Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 1/15 p. 30-p. 32 par. 6
  • Darussa Daga Littafin Ru’ya ta Yohanna—Sashe na Ɗaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Ru’ya ta Yohanna—Sashe na Ɗaya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “ƊAN RAGO” YA BUƊE SHIDA CIKIN HATIMAI BAKWAI
  • (R. Yoh. 1:1–7:17)
  • BUƊE HATIMI NA BAKWAI YA KAI GA BUSA ƘAHO NA BAKWAI
  • (R. Yoh. 8:1–12:17)
  • Maganar Jehobah Rayayya Ce Darussa Daga Littafin Ru’ya ta Yohanna—Sashe na Biyu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Abin da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna Ya Ce Zai Faru da Kai a Nan Gaba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Abubuwan da Ke Cikin Littafin Ruꞌuya ta Yohanna
    Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
  • Duniya Ta Zama Aljanna!
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 1/15 p. 30-p. 32 par. 6

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Littafin Ru’ya ta Yohanna—Sashe na Ɗaya

SA’AD da yake kurkuku a tsibirin Batmusa, manzo Yohanna tsoho ya sami wahayi guda sha shida. A cikinsu, ya ga abubuwan da Jehobah Allah da Yesu Kristi suka cim ma a ranar Ubangiji, lokacin da ya soma daga sa’ad da aka kafa Mulkin Allah a shekara ta 1914 zuwa ƙarshen Sarautar Kristi ta shekara Dubu. Littafin Ru’ya ta Yohanna, wanda Yohanna ya rubuta a wajen shekara ta 96 A.Z., yana ɗauke da labarai masu ban sha’awa na waɗannan wahayin.

Bari yanzu mu tattauna darussan da ke cikin Ru’ya ta Yohanna 1:1–12:17, waɗanda suka ƙunshi wahayi guda bakwai na farko da Yohanna ya karɓa. Waɗannan wahayin suna da amfani a gare mu domin suna ɗauke ne da abubuwan da ke faruwa a duniya a yanzu kuma sun nuna yadda Jehobah zai ɗauki mataki a nan gaba. Waɗanda suka karanta labarin da ke cikin waɗannan wahayin da bangaskiya za su sami ƙarfafa.—Ibran. 4:12.

“ƊAN RAGO” YA BUƊE SHIDA CIKIN HATIMAI BAKWAI

(R. Yoh. 1:1–7:17)

Na farko, Yohanna ya ga Yesu Kristi da aka ɗaukaka kuma ya karɓi saƙonni da zai ‘rubuta cikin littafi, ya aika zuwa ga ikilisiyoyin nan bakwai.’ (R. Yoh. 1:10, 11) Bayan haka, ya ga wahayi na kursiyi a sama. A hannun dama na Wanda yake zaune a kan kursiyin akwai littafin da aka hatimce da hatimai guda bakwai. Ainihin wanda ya “isa da za shi buɗe litafin” shi ne “zaki wanda shi ke na asalin kabilar Yahuda” ko kuwa “ɗan rago . . . [mai] ƙafo bakwai, da ido bakwai.”—R. Yoh. 4:2; 5:1, 2, 5, 6.

Wahayi na uku ya nuna abin da ya faru ne sa’ad da “Ɗan ragon” ya buɗe hatimai shida na farko, ɗaya bayan ɗaya. Sa’ad da ya buɗe hatimi na bakwai, babbar girgizar ƙasa ta auku kuma babbar ranar hasala ta iso. (R. Yoh. 6:1, 12, 17) Amma wahayi na gaba ya nuna ‘mala’iku huɗu suna riƙe da iskoki huɗu na duniya’ har sa’ad da aka kammala hatimce mutane 144,000. An ga “taro mai-girma” na waɗanda ba a hatimce ba “suna tsaye gaban kursiyin da gaban Ɗan ragon.”—R. Yoh. 7:1, 9.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

1:4; 3:1; 4:5; 5:6—Menene furcin nan ‘ruhohi bakwai’ yake nufi? Adadin nan bakwai yana nufin cikakke a wurin Allah. Saboda haka, saƙon da aka aika wa ‘ikilisiyoyin nan bakwai’ gabaki ɗaya yana nuni ne ga dukan mutanen Allah da suke ikilisiyoyi fiye da 100,000 a dukan duniya. (R. Yoh. 1:11, 20) Tun da yake za a ba da ruhu mai tsarki ne bisa ga abubuwan da ake son ya cim ma wa, furcin nan ‘ruhohi bakwai’ yana nufin cikakken aikinsa wajen ba da fahimi da kuma kawo albarka ga waɗanda suka mai da hankali ga annabcin. Kamar dai littafin Ru’ya ta Yohanna tana magana ne a kan abubuwa bakwai. Adadin nan bakwai a nan yana wakiltar cikakke, kuma littafin ya tattauna “cika,” ko kammala “asirin Allah.”—R. Yoh. 10:7.

1:8, 17—Wanene ke da laƙabin nan “Alpha da Omega” da kuma “na Farko da na Ƙarshe”? Laƙabin nan “Alpha da Omega” suna nuni ne ga Jehobah, kuma hakan na nanata cewa babu Allah maɗaukaki kafin shi kuma ba za a taɓa samun wani bayansa ba. Shi ne “farko da ƙarshe.” (R. Yoh. 21:6; 22:13) Ko da yake an kira Jehobah “farko da ƙarshe” a Ru’ya ta Yohanna 22:13 domin babu wani kafin shi da kuma bayansa, abin da aka faɗa a sura ta farko na Ru’ya ta Yohanna ya nuna cewa laƙabi nan “farko da ƙarshe” yana nuni ga Yesu Kristi. Shi ne ɗan adam na farko da aka ta da daga matattu zuwa rayuwa ta ruhu da ba a mutuwa kuma shi ne na ƙarshe da Jehobah da kansa ya ta da zuwa irin wannan rayuwar.—Kol. 1:18.

2:7—Menene Aljanna “na Allah” yake nufi? Tun da yake waɗannan kalaman an yi su ne ga shafaffu Kiristoci, aljannar nan tana nuni ne ga yanayi na aljanna a sama, wato, a gaban Allah. Shafaffu masu aminci za su sami sakamakon cin “itace na rai.” Za su sami rayuwa da ba a mutuwa.—1 Kor. 15:53.

3:7—A wane lokaci ne Yesu ya karɓi “maƙullin Dauda,” kuma ta yaya yake amfani da maƙullin? Sa’ad da ya yi baftisma a shekara ta 29 A.Z., Yesu ya zama Sarki Zaɓaɓɓe a zuriyar Dauda. Amma, Yesu bai karɓi maƙullin Dauda ba har sai a shekara ta 33 A.Z., sa’ad da aka ɗaukaka shi zuwa hannun dama na Allah a sama. A nan ne ya yi gadon dukan ikon Mulkin Dauda. Tun daga lokacin, Yesu yana ta yin amfani da maƙullin ya buɗe dama da gata da suka shafi Mulki. A shekara ta 1919, Yesu ya ba da ‘maƙullin gidan Dauda’ ga “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ta wajen naɗa wannan rukunin bawan “bisa dukan abin da ya ke da shi.”—Isha. 22:22; Mat. 24:45, 47.

3:12—Menene “sabon suna” na Yesu? Wannan suna ne na sabon muƙamin Yesu da kuma gatan da yake da su. (Filib. 2:9-11) Ko da yake babu wanda ya san sunan nan kamar Yesu, Yesu ya rubuta shi a kan ’yan’uwansa masu aminci da ke sama, kuma hakan ya sa sun ƙara kasancewa da dagantaka na kud da kud da shi. (R. Yoh. 19:12) Ya kuma ba su wasu daga cikin gatan da yake da shi.

Darussa Dominmu:

1:3. Domin “sa’a [ta hukuncin Allah a kan duniyar Shaiɗan] ta kusa,” ana bukatar a fahimci saƙon da ke cikin littafin Ru’ya ta Yohanna da gaggawa kuma a yi abin da ya ce.

3:17, 18. Domin mu kasance masu ruhaniya sosai, muna bukatar mu sayi “zinariya gyartaciya ta wurin wuta” daga Yesu. Wato, muna bukatar mu wadatu a ayyuka masu kyau. (1 Tim. 6:17-19) Kuma muna bukatar mu saka “fararen tufafi,” wanda ke bayyana mu a matsayin mabiyan Kristi, kuma muna bukatar mu yi amfani da “maganin ido,” kamar su shawarwarin da ake wallafawa cikin jaridar Hasumiyar Tsaro don mu sami fahimi na ruhaniya.—R. Yoh. 19:8.

7:13, 14. Dattawa 24 suna wakiltar mutane 144,000 a ɗaukakarsu ta samaniya, inda suke hidima a matsayin sarakuna da kuma firistoci. Firistocin Isra’ila na dā waɗanda Sarki Dauda ya raba gida 24 ne suke wakiltansu. Ɗaya daga cikin dattawan ne ya bayyana wa Yohanna taro mai girma. Saboda haka, an soma ta da shafaffu Kiristoci daga matattu kafin shekara ta 1935. Me ya sa? Domin a wannan shekarar ce aka bayyana wa bayin Allah shafaffu da ke duniya ma’anar taro mai girma.—Luk 22:28-30; R. Yoh. 4:4; 7:9.

BUƊE HATIMI NA BAKWAI YA KAI GA BUSA ƘAHO NA BAKWAI

(R. Yoh. 8:1–12:17)

Ɗan rago ya buɗe hatimi na bakwai. Mala’iku bakwai sun karɓi ƙaho bakwai. Shida daga cikin mala’ikun sun busa ƙahonsu, suna sanar da hukunci a kan “sulusin” duniya, wato, Kiristendom. (R. Yoh. 8:1, 2, 7-12; 9:15, 18) Wannan shi ne abin da Yohanna ya gani a wahayi na biyar. Ta wajen saka hannu a wahayi na gaba, Yohanna ya ci ɗan ƙaramin littafi kuma ya gwada mazaunin haikali. Bayan an busa ƙaho na bakwai, da manyan muryoyi an sanar cewa: “Mulkin duniya ya zama na Ubangijinmu, da na Kristinsa: za ya yi mulki kuma har zuwa zamanun zamanai.”—R. Yoh. 10:10; 11:1, 15.

Wahayi na bakwai ya faɗaɗa abin da aka faɗa a Ru’ya ta Yohanna 11:15, 17. An ga alama mai girma a sama. Mace ta samaniya ta haifi ɗa namiji. An kori Iblis daga sama. Domin ya yi fushi da macen ta samaniya, ya tafi “ya ɗaura yaƙi da sauran zuriya tata.”—R. Yoh. 12:1, 5, 9, 17.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

8:1-5—Me ya sa aka yi shuru a cikin sama, kuma menene aka zubar a duniya? An yi shuru na alama a sama domin a ji “addu’oin tsarkaka” da ke duniya. Hakan ya faru ne a ƙarshen yaƙin duniya na ɗaya. Shafaffu Kiristoci ba su koma sama ba a ƙarshen Lokuttan Al’ummai, kamar yadda yawanci suke tsammani. Sun sha wahala a lokacin yaƙin. A yanzu suna addu’a ne sosai don samun ja-gora. Ta wajen amsa addu’o’insu, mala’ikan ya jefa wuta ta alama a duniya wadda ta motsa shafaffu Kiristoci su yi aiki sosai. Ko da yake ba su da yawa, sun soma yin wa’azi a dukan duniya wanda ya mai da Mulkin Allah batun da ake yi yau da kullum, da haka, ya cinna wuta a Kiristendom. An sanar da gargaɗi daga cikin Littafi Mai Tsarki, an ƙara ba da haske na gaskiya ta Ruhaniya, kuma hakan ya girgiza tushen addinin ƙarya, kamar yadda girgizar ƙasa take girgiza gidaje.

8:6-12; 9:1, 13; 11:15—A wane lokaci ne mala’iku bakwai suka shirya busa ƙahonsu, a yaushe kuma ta yaya ne aka busa ƙahon? Shirin busa ƙahon ya haɗa da ba da umurni ga rukunin Yohanna da aka sake ƙarfafawa daga shekara ta 1919 zuwa 1922. Waɗannan shafaffun suna ta aiki tuƙuru wajen sake shirin hidimar wa’azi da kuma gina wuraren wallafa littattafai. (R. Yoh. 12:13, 14) Busa ƙahon yana nufin sanar da hukuncin Jehobah a kan duniyar Shaiɗan da mutanen Allah suke yi babu tsoro cikin haɗin kai da mala’iku. Babu shakka, hakan ya soma ne a taron gundumar da aka yi a Cedar Point, Ohio, a shekara ta 1922 kuma hakan zai kai lokacin ƙunci mai girma.

8:13; 9:12; 11:14—Ta yaya ne ƙaho uku na ƙarshe suka busa “kaito”? Ko da yake ƙaho huɗu da aka soma busawa sanarwa ce ta fallasa matacciyar yanayin Kiristendom, gudu uku na ƙarshe kaito ne domin suna magana ne game da wasu abubuwa da za su faru. Ƙaho na biyar da aka busa game da mutanen Allah ne da aka sako daga “rami mara-matuƙa” na rashin aiki a shekara ta 1919 zuwa aikin wa’azin da suke yi babu gajiya, wanda ya zama kamar annoba ga Kiristendom. (R. Yoh. 9:1) Na shida game da mahaya mafi girma a tarihi ne da kuma aikin wa’azi da ake yi a dukan duniya da ya soma a shekara ta 1922. Busa ƙaho na ƙarshe game da haihuwar Mulkin Almasihu ne.

Darussa Dominmu:

9:10, 19. Magana mai iko da aka ɗauko daga cikin Littafi Mai Tsarki da ke cikin littattafan “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” suna ɗauke da saƙo mai harbi. (Mat. 24:45) Wannan saƙon ya yi daidai da wutsiyar babe da suke da ‘ƙari’ kamar kunamai, sun kuma yi kama da dawakan yaƙi, waɗanda “wutsiyoyinsu suna kama da macizai.” Me ya sa? Domin waɗannan littattafan suna gargaɗi ne game da “ranar sakaiya ta [Jehobah].” (Isha. 61:2) Bari mu kasance da gaba gaɗi da kuma ƙwazo wajen rabar da su.

9:20, 21. Mutane da yawa masu adalci da ke zaune a ƙasashen da aka ce ba na Kiristoci ba ne sun yi na’am da saƙon da muke sanarwa sosai. Amma, ba ma sa ran cewa mutane da yawa daga cikin Kiristendom za su tuba, waɗanda aka kira “sauran mutane.” Duk da haka, muna dagewa a hidimarmu.

12:15, 16. “Ƙasa,” wato, abubuwan da ke cikin duniyar Shaiɗan, ko kuwa masu sarauta a ƙasashe dabam dabam, suna ɗaukaka damar yin bauta. Somawa daga shekara ta 1940, waɗannan masu ikon sun “shanye kogin [tsanantawa] da dragon ya zubas daga bakinsa.” Hakika, a duk lokacin da Jehobah yake son ya yi hakan, yana iya sa kowace gwamnati da ke da iko ta cim ma nufinsa. Daidai da haka, Misalai 21:1 ta ce: “Zuciyar sarki tana hannun Ubangiji kamar magudanan ruwaye: Ya kan juya ta dukan inda ya ga dama.” Ya kamata hakan ya ƙarfafa bangaskiyarmu a Allah.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba