’anda ku ke yin addu’a kuma, kada ku zama kamar masu-riya: gama su suna so su tsaya su yi addu’a a cikin majami’u da ƙusurwoyin karabku, domin mutane su gan su. Gaskiya ni ke ce maku, Sun rigaya sun karɓi ladassu.”—Mat. 6:5.

4-6. (a) Me ya sa Farisawa suke son yin addu’a a tsaye a “cikin majami’u da ƙusurwoyin karabku”? (b) Ta yaya irin waɗannan masu riya “sun rigaya sun karɓi ladassu”?

4 Sa’ad da suke addu’a, almajiran Yesu ba za su yi koyi da “masu riya” kamar Farisawa masu adalcin kai ba, waɗanda suke ƙoƙarin su ruɗi mutane ta wajen nuna kamar su masu ibada ne. (Mat. 23:13-32) Waɗannan masu riya suna son su yi addu’a “su tsaya ... a cikin majami’u da ƙusurwoyin karabku.” Me ya sa? “Domin mutane su gan su.” Al’adar Yahudawa na ƙarni na farko ce su yi addu’a tare a ikilisiya a lokacin da suke miƙa hadaya ta ƙonewa a haikali a misalin ƙarfe tara na safe da kuma ƙarfe uku na rana). Mazauna Urushalima da yawa suna addu’a tare da taron jama’a masu bauta a cikin haikalin. A bayan birnin, Yahudawa masu bauta sau da yawa suna addu’a sau biyu a rana “su tsaya a cikin majami’u.”—Gwada da Luka 18:11, 13.

5 Tun da yake yawancin mutane ba sa kusa da haikalin ko kuma majami’a don addu’o’in da aka ambata ɗazu, suna iya yin addu’a a duk inda suke a lokacin. Wasu suna son lokacin addu’ar ta same su a “ƙusurwoyin karabku.” Suna son mutane da suke wucewa ta wuraren nan “su gan su.” Masu riya da suke nuna suna da ibada suna yin “addu’o’i da tsawo domin riya” don mutane da suke kallonsu su yi sha’awarsu. (Luk 20:47) Bai kamata mu kasance da irin wannan halin ba.

6 Yesu ya sanar da cewa irin waɗannan masu riya “sun rigaya sun karɓi ladassu.” Suna son a san da su kuma ’yan’uwansu mutane su yabe su, kuma abin da za su samu ke nan. Ladar da za su sami ke nan, don Jehobah ba zai amsa addu’o’insu na munafunci ba. A wata sassa kuma, Allah zai amsa addu’o’in mabiyan Kristi na gaskiya, kamar yadda furcin Yesu na gaba a kan wannan batun ya nuna.

7. Menene umurnin yin addu’a a ‘cikin lolokinmu’ yake nufi?

7 “Amma kai, lokacinda ka ke yin addu’a, shiga cikin lolokinka, bayanda ka rufe ƙofarka kuma, ka yi addu’a ga Ubanka wanda ke cikin ɓoye, Ubanka kuwa wanda ya ke gani daga cikin ɓoye za ya sāka maka.” (Mat. 6:6) Umurnin da Yesu ya ba da cewa a yi addu’a cikin ɗaki bayan an rufe ƙofa, ba ya nufin cewa mutum ba zai iya yin addu’a a madadin ikilisiya ba. Ya ba da wannan umurnin don a daina yin addu’a a fili da manufar jawo hankali ga wanda yake yin addu’ar kuma don mutane su yaba masa. Ya kamata mu tuna wannan idan muna da gatar yin addu’a a madadin mutanen Allah. Bari kuma mu bi umurnin Yesu na gaba game da addu’a.

8. In ji Matta 6:7, wace hanyar yin addu’a da ba ta dace ba ya kamata mu guje wa?

8 “Cikin yin addu’a kuma kada ku yi ta maimaitawa ta banza, kamar yadda Al’ummai su ke yi: gama suna tsammani bisa ga yawan maganarsu za a amsa masu.” (Mat. 6:7) Yesu ya ambata wata hanya da ba ta dace ba na yin addu’a, wato, maimaitawa. Ba ya nufin cewa kada mu taɓa maimaita roƙo ko kuma furci na godiya da muka yi da dukan zuciyarmu sa’ad da muke addu’a. A lambun Jathsaimani, daddare kafin ya mutu, Yesu a kai a kai “yana faɗin magana ta dā.”—Mar. 14:32-39.

9, 10. A wane azanci ne ba za mu riƙa maimaita addu’o’i ba?

9 Ba shi da kyau mu yi kwaikwayon yadda mutanen “al’ummai” suke maimaita addu’o’insu. Sau da sau suna ta “maimaitawa,” wato, kalmomi masu yawa da suka haddace da ba shi da muhimmanci. Masu bauta wa Ba’al ba su samu amfani ba ta wajen kira bisa sunan allan ƙarya “tun daga safiya har tsakar rana, suna cewa, Ya Baal, ka ji mu.” (1 Sar. 18:26) Miliyoyin mutane a yau suna maimaita addu’o’i ta wajen yawan magana, suna tsammanin cewa “za a amsa musu.” Amma Yesu ya taimake mu mu fahimci cewa ‘yawan magana’ a dogon addu’o’i da ake ta maimaitawa ba shi da amfani ga Jehobah. Yesu ya daɗa cewa:

10 “Kada ku zama kamarsu fa: gama Ubanku ya san abin da ku ke bukata, tun ba ku roƙe shi ba.” (Mat. 6:8) Shugabannin addinan Yahudawa da yawa sun mai da kansu kamar ’yan Al’umma ta wurin yawan magana sa’ad da suke yin addu’a. Addu’ar da aka yi da dukan zuciya da ta ƙunshi yabo, godiya, da roƙo sashe ne mai muhimmanci na bauta ta gaskiya. (Filib. 4:6) Amma, ba zai dace ba mu riƙa faɗin abu ɗaya sau da sau da tsammanin cewa muna bukatar maimaitawa don mu gaya wa Allah bukatunmu. Sa’ad da muke addu’a, ya kamata mu tuna cewa muna magana da wanda ‘ya san abin da muke bukata, tun ba mu roƙe shi ba.’

11. Me ya kamata mu tuna idan muna da gatar yin addu’a game da jama’a?

11 Ya kamata zantattukan Yesu game da addu’o’i da ba su dace ba su tuna mana cewa manyan furci da kuma kalmomin da ba su da amfani ba sa burge Allah. Ya kamata mu fahimci cewa addu’ar da aka yi a madadin jama’a ba lokaci ba ne na burge masu sauraro ko kuma a sa su riƙa mamakin ko yaushe za mu ce “Amin.” Yin sanarwa ko gargaɗi ga masu sauraro a cikin addu’a ba zai jitu da abin da Yesu yake nufi a zantattukansa da ke Huɗuba na kan Dutse ba.

Yesu Ya Koya Mana Yadda Ake Addu’a

12. Ta yaya za ka bayyana ma’anar roƙon nan “a tsarkake sunanka”?

12 Ko da yake Yesu ya yi gargaɗi mu guji yin addu’a yadda bai dace ba, ya koya wa almajiransa yadda ake yin addu’a. (Karanta Matta 6:9-13.) Wannan addu’ar da ya yi don koya musu bai kamata a haddace ta ba domin a riƙa maimaitawa a kai a kai. Maimakon haka, ta kafa misalin yadda za mu yi namu addu’ar. Alal misali, Yesu ya soma ambata sunan Allah sa’ad da ya soma addu’ar: “Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka.” (Mat. 6:9) Muna kiran Jehobah “Ubanmu” domin shi ne Mahaliccinmu, wanda yake zaune “cikin sama,” can nesa da duniya. (K. Sha 32:6; 2 Laba. 6:21; A. M. 17:24, 28) Yin amfani da jam’i nan “Ubanmu” ya kamata ya tuna mana cewa ’yan’uwanmu masu bi suna da dangantaka na kud da kud da Allah. “A tsarkake sunanka” roƙo ne cewa Jehobah ya aikata don ya tsarkake kansa ta wajen kawar da dukan hanyoyin da aka zargi sunansa tun tawayen da aka yi a Adnin. Sa’ad da ya amsa wannan addu’ar, Jehobah zai cire mugunta daga duniya, ta hakan ya tsarkake kansa.—Ezek. 36:23.

13. (a) Ta yaya roƙon nan “mulkinka shi zo” zai cika? (b) Menene yin nufin Allah a duniya zai ƙunsa?

13 “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Mat. 6:10) A addu’ar da Yesu ya yi a matsayin misali, ya kamata mu tuna cewa ‘mulkin’ ita ce gwamnatin Almasihu a sama a hannun Kristi da “tsarkaka” da aka ta da daga matattu da suke tare da shi. (Dan. 7:13, 14, 18; Isha. 9:6, 7) Yin addu’a mulkin ya “zo” roƙo ne cewa Mulkin Allah ya zo bisa dukan masu hamayya da sarautar Allah a duniya. Hakan zai faru ba da daɗewa ba, kuma zai buɗe hanya ga aljanna na adalci, salama, da ni’ima a dukan duniya. (Zab. 72:1-15; Dan. 2:44; 2 Bit. 3:13) Ana yin nufin Jehobah a sama, kuma addu’ar da muke yi cewa a yi nufinsa a duniya roƙo ne cewa Allah ya yi nufe-nufensa game da duniyarmu, har da cire masu hamayya da shi a yau yadda ya yi a zamanin dā.—Karanta Zabura 83:1, 2, 13-18.

14. Me ya sa ya dace mu ce a ba mu “abincin yini”?

14 “Ka ba mu yau abincin yini.” (Mat. 6:11; Luk 11:3) Sa’ad da muka yi wannan roƙo a addu’a, muna roƙon Allah ya ba mu abincin “yini.” Wannan ya nuna cewa muna da bangaskiya cewa Jehobah zai iya kula da bukatunmu na kullum. Wannan ba ya nufin cewa mu yi addu’a don mu samu tanadi mai yawa. Wannan roƙo na bukatunmu na kullum zai tuna mana cewa Allah ya umurci Isra’ilawa su tara manna, “kowace rana su tattara bukatar yini.”—Fit. 16:4.

15. Ka ba da bayanin ma’anar “gafarta mana basussuwanmu, kamar yadda mu kuma mun gafarta ma mabartanmu.”

15 Roƙo na gaba da aka yi cikin addu’ar misali ya jawo hankalinmu ga wani abu da muke bukata. Yesu ya ce: “Ka gafarta mana basussuwanmu, kamar yadda mu kuma mun gafarta ma mabartanmu.” (Mat. 6:12) Linjilar Luka ta nuna cewa waɗannan “basussuwa” ‘zunubai’ ne. (Luk 11:4) Sai mun “gafarta” wa waɗanda suke mana zunubi ne kawai Jehobah zai gafarta mana. (Karanta Matta 6:14, 15.) Ya kamata mu gafarta wa mutane da yardan rai.—Afis. 4:32; Kol. 3:13.

16. Ta yaya za mu fahimci roƙon nan game da jarraba da kuma ceto daga mugun?

16 “Kada ka kai mu cikin jaraba, amma ka cece mu daga Mugun.” (Mat. 6:13) Ta yaya za mu fahimci waɗannan roƙo biyu da ke cikin addu’ar misali na Yesu? Abu ɗaya shi ne: Jehobah ba ya gwada mu mu yi zunubi. (Karanta Yaƙub 1:13.) Shaiɗan, “mugun,” shi ne ainihi “mai-jaraba.” (Mat. 4:3) Amma, Littafi Mai Tsarki ya yi maganar Allah a matsayin mai yin abubuwan da kawai ya ƙyale. (Ruth 1:20, 21; M. Wa. 11:5) Saboda haka, “kada ka kai mu cikin jaraba” roƙo ne cewa kada Jehobah ya ƙyale mu mu faɗi sa’ad da aka jarrabe mu mu yi masa rashin biyayya. A ƙarshe, a “cece mu daga Mugun” roƙo ne cewa kada Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya sa mu tuntuɓe. Kuma muna da tabbaci cewa Allah ‘ba za ya bari a yi mana jarraba wadda ta fi ƙarfinmu ba.’—Karanta 1 Korinthiyawa 10:13.

‘Ku Roƙa, Ku Nema, Ku Ƙwanƙwasa’

17, 18. Menene ci gaba da ‘roƙo, a nema, da kuma ƙwanƙwasawa’ yake nufi?

17 Manzo Bulus ya aririci ’yan’uwa masu bi su: “Lizima cikin addu’a.” (Rom. 12:12) Yesu ya ba da irin wannan umurnin sa’ad da ya sanar: “Ku roƙa, za a ba ku; ku nema, za ku samu; ku ƙwanƙwasa, za a buɗe muku. Gama dukan wanda ya ke roƙo yana karɓa; wanda ya ke nema kuma yana samu; wanda ya ke ƙwanƙwasawa kuma za a buɗe masa.” (Mat. 7:7, 8) Ya dace mu ci gaba da ‘roƙon’ duk wani abu da ya jitu da nufin Allah. Ta wajen bin kalmomin Yesu, manzo Yohanna ya rubuta: “Gaba gaɗi ke nan da mu ke yi a gabansa [Allah], idan mun roƙi komi daidai da nufinsa, yana jinmu.”—1 Yoh. 5:14.

18 Shawarar da Yesu ya ba da na ci gaba da ‘roƙo da nema,’ tana nufin cewa ya kamata mu yi addu’a kuma kada mu daina. Yana da muhimmanci mu ci gaba da “ƙwanƙwasawa” don mu samu shiga cikin Mulkin kuma mu more albarkarsa, amfaninsa, da kuma ladansa. Amma za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Allah zai amsa addu’o’inmu? Hakika, za mu iya idan muna da aminci ga Jehobah, gama Kristi ya ce: “Dukan wanda ya ke roƙo yana karɓa; wanda ya ke nema kuma yana samu; wanda ya ke ƙwanƙwasawa kuma za a buɗe masa.” Labarin bayin Jehobah masu yawa ya nuna cewa Allah da gaske “Mai-jin addu’a” ne.—Zab. 65:2.

19, 20. Bisa kalmomin Yesu da ke rubuce a Matta 7:9-11, ta yaya Jehobah yake kama da uba mai ƙauna?

19 Yesu ya kwatanta Allah da uba mai ƙauna wanda yake tanadin abubuwa masu kyau ga ’ya’yansa. A ce kana wurin sa’ad da ya ba da Huɗuba na kan Dutse, kuma ka ji sa’ad da Yesu ya ce: “Wanene kuwa daga cikinku, kadan ɗansa ya roƙe shi dunƙulen gurasa, za ya ba shi dutse? ko kuwa kadan ya roƙi kifi, za ya ba shi maciji? Idan fa ku, da ku ke miyagu, kun sani ku bada kyautai masu-kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku wanda ke cikin sama za shi bada alherai ga waɗanda su ke roƙonsa!”—Mat. 7:9-11.

20 Uba ɗan adam, ko da yake ‘mugu’ ne domin zunubi da ya gada, yana ƙaunar ɗansa. Ba zai ruɗi ɗansa ba amma zai yi ƙoƙari ya yi masa ‘kyauta mai kyau.’ Da yake yana aikata kamar uba a gare mu, Ubanmu na samaniya mai ƙauna yana ba mu abubuwa “masu-kyau,” kamar ruhunsa mai tsarki. (Luk 11:13) Hakan zai iya ƙarfafa mu mu yi bautar da Jehobah zai amince da ita domin shi ne ba da “kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta.”—Yaƙ. 1:17.

Ka Ci Gaba da Amfana Daga Zantattukan Yesu

21, 22. Me ya sa Huɗuba a kan Dutse take da muhimmanci, kuma yaya kake ji game da waɗannan koyarwa na Yesu?

21 Hakika, Huɗuba na kan Dutse ita ce jawabi mafi kyau da aka taɓa ba da wa a duniya. Tana da ban al’ajabi don abin da ta koya mana game da Allah kuma ta fita sarai. Kamar yadda darussa da aka koya daga waɗannan talifofi suka nuna, za mu amfana sosai idan muka yi amfani da shawarar da ke cikin wannan huɗuba. Waɗannan zantattuka na Yesu za su iya kyautata rayuwarmu a yanzu kuma za su ba mu begen more rayuwa a nan gaba.

22 A waɗannan talifofi, mun bincika kaɗan kawai cikin zantattukan Yesu masu tamani a Huɗuba na kan Dutse. Ba abin mamaki ba ne da waɗanda suka saurari jawabinsa “suka yi mamaki da koyarwansa.” (Mat. 7:28) Mu ma za mu yi hakan sa’ad da muka cika zuciyarmu da waɗannan da kuma wasu zantattuka masu tamani na Babban Malami, Yesu Kristi.

Mecece Amsarka?

• Menene Yesu ya faɗa game da masu addu’a da riya?

• Me ya sa za mu guji maimaita kalmomi sa’ad da muke addu’a?

• Addu’ar misali na Yesu ta ƙunshi waɗanne roƙo?

• Ta yaya za mu ci gaba da ‘roƙo, da nema, da kuma ƙwanƙwasawa’?

[Hotunan da ke shafi na 15]

Yesu ya hukunta masu riya da suke addu’a don a gansu

[Hotunan da ke shafi na 17]

Ka san abin da ya sa ya dace mu yi addu’a don abincinmu na yini?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba