Abin Da Muka Koya Daga Yesu
Game da Addu’ar da Allah Yake Sauraro
Sau da yawa Yesu yana neman wurin da babu kowa don ya yi addu’a, kuma ya umurci mabiyansa su yi hakan. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ananan yana addu’a a wani wuri, sa’anda ya dena, sai wani daga cikin almajiransa ya ce masa, Ubangiji, ka koya mana yin addu’a, . . . Ya ce musu, Sa’anda kuna yin addu’a, ku ce, Ya Uba, A tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo.” (Luka 5:16; 11:1, 2) Yesu ya nuna cewa ya kamata a yi addu’o’i zuwa ga Ubansa Jehobah ne kawai. Shi ne kaɗai Mahaliccinmu kuma “mai-jin addu’a.”—Zabura 65:2.
Dukan addu’o’i ne suke faranta wa Allah rai?
Maimaitawar addu’o’in da aka haddace ba sa faranta wa Allah rai. Yesu ya ce: “Cikin yin addu’a kuma kada ku yi ta maimaitawa.” (Matta 6:7) Dole ne mu yi magana da Ubanmu na samaniya daga zuciyarmu. Yesu ya bayyana wa almajiransa cewa Allah zai karɓi addu’o’in mutum mai zunubi da yake so ya tuba fiye da na mutum mai fahariya da yake kiyaye al’adun addini. (Luka 18:10-14) Saboda haka, idan muna son Allah ya saurari addu’o’inmu, sai mu yi ƙoƙarin yin abin da ya ce. Yesu ma ya ce: “Ina faɗin waɗannan magana yadda Uba ya koya mani . . . Kullum ina aika abin da ya gamshe shi.” (Yohanna 8:28, 29) A cikin addu’a Yesu ya ce: “Ba nawa nufi ba, naka za a yi.”—Luka 22:42.
Menene ya kamata mu roƙa a cikin addu’a?
Tun da an ɓata sunan Allah, Yesu ya ce: ‘Da hakanan fa za ku yi addu’a: Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Matta 6:9, 10) Ya kamata mu yi addu’a don Mulkin Allah ya zo saboda shi ne gwamnatin da Allah zai yi amfani da shi don ya cika nufinsa a sama da ƙasa. Yesu ya ce za mu iya yin addu’a don “abincin yini.” Za mu iya roƙon Jehobah ya taimake mu mu sami aiki, mafaka, sutura, da kuma wasu abubuwa da suke damunmu. Bugu da ƙari, Yesu ya ce mu roƙi addu’a don neman gafara.—Luka 11:3, 4.
Ya dace mu yi addu’a don wasu?
Yesu ya yi addu’a don wasu: “Sa’annan aka kawo masa yara ƙanƙanana domin shi ɗibiya masu hannuwansa, shi yi addu’a.” (Matta 19:13) Yesu ya ce wa manzo Bitrus: “Na yi maka addu’a kada bangaskiyarka ta kāsa.” (Luka 22:32) Yesu ya ƙarfafa mabiyansa su yi addu’a don wasu, duk da waɗanda suke tsananta musu da kuma waɗanda suke zarginsu.—Matta 5:44; Luka 6:28.
Me ya sa za mu nace da yin addu’a?
Yesu ya keɓe lokaci don ya yi addu’a kuma ya ƙarfafa mabiyansa su ‘riƙa yin addu’a, kada su suma.’ (Luka 18:1) Jehobah ya gayyace mu mu nuna amincinmu gare shi ta wurin gaya masa a kai a kai abubuwan da ke damunmu. Yesu ya ce: “Ku roƙa, za a ba ku.” Amma wannan ba ya nufin cewa Jehobah yana jin nauyin amsa waɗanda suke ƙaunarsa kuma suna daraja shi a matsayin Uba. Maimakon haka, Yesu ya ce: “Idan ku fa da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?”—Luka 11:5-13.
Don ƙarin bayani, ka dubi babi na 17 a cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?a
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.