Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • nwt pp. 409-411
  • Abubuwan da Ke Cikin Littafin Ruꞌuya ta Yohanna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abubuwan da Ke Cikin Littafin Ruꞌuya ta Yohanna
  • Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna Ta Ce Zai Faru da Maƙiyan Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Maganar Jehobah Rayayya Ce Darussa Daga Littafin Ru’ya ta Yohanna—Sashe na Biyu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
Abubuwan da Ke Cikin Littafin Ruꞌuya ta Yohanna

RUꞌUYA TA YOHANNA

ABUBUWAN DA KE CIKIN LITTAFIN NAN

  • 1

    • Ruꞌuya daga Allah, ta wurin Yesu (1-3)

    • Gaisuwa zuwa ga ikilisiyoyi bakwai (4-8)

      • “Ni ne Alfa da Omega” (8)

    • Yohanna ya sami kansa a ranar Ubangiji ta wurin ruhu mai tsarki (9-11)

    • Wahayin Yesu wanda aka ɗaukaka (12-20)

  • 2

    • Saƙonni zuwa ga Afisa (1-7), zuwa ga Simirna (8-11), zuwa ga Birgamum (12-17), zuwa ga Tayatira (18-29)

  • 3

    • Saƙonni zuwa ga Sardis (1-6), zuwa ga Filadelfiya (7-13), zuwa ga Laudikiya (14-22)

  • 4

    • Yohanna ya ga Jehobah a sama cikin wahayi (1-11)

      • Jehobah yana zaune a kujerar mulkinsa (2)

      • Dattawa ashirin da huɗu da ke zaune a kujerun mulki (4)

      • Halittu huɗu masu rai (6)

  • 5

    • Naɗaɗɗen littafi mai hatimai guda bakwai (1-5)

    • Ɗan Ragon ya ɗauki naɗaɗɗen littafin (6-8)

    • Ɗan Ragon ya cancanci ya buɗe hatiman (9-14)

  • 6

    • Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na farko zuwa na shida (1-17)

      • Mai cin nasara yana zaune a kan farin doki (1, 2)

      • Wanda yake zaune a kan jan doki ya ɗauke salama (3, 4)

      • Wanda yake zaune a kan baƙin doki ya kawo ƙarancin abinci (5, 6)

      • Sunan wanda yake zaune a kan dokin da kalarsa ta koɗe, Mutuwa ne (7, 8)

      • A ƙarƙashin bagaden akwai rayukan waɗanda aka kashe (9-11)

      • Babbar girgizar ƙasa (12-17)

  • 7

    • Malaꞌiku huɗu suna riƙe da iskoki na hallaka (1-3)

    • An hatimce mutane dubu ɗari da dubu arbaꞌin da huɗu (144,000) (4-8)

    • Taro mai girma sanye da fararen riguna (9-17)

  • 8

    • An buɗe hatimi na bakwai (1-6)

    • An busa kakaki na farko zuwa na huɗu (7-12)

    • An sanar da kaito uku (13)

  • 9

    • Kakaki na biyar (1-11)

    • Kaito ɗaya ya wuce, biyu suna zuwa (12)

    • Kakaki na shida (13-21)

  • 10

    • Wani malaꞌika mai ƙarfi riƙe da ƙaramin naɗaɗɗen littafi (1-7)

      • “Ba za a ƙara yin jinkiri ba” (6)

      • Sirri mai tsarki zai faru da gaske (7)

    • Yohanna ya ci ƙaramin naɗaɗɗen littafin (8-11)

  • 11

    • Shaidu biyun (1-13)

      • Yin annabci na kwanaki dubu ɗaya da ɗari biyu da sittin sanye da rigar makoki (3)

      • An kashe su kuma ba a binne su ba (7-10)

      • An ta da su bayan kwanaki uku da rabi (11, 12)

    • Kaito na biyu ya wuce, na uku yana zuwa (14)

    • Kakaki na bakwai (15-19)

      • Mulkin Ubangijinmu da na Kristinsa (15)

      • Za a hallaka waɗanda suke hallaka duniya (18)

  • 12

    • Matar, ɗa namiji, da babban maciji (1-6)

    • Mikaꞌilu ya yi yaƙi da babban macijin (7-12)

      • An jefa babban macijin zuwa ƙasa (9)

      • Ibilis ya san lokacin da ya rage masa kaɗan ne (12)

    • Babban macijin yana tsananta wa matar (13-17)

  • 13

    • Dabbar daji mai kawuna bakwai da take fitowa daga teku (1-10)

    • Dabbar daji mai ƙahoni biyu tana fitowa daga duniya (11-13)

    • Siffar dabbar daji mai kawuna bakwai (14, 15)

    • Alama da kuma lambar dabbar dajin (16-18)

  • 14

    • Ɗan Ragon da kuma mutane dubu ɗari da dubu arbaꞌin da huɗu (144,000) (1-5)

    • Saƙonni daga malaꞌiku uku (6-12)

      • Malaꞌika a tsakiyar sararin sama yana shelar labari mai daɗi (6, 7)

    • Masu farin ciki ne waɗanda suka mutu cikin haɗin kai da Kristi (13)

    • An yi girbin amfanin duniya sau biyu (14-20)

  • 15

    • Malaꞌiku bakwai da annoba bakwai (1-8)

      • Waƙar Musa da na Ɗan Ragon (3, 4)

  • 16

    • Kwanuka bakwai na fushin Allah (1-21)

      • An juye kwanukan a kan duniya (2), da teku (3), da koguna da maɓuɓɓugan ruwa (4-7), da rana (8, 9), da kujerar mulki na dabbar dajin (10, 11), da Yufiretis (12-16), da kuma a iska (17-21)

      • Yaƙin Allah a Armageddon (14, 16)

  • 17

    • Hukuncin da za a yi wa “Babila Babba” (1-18)

      • Babbar karuwa tana zaune a kan jar dabbar daji (1-3)

      • Dabbar dajin, ‘a dā tana nan, yanzu ba ta nan, duk da haka za ta fito daga rami marar iyakan’ (8)

      • Ƙahoni goman za su yi faɗa da Ɗan Ragon (12-14)

      • Ƙahoni goman za su tsani karuwar (16, 17)

  • 18

    • Faɗuwar “Babila Babba” (1-8)

      • “Ku fita daga cikinta mutanena” (4)

    • Makoki don faɗuwar Babila (9-19)

    • An yi farin ciki a sama don faɗuwar Babila (20)

    • Za a jefa Babila cikin teku kamar dutse (21-24)

  • 19

    • Ku yabi Jah domin hukunce-hukuncensa (1-10)

      • Auren Ɗan Ragon (7-9)

    • Mahayin farin dokin (11-16)

    • Babbar liyafar yamma ta Allah (17, 18)

    • An yi nasara a kan dabbar dajin (19-21)

  • 20

    • An ɗaure Shaiɗan na shekaru dubu ɗaya (1-3)

    • Waɗanda za su yi sarauta na shekaru dubu ɗaya tare da Kristi (4-6)

    • An sako Shaiɗan, sai aka hallaka shi (7-10)

    • An yi wa matattu shariꞌa a gaban kujerar mulki mai farin kala (11-15)

  • 21

    • Sabon sama da sabuwar duniya (1-8)

      • Ba za a ƙara mutuwa ba (4)

      • An sa dukan abubuwa su zama sabo (5)

    • An kwatanta yadda Sabuwar Urushalima take (9-27)

  • 22

    • Kogin ruwan rai (1-5)

    • Kammalawa (6-21)

      • ‘Ku zo! Ku sha ruwan rai kyauta’ (17)

      • “Ka zo, ya Ubangiji Yesu” (20)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba