Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 2/15 pp. 19-21
  • Ya Kamata Ne Ka Nace wa Abubuwan da Ka Fi So?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ya Kamata Ne Ka Nace wa Abubuwan da Ka Fi So?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Zaɓan Aiki
  • Zaɓan Abokai
  • Sa Tufafi da Yin Ado
  • A Batutuwan Kasuwanci
  • Har a Ƙananan Abubuwa
  • Tufafinka Suna Daukaka Allah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ka Yi La’akari da Irin Kayan da Kake Sakawa da Kuma Adonka
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • “Ayyuka Masu-girma Na Allah” Sun Motsa Su
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Me Ya Sa Muke Saka Tufafin da Ya Dace Zuwa Taronmu?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 2/15 pp. 19-21

Ya Kamata Ne Ka Nace wa Abubuwan da Ka Fi So?

YARA biyu suna wasa tare. Sai ɗaya ya kwace abin wasa da ya fi so daga ɗayan kuma ya yi kururuwa, “Nawa ne!” Tun suna ƙananan yara, ’yan adam ajizai suna nuna son kai. (Far. 8:21; Rom. 3:23) Bugu da ƙari, duniya gabaki ɗaya tana ɗaukaka halin ni ne farko. Idan muna so mu guji wannan halin, dole ne mu yi ƙoƙari mu yaƙi halaye na son kai. Idan ba mu yi haka ba, za mu sa wasu su yi tuntuɓe kuma za mu raunana dangantakarmu da Jehobah.—Rom. 7:21-23.

Sa’ad da yake ƙarfafa mu mu yi la’akari da yadda abubuwan da muke yi yake shafan wasu, manzo Bulus ya rubuta: “Abu duka halal ne; amma ba dukan abu ya dace ba. Abu duka halal ne; amma ba dukan abu ne ya ke gini ba.” Bulus ya kuma daɗa: “Kada ku bada sanadin tuntuɓe.” (1 Kor. 10:23, 32) A al’amuran da suka shafi abubuwan da muke so, yana da kyau mu tambayi kanmu: ‘Ina a shirye na yi watsi da wasu abubuwa idan za su shafi salama na ikilisiya? A shirye nike na bi mizanan Littafi Mai Tsarki, ko sa’ad da yin hakan yake da wuya?’

Zaɓan Aiki

Yawancin mutane suna ganin cewa aikin da suka zaɓa bai shafi kowa ba, shawarar kansu ne. Ka yi la’akari da labarin wani ɗan kasuwa da yake wani ƙaramin gari a Amirka ta Kudu. An san cewa mashayi ne kuma yana caca. Amma, domin nazarin Littafi Mai Tsarki da ya yi da Shaidun Jehobah, ya samu ci gaba na ruhaniya kuma ya canja hanyar rayuwarsa. (2 Kor. 7:1) Sa’ad da ya faɗi cewa yana so ya soma wa’azi tare da ikilisiyar, wani dattijo cikin basira ya ƙarfafa shi ya yi tunani game da irin aikin da yake yi. Da daɗewa, mutumin ne ainihi yake sayar da ruwan rake zalla da ya yi tsami, ruwan da ake amfani da shi a yi abubuwa masu yawa, amma a wannan yankin ana haɗa shi ne da lemun kwalba don a sha a bugu.

Mutumin ya fahimci cewa idan yana wa’azi kuma yana sayar da wannan abu, hakan zai ɓata sunan ikilisiya kuma ya ɓata dangantakarsa da Allah. Ko da yake yana da babban iyali da zai kula da ita, ya daina sayar da giya. A yanzu yana kula da iyalinsa ta wajen sayar da takardu. Wannan mutumin da matarsa, da kuma biyu daga cikin yaransa biyar sun yi baftisma. Suna wa’azin bishara da himma a ko’ina da gaba gaɗi.

Zaɓan Abokai

Yin abokantaka da waɗanda ba sa bin imaninmu batun abin da muke so ne, ko kuwa hakan ya shafi mizanan Littafi Mai Tsarki? Wata ’yar’uwa tana son ta je fati da wani saurayi da ba mai bi ba ne. Ko da yake an gaya mata haɗarin da ke tattare da haka, ta ga cewa tana da ikon yin hakan kuma ta tafi wannan fatin. Ba da daɗewa ba da kai wa wurin, an ba ta abin sha da aka sa maganin barci a ciki. Da ta farka bayan sa’o’i da yawa sai ta gane cewa abokinta ɗin ya yi mata fyaɗe.—Gwada Farawa 34:2.

Ko da yake ba koyaushe ba ne yin tarayya da marasa bi yake kawo irin wannan bala’in, Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima: Amma abokin tafiyar wawaye za ya ciwutu dominsa.” (Mis. 13:20) Babu wata tantama, zaɓan mugun abokai zai jawo mana bala’i! Misalai 22:3 ta ce: “Mutum mai-hankali ya kan hangi masifa, ya ɓuya: Amma gaɓaye su kan wuce, su sha wuya.” Abokanmu suna iya shafanmu da kuma dangantakarmu da Allah.—1 Kor. 15:33; Yaƙ. 4:4.

Sa Tufafi da Yin Ado

Yin yayin kaya yana canjawa a kai a kai. Amma, mizanan Littafi Mai Tsarki game da tufafi da yin ado ba sa canjawa. Bulus ya aririci Kiristoci mata su “yafa tufafi na ladabi tare da [filako] da hankali,” wannan mizanin ya shafi maza ma. (1 Tim. 2:9) Bulus ba ya nufin sa tufafi mai araha sosai, ko kuwa dukan Kiristoci su so abu iri ɗaya. Menene filako? Wani ƙamus ya ba da ma’anar filako cewa “’yanci ne daga girman kai ... saka tufafin da ya kamata, yin magana ko ɗabi’ar da ta dace.”

Muna bukatar mu tambayi kanmu: ‘Zan iya cewa da gaske ina da sauƙin kai idan na nace yin ado a hanyar da zan jawo hankalin mutane a gare ni? Yadda nake yin ado yana sa mutane su riƙa mamaki game da irin hali na ko kuma ɗabi’a ta?’ Za mu guji “dalilin tuntuɓe cikin komi” a wannan batun idan ‘kowa ba ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula, har da ta ɗan’uwansa ma.’—2 Kor. 6:3; Filib. 2:4, Littafi Mai Tsarki.

A Batutuwan Kasuwanci

Sa’ad da batu mai muhimmanci ya taso a kan sha’anin ha’inci a cikin ikilisiyar da ke Koranti, Bulus ya rubuta: “Ba gwamma a yi haƙuri da zalunci ba?” Bulus ya gargaɗi Kiristoci su kasance a shirye su yi hasara maimakon su kai ɗan’uwansu kotu. (1 Kor. 6:1-7) Wani ɗan’uwa a Amirka ya yi amfani da wannan gargaɗin. Ya yi jayayya da shugabansa Kirista game da kuɗin da yake binsa. Ta wajen bin ƙa’idodin Nassi, ’yan’uwan sun tattauna batun sau da yawa amma ba su magance matsalar ba. A ƙarshe suka kai batun ga “ikilisiya,” da dattawa Kiristoci suke wakilta.—Mat. 18:15-17.

Abin baƙin ciki, an kasa magance matsalar. Bayan ya yi addu’a sosai, ma’aikacin ya tsai da shawarar ƙyale yawancin kuɗin da yake bi bashi. Me ya sa? Ya ce: “Jayayyar ta hana ni farin ciki kuma tana cin lokaci mai tamani da za a yi amfani da shi wajen yin ayyuka na ruhaniya.” Bayan ya tsai da wannan shawarar, ɗan’uwan ya soma farin ciki, kuma ya ga cewa Jehobah yana yi wa hidimarsa albarka.

Har a Ƙananan Abubuwa

Ƙin nace wa abin da muka fi so zai sa mu sami albarka a ƙananan batutuwa. A rana ta farko na wani taron gunduma, wani ma’aurata majagaba sun zo da wuri don su zauna a wurin da suke so. Sa’ad da aka soma taron, wata babban iyali da yara masu yawa suka shigo wurin taron da ke cike da mutane cikin hanzari. Da suka lura cewa iyalin suna neman wurin zama da ya dace, ma’auratan majagaba suka ba su wajen zamansu. Hakan ya sa dukan iyalin su zauna tare. ’Yan kwanaki bayan taron, ma’auratan suka samu wasiƙar godiya daga iyalin. Wasiƙar ta bayyana yadda suka yi sanyin gwiwa sa’ad da suka zo taron a makare. Baƙin cikinsu ba da daɗewa ta koma farin ciki da kuma godiya domin alherin da ma’auratan majagaba suka nuna.

Sa’ad da muka samu zarafi, bari mu bar abubuwa da muke so da son rai a madadin wasu. Ta wajen nuna ƙauna da “ba ta biɗa ma kanta,” muna sa salama ta kasance a cikin ikilisiya da kuma maƙwabtanmu. (1 Kor. 13:5) Amma, mafi muhimmanci, za mu ci gaba da abota da Jehobah.

[Hotunan da ke shafi na 20]

Kana shirye ka bar abubuwa da kake so sa’ad da kake zaɓan tufafi da za ka saka?

[Hotunan da ke shafi na 21]

Za ka so ka ba da wajen zamanka ga ’yan’uwanka?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba