Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/15 pp. 21-25
  • Kana Girmama Mutane Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Girmama Mutane Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Girmama Jehobah da Sunansa
  • Masu Kula a Ikilisiya Suna Girmama Mutane
  • Ka Daraja Ikilisiyar Jehobah da Ja-gorarta
  • Girmama Masu Kula Masu Ziyara
  • “Ku Girmama Dukan Mutane”
  • Kana A Kan Gaba Wajen Girmama ’Yan’uwa Masu Bi Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ka Girmama Wanda Ya Cancanci Girmamawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Mu Riƙa Daraja Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ku Girmama Waɗanda Suke Da Iko Bisa Kanku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/15 pp. 21-25

Kana Girmama Mutane Kuwa?

“Kuna gabatarda juna cikin bangirma.”—ROM. 12:10.

1. Menene ya zama ruwan dare gama gari a wasu wurare a duniya?

A WASU wurare a duniya, al’ada ce yara su durƙusa idan manya suna zaune, hakan zai nuna cewa suna girmama su. Ta haka, ba za su fi manyan tsayi ba. A wannan wurin kuma, rashin ladabi ne matasa su juya wa wanda ya girme su baya. Ko da yake yadda al’adu suke nuna daraja ya bambanta, irin wannan daraja tana tuna mana Dokar Musa. Hakan ya ƙunshi wannan umurni: “Za ka tashi tsaye a gaban mai-furfura, a bada girma ga fuskar dattijo, ka ji tsoron Allahnka: ni ne Ubangiji.” (Lev. 19:32) Abin baƙin ciki, a wurare da yawa rashin girmama mutane ya zama ruwan dare gama gari. Yau ana ganin rashin biyayya a ko’ina.

2. Wanene Kalmar Allah ta ce mu girmama?

2 Kalmar Allah ta ɗauki daraja mutane da muhimmanci. Ta ce mu girmama Jehobah da Yesu. (Yoh. 5:23) An kuma umurce mu mu daraja iyalinmu, ’yan’uwa masu bi da kuma wasu da ba sa cikin ikilisiya. (Rom. 12:10; Afis. 6:1, 2; 1 Bit. 2:17) Waɗanne hanyoyi ne muke nuna cewa muna girmama Jehobah? Ta yaya muke girmama, ko kuma daraja ’yan’uwanmu? Bari mu tattauna waɗannan da kuma wasu tambayoyi.

Ka Girmama Jehobah da Sunansa

3. Wace hanya ce mafi muhimmanci da za a girmama Jehobah?

3 Wata hanya mafi muhimmanci da za ka iya girmama Jehobah ita ce ka daraja sunansa yadda ya dace. Ban da haka ma, mu ‘jama’a domin sunansa’ ne. (A. M. 15:14) Abu mai daraja ne mu zama masu ɗauke da sunan Maɗaukaki Allah Jehobah. Annabi Mikah ya ce: “Dukan kabilan mutane za su yi biyayya da sunan allahnsu, mu kuwa za mu yi biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.” (Mi. 4:5) Za mu yi ‘biyayya da sunan Ubangiji Allah’ idan muka yi ƙoƙari mu yi rayuwa da za ta ɗaukaka sunan Allah kowace rana. Kamar yadda Bulus ya tuna wa Kiristoci a Roma, idan ba mu yi rayuwar da ta jitu da bisharar da muke yi ba, hakan zai sa a ‘saɓa’ wa sunan Allah, a kuma ɓata sunan.—Rom. 2:21-24.

4. Yaya ya kamata mu ɗauki gatan yin wa’azi game da Jehobah?

4 Muna kuma girmama Jehobah ta wurin aikin wa’azi. A dā, Jehobah ya gayyaci Isra’ilawa su zama shaidunsa, amma suka kasa cika hakkinsu. (Isha. 43:1-12) Sau da yawa sun juya wa Jehobah baya kuma suka “cakuni Mai-tsarki na Isra’ila.” (Zab. 78:40, 41) Daga baya, al’ummar ta rasa tagomashin Jehobah gabaki ɗaya. A yau, muna godiya ga gatan da aka ba mu na shelar bisharar Jehobah da kuma sanar da sunansa. Muna yin haka saboda muna ƙaunarsa kuma muna son a tsarkake sunansa. Sanin gaskiya game da Ubanmu na samaniya da kuma nufinsa zai sa mu mu so yin wa’azi. Za mu ji kamar manzo Bulus sa’ad da ya ce: “Ya zama mini dole; kaitona fa in ban yi wa’azin bishara ba.”—1 Kor. 9:16.

5. Ta yaya ne bangaskiya ga Jehobah take da nasaba da daraja shi?

5 Mai zabura Dauda ya ce: “Waɗanda sun san sunanka za su dogara gareka; gama ba ka yarfadda masu-nemanka ba, ya Ubangiji.” (Zab. 9:10) Idan mun san Jehobah kuma muka daraja sunansa don abin da yake wakilta, hakan zai sa mu dogara gare shi kamar yadda amintattun bayinsa na dā suka yi. Idan muka dogara kuma muka gaskata da Jehobah hakan zai nuna cewa muna daraja shi. Ka yi la’akari da yadda Kalmar Allah ta nuna cewa akwai dangantaka tsakanin dogara ga Jehobah da kuma daraja shi. Sa’ad da Isra’ila ta dā ta ƙi dogara gare shi, Jehobah ya tambayi Musa: ‘Har yaushe mutanen nan za su rena ni: har yaushe kuma za su ƙi gaskanta ni, ga kuwa dukan alamun da na aikata a wurinsu?’ (Lit. Lis. 14:11) Hakazalika, idan muka dogara ga Jehobah ya kāre mu kuma ya kiyaye mu sa’ad da muke fuskantar gwaji, hakan zai nuna cewa muna daraja shi.

6. Menene yake motsa mu mu daraja Jehobah sosai?

6 Yesu ya nuna cewa dole ne daraja Jehobah ta fito daga zuciyar mutum. Sa’ad da yake yin magana ga waɗanda bautarsu ba ta fito daga zuciyarsu ba, Yesu ya yi kaulin Jehobah yana cewa: “Wannan al’umma tana girmamana da leɓunansu; Amma zuciyarsu tana nesa da ni.” (Mat. 15:8) Daraja Jehobah za ta fito daga zuciya mai ƙaunarsa ne. (1 Yoh. 5:3) Muna kuma tuna da alkawarin Jehobah: “Waɗanda su ke girmamana, ni kuma zan girmama su.”—1 Sam. 2:30.

Masu Kula a Ikilisiya Suna Girmama Mutane

7. (a) Me ya sa ya kamata ’yan’uwa da suke da hakki suke bukatar su daraja waɗanda suke ƙarƙashinsu? (b) Ta yaya Bulus ya nuna cewa yana daraja ’yan’uwa masu bi?

7 Manzo Bulus ya aririce ’yan’uwa masu bi: “Kuna gabatarda juna cikin bangirma.” (Rom. 12:10) Ya kamata ’yan’uwa da suke da hakki a cikin ikilisiya su kafa misali na soma girmama waɗanda suke ƙarƙashinsu. A haka, ya kamata waɗanda suke da hakki da yawa su bi misalin da Bulus ya kafa. (Ka karanta 1Tasalonikawa 2:7, 8.) ’Yan’uwa da suke ikilisiyoyin da Bulus ya ziyarta sun san cewa ba zai taɓa ce su yi abin da shi da kansa ba zai so ya yi ba. Bulus ya nuna yana daraja ’yan’uwa masu bi, kuma suna daraja shi. Sa’ad da Bulus ya ce: “Ina roƙonku fa ku zama masu-koyi da ni,” mun tabbata cewa mutane da yawa sun yi koyi da Bulus saboda misalinsa mai kyau.—1 Kor. 4:16.

8. (a) A wace hanya ce mai muhimmanci Yesu ya nuna yana daraja almajiransa? (b) A yau ta yaya ne masu kula da ikilisiya za su iya yin koyi da misalin Yesu?

8 Wata hanya da ɗan’uwa zai iya daraja waɗanda suke ƙarƙashinsa ita ne idan ya gaya musu dalilin da ya sa ya ba su umurnin. Ta yin haka, yana yin koyi da Yesu. Alal misali, sa’ad da yake gaya wa almajiransa su yi addu’a don a sami ƙarin ma’aikata da za su yi girbi, Yesu ya gaya musu dalilin da ya sa ya ce hakan. Ya ce: “Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aike ma’aikata cikin girbinsa.” (Mat. 9:37, 38) Hakazalika, sa’ad da ya ce wa almajiransa ‘su yi tsaro,’ ya ba su dalilin yin haka. Ya ce: ‘Gama ba ku sani ba cikin kowace rana Ubangijinku ke zuwa.’ (Mat. 24:42) Kowane lokaci, Yesu yana gaya wa almajiransa abin da za su yi da kuma dalilin da ya sa ya kamata su yi hakan. A haka, yana daraja su. Wannan misali ne mai kyau da ya kamata Kiristoci masu kula da ikilisiya su yi koyi da shi.

Ka Daraja Ikilisiyar Jehobah da Ja-gorarta

9. Sa’ad da muka daraja dukan ikilisiyar Kirista da kuma wakilanta, wanene muke girmamawa? Ka yi bayani.

9 Don mu girmama Jehobah, dole ne mu daraja dukan ikilisiyoyi na Kirista, da kuma wakilanta. Sa’ad da muka bi umurnin Nassi da bawa mai hikima yake bayarwa, muna nuna cewa muna daraja tsarin Jehobah. A ikilisiyar Kirista a ƙarni na farko, manzo Yohanna ya ga cewa bai kamata ya amince da waɗanda ba sa daraja waɗanda aka naɗa ba. (Ka karanta 3 Yohanna 9-11.) Kalaman Yohanna sun nuna cewa wasu ba sa daraja masu kula da ikilisiya kuma ba sa bin koyarwar ikilisiya da kuma ja-gorarta. Abin farin ciki, yawancin Kiristoci ba su da irin wannan ra’ayin. Sa’ad da manzannin suke da rai, duka ’yan’uwa suna daraja waɗanda suke kula da ikilisiya.—Filib. 2:12.

10, 11. Ka bayyana daga cikin Nassi dalilin da ya sa ya dace a daraja waɗanda suke da hakki a cikin ikilisiyar Kirista.

10 Wasu sun yi tunani cewa tun da Yesu ya ce wa almajiransa “ku duka kuwa ’yan’uwa ne,” bai kamata wasu su shugabanci ikilisiyar Kirista ba. (Mat. 23:8) Amma, Nassosin Ibrananci da Helenanci suna ɗauke da misalai masu yawa na waɗanda Allah ya ba hakkin shugabanci. Tarihin ubanin iyalai, alƙalawa da kuma sarakuna a cikin Ibraniyawa na dā ya nuna cewa Jehobah yana ba da umurni ta wurin wakilansa. Sa’ad da mutanen suka ƙi daraja waɗanda Allah ya naɗa yadda ya kamata, Jehobah ya yi musu horo.—2 Sar. 1:2-17; 2:19, 23, 24.

11 Kazalika, Kiristoci na ƙarni na farko sun yarda da shugabancin manzannin. (A. M. 2:42) Alal misali, Bulus ya ba ’yan’uwansa umurni. (1 Kor. 16:1; 1 Tas. 4:2) Duk da haka, ya yi biyayya ga waɗanda yake ƙarƙashinsu. (A. M. 15:22; Gal. 2:9, 10) Hakika, Bulus ya ɗauki daraja waɗanda suke da hakki a ikilisiyar Kirista da muhimmanci.

12. Waɗanne darussa biyu ne game da shugabanci muka koya daga misalan Littafi Mai Tsarki?

12 Darassi da muka koya yana da ma’ana biyu. Na farko, bisa ga Nassi, ya dace “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ta wurin Hukumar Mulki ya naɗa maza su kasance da hakki a cikin ikilisiya, kuma ya naɗa wasu cikin mazan su shugabanci sauran mazan da aka naɗa. (Mat. 24:45-47; 1 Bit. 5:1-3) Na biyu, ya kamata dukanmu, har da maza da aka naɗa mu daraja waɗanda suke da hakkin kula da mu. Waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna cewa muna daraja waɗanda suke da hakkin kula da dukan ikilisiyar Kirista?

Girmama Masu Kula Masu Ziyara

13. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja wakilan ikilisiyar Kirista na zamanin nan?

13 Bulus ya ce: “Amma muna roƙonku ’yan’uwa, ku girmama masu fama da aiki a cikinku, wato waɗanda ke shugabanninku cikin Ubangiji, suke kuma yi muku gargaɗi. Ku riƙe su da mutunci ƙwarai game da ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.” (1 Tas. 5:12, 13; LMT) Hakika, masu kula masu ziyara suna ɗaya daga cikin waɗanda suke “fama da aiki.” Saboda haka, ya kamata mu riƙe su da “mutunci ƙwarai.” Wata hanya ɗaya da za mu iya yin haka ita ce ta yin biyayya ga umurninsu. Sa’ad da mai kula ya ba mu umurni daga bawan nan mai hikima, “hikima mai-fitowa daga bisa” za ta motsa mu mu “kasance a shirye mu yi biyayya.”—Yaƙ. 3:17; NW.

14. Ta yaya ne ikilisiya za ta iya daraja masu kula masu ziyara, kuma da wane sakamako?

14 Idan aka ce mu yi wani abu da ya bambanta da wanda muka saba yi kuma fa? A wani lokaci yin biyayya zai bukaci mu yaƙi irin wannan tunanin, “Ba ma yin haka a nan” ko kuma, “Hakan zai iya yiwuwa a wasu ikilisiyoyin amma ba ta mu ba.” Maimakon haka, mu yi ƙoƙari mu yi biyayya. Tuna cewa ikilisiyar ta Jehobah ce kuma Yesu ne shugaban ikilisiyar zai taimake mu mu yi biyayya. Idan aka karɓi umurnin da mai kula mai ziyara ya ba da da farin ciki kuma aka yi amfani da shi a ikilisiya, hakan zai nuna daraja daga cikin zuciya. Manzo Bulus ya yaba wa ’yan’uwa a Koranti don irin biyayya da suka yi ga umurnin da Titus dattijo mai ziyara ya ba da. (2 Kor. 7:13-16) A yau, mu tabbata cewa idan muka amince da umurnin da masu kula masu ziyara suke bayarwa da son rai, hakan zai sa mu sami farin ciki a aikin wa’azi da muke yi.—Ka karanta 2 Korinthiyawa 13:11.

“Ku Girmama Dukan Mutane”

15. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya girmama ’yan’uwanmu masu bi?

15 Bulus ya rubuta: “Kada ka tsauta ma dattijo, amma ka yi roƙonsa kamar uba; majiya ƙarfi kuma kamar ’yan’uwa. Dattijai mata kuma kamar uwaye; ƙanƙanana kamar ’yan’uwa mata cikin dukan tsabtar rai. Ka bada girma ga gwauraye waɗanda su ke gwaurayen gaske.” (1 Tim. 5:1-3) Hakika, Kalmar Allah ta aririce mu mu girmama dukan mutane a cikin ikilisiyar Kirista. Idan ka sami ɗan matsala da ɗan’uwa ko ’yar’uwa fa? Hakan zai hana ka ka girmama ɗan’uwan ne? Ko kuma za ka iya gyara halinka ta wurin kasancewa da halaye masu kyau na ruhaniya da ɗan’uwan yake da shi? Ya kamata waɗanda suke da hakki su daraja ’yan’uwansu kada su “nuna sarauta bisa . . . garken.” (1 Bit. 5:3) Hakika, a ikilisiyar Kirista da aka sani da nuna ƙauna ga juna, muna da zarafi masu yawa na girmama juna.—Ka karanta Yohanna 13:34, 35.

16, 17. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu daraja waɗanda muke yi wa wa’azi da waɗanda suke tsananta mana? (b) Ta yaya za mu “girmama dukan mutane”?

16 Hakika, ba waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista ba ne kawai ya kamata mu daraja ba. Bulus ya rubuta wa Kiristoci na zamaninsa: “Yayinda mu ke da dama fa, bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane.” (Gal. 6:10) Hakika, bin wannan ƙa’ida zai iya kasance da wuya idan abokan aikinmu ko kuma abokan makarantarmu suna yi mana mugunta. A irin waɗannan lokatai, ya kamata mu tuna da waɗannan kalaman: “Kada ka dami ranka saboda masu-aika mugunta.” (Zab. 37:1) Bin wannan umurnin zai taimake mu mu daraja masu tsananta mana. Hakazalika, sa’ad da muke yin wa’azi, kasancewa da tawali’u zai taimake mu mu daraja dukan mutane da “tawali’u da bangirma.” (1 Bit. 3:15; LMT) Adonmu da tufafinmu suna iya nuna cewa muna daraja waɗanda muke yi musu wa’azi.

17 Hakika, idan muna tattaunawa da ’yan’uwanmu masu bi ko marasa bi, ya kamata mu bi wannan umurnin: “Ku girmama dukan mutane. Ku ƙaunaci ’yan’uwanci. Ku yi tsoron Allah. Ku girmama sarki.”—1 Bit. 2:17.

Yaya Za Ka Amsa?

Ta yaya za mu iya nuna daraja ga:

• Jehobah?

• Dattawa na ikilisiya da masu kula masu ziyara?

• Dukan ’yan’uwa na ikilisiya?

• Dukan waɗanda muke yi wa wa’azi?

[Hoto a shafi na 23]

Kiristoci na ƙarni na farko sun daraja umurnin Hukumar Mulki

[Hoto a shafi na 24]

Dattawa a kowace ƙasa suna daraja masu kula masu ziyara, waɗanda Hukumar Mulki ta naɗa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba