Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/15 pp. 17-20
  • “Ubangiji Ƙarfina ne”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ubangiji Ƙarfina ne”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Na Koyi Gaskiya
  • Hidimar Majagaba da Kuma Albarkarta
  • An Koyar da Ni a Makarantar Gilead
  • “Ƙasa Mai Fara’a”
  • Sabon Abokin Aiki da Sabon Aiki
  • Albarka Daga Rayuwa ta Bauta wa ‘Jehobah da Ƙarfi’
  • Jehobah Ya Koyar da Ni In Yi Nufinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/15 pp. 17-20

“Ubangiji Ƙarfina ne”

Joan Coville ce ta ba da labarin

An haife ni a watan Yuli a shekara ta 1925 a Huddersfield da ke Ingila. Ni kaɗai ce iyayena suka haifa kuma ba ni da cikakkiyar lafiya. Mahaifina yakan ce, “A duk lokacin da iska ta hura ki, za ki yi rashin lafiya.” Kuma hakan ya zama da gaske.

SA’AD da nake ƙarama, shugabannin addinai suna yin addu’a sosai don zaman lafiya, amma lokacin da aka soma yaƙin duniya na biyu, suna yin addu’a don a yi nasara. Hakan ya ba ni mamaki kuma ya sa ni shakka. A lokacin ne Annie Ratcliffe Mashaidiyar Jehobah kaɗai da ke yankinmu ta zo gidanmu.

Na Koyi Gaskiya

Annie ta ba mu littafin nan Salvation kuma ta gayyaci mamata ta halarci tattaunawar Littafi Mai Tsarki da za a yi a gidansu Annie.a Mamata ta ce mu tafi tare. Har yanzu ina tuna da wannan tattaunawa na farko. Tattaunawar game da fansa ne, kuma na yi mamaki cewa bai gajiyar da ni ba ko kaɗan. An amsa yawancin tambayoyin da nake da shi. Mako na gaba kuma mun halarta. A ranar, an bayyana annabcin Yesu na alamar kwanaki na ƙarshe. Da muka tuna da yadda mugun yanayin duniya yake, nan da nan ni da mamata muka fahimci cewa mun sami gaskiya. A wannan rana ce aka gayyace mu zuwa Majami’ar Mulki.

A Majami’ar Mulki, na haɗu da wasu matasa majagaba, a cikinsu akwai Joyce Barber (yanzu ta zama Ellis), wadda har yanzu ita da mijinta Peter suna hidima a Bethel da ke Landan. Na aza kamar kowa ne yake yin hidima na majagaba. Nan da nan sai na soma yin wa’azi, ina samun awa 60 a kowace wata, ko da yake har ila ina zuwa makaranta.

Bayan watanni biyar, a ranar 11 ga Fabrairu shekara ta 1940, ni da mamata muka yi baftisma a taron da’ira a Bradford. Baba bai hana mu bin wannan addinin ba, amma bai zama Mashaidi ba. A lokacin da na yi baftisma ne aka soma wa’azi na kan titi. Na yi hakan, ina ɗauke da jakar mujalla da katuna da suke sanar da jawabi da za a yi. A wata ranar Asabar, aka ce in tsaya a wajen wani sashe na sayayya da ke cike da mutane. Har ila ina jin tsoron mutane, kuma ina jin tsoro kada ’yan makarantarmu su wuce inda nake tsaye.

A shekara ta 1940 an ga cewa ya kamata a raɓa ikilisiyarmu. Bayan da aka yi hakan, yawancin tsara na suna ɗaya ikilisiyar. Na kai kuka wajen shugaban ikilisiyarmu. Ya ce, “Idan kina son abokai matasa, ki je ki yi musu wa’azi.” Kuma na yi hakan. Ba da daɗewa ba, sai na haɗu da Elsie Noble. Ta amince da gaskiya kuma ta zama ƙawata da daɗewa.

Hidimar Majagaba da Kuma Albarkarta

Bayan da na gama makaranta, na yi wa wani akanta aiki. Amma, da na lura da farin cikin da bayi na cikakken lokaci suke yi, muradina na bauta wa Jehobah a matsayin majagaba ya ƙaru. A watan Mayu a shekara ta 1945, na yi farin cikin zama majagaba na musamman. A rana ta farko da na fita hidima, an yi ruwan sama sosai har yamma. Amma, na yi farin cikin fita wa’azi har ya sa ban damu da ruwan saman ba. Hakika, fita kowacce rana da kuma motsa jikina a bisa keke idan na fita hidima ya ba ni ƙarfin jiki sosai. Ko da yake ban taɓa wuce nauyin 42 ba, ba abin da ya hana ni yin hidima ta na majagaba. A waɗannan shekarun, na shaida cewa “Ubangiji ƙarfina ne.”—Zab. 28:7.

An kai ni wani gari da babu Shaidu don na ƙafa sabuwar ikilisiya a wurin. Da farko na yi hidima na shekara uku a Ingila da kuma shekara uku a Ireland. Sa’ad da nake hidima a Lisburn da ke Ireland, Na yi nazari da wani mutum wanda shi ne mataimakin Fasto a cocin Farostatan. Sa’ad da ya koyi gaskiya game da koyarwar Littafi Mai Tsarki, ya koya wa ikilisiyarsa sabon abin da ya koya. Wasu cikinsu suka kai ƙara wajen shugabannin cocin, sai aka ce ya bayyana dalilin da ya sa yake koya musu waɗannan abubuwa. Ya ce wai ya ga cewa hakkinsa ne na Kirista ya gaya wa garken cewa abin da ya koya musu a dā ba gaskiya ba ne. Ko da yake iyalinsa sun tsananta masa sosai, ya keɓe kansa ga Jehobah kuma ya bauta masa cikin aminci har mutuwarsa.

Na yi hidimata ta biyu a Larne da ke Ireland, na yi hakan na makonni shida ni kaɗai, tun da yake ƙawata da muke majagaba tare ta tafi taro mai jigo, Theocracy’s Increase Assembly a New York a shekara ta 1950. Wannan lokacin ya yi mini wuya sosai. Na so in je taron. Duk da haka, a cikin makonnin nan, na sami ƙarfafawa da yawa a hidima. Na haɗu da wani mutum tsoho da ya karɓi ɗaya daga cikin littattafanmu fiye da shekaru 20 da suka wuce. A shekaru da suka wuce ya karanta shi sau da yawa har ya haddace littafin. Da shi da ɗansa da ’yarsa suka amince da koyarwa Littafi Mai Tsarki.

An Koyar da Ni a Makarantar Gilead

A shekara ta 1951, tare da wasu majagaba goma a Ingila an gayyace ni zuwa makarantar Gilead aji na 17 a South Lansing da ke New York. Na yi farin cikin koyarwar Littafi Mai Tsarki da aka yi mana a waɗannan watannin. A lokacin nan ba a haɗa ’yan’uwa mata a cikin tsarin Makarantar Hidima ta Allah a ikilisiya ba, amma a Gilead an ba ’yan’uwa mata jawabi na ɗalibai da kuma rahotanni. Mun ji tsoro sosai. Har na gama jawabi na na farko, hannuna da takarda da na riƙe suna ta rawa. Malaminmu ɗan’uwa Maxwell Friend ya ce: “Kamar yadda dukan ƙwararrun masu ba da jawabi suke jin tsoro daga farko, ke kin ji tsoro har zuwa ƙarshe.” Sa’ad da muke makarantan, dukanmu mun koyi yadda za mu iya bayyana kanmu a gaban ajin. Ba da son ranmu ba, makarantar ta kawo ƙarshe, kuma an aika mu zuwa wasu ƙasashen da ba namu ba. An aika ni zuwa Thailand.

“Ƙasa Mai Fara’a”

Sa’ad da aka ce Astrid Anderson ta zama abokiyata na wa’azi a Thailand, na ɗauke ta kamar albarka ce daga wajen Jehobah. Mun yi makonni bakwai a cikin jirgin ruwa kafin mu kai ƙasar. Sa’ad da muka kai birnin tarayya Bangkok , mun ga cewa birnin wajen sayayya ne da ke cike da mutane da kuma wata ’yar hanya wadda ita ce babban hanyar birnin. A shekara ta 1952 masu shelar mulki a ƙasar ba su kai mutane 150 ba.

Sa’ad da muka fara ganin Hasumiyar Tsaro a harshen Thai, mun yi mamaki, ‘Za mu taɓa iya yin wannan yaren kuwa?’ Musamman ma yana da wuya a ambata kalmar yadda ya kamata. Alal misali, idan za a ambata kalmar nan khaù da take nufi “shinkafa” a kan ɗaga murya sannan a sauke ta, amma idan aka ambata wannan kalmar da murya mai zurfi, tana nufin “labari.” Sa’ad da muka fita hidima da farko, muna ta faman gaya wa mutane cewa, “Mun kawo muku shinkafa mai kyau” maimakon mu ce “labari mai daɗi.” Amma da kaɗan kaɗan bayan an yi mana dariya, mun koyi yaren.

Mutanen Thai suna da fara’a sosai. Shi ya sa ake kiran Thailand Ƙasa mai Fara’a. Da farko an aika mu birnin Khorat (yanzu ana kiran ta Nakhon Ratchasima), inda muka yi hidima na shekara biyu. Daga baya, an aika mu birnin Chiang Mai. Yawancin mutanen Thai ’yan addinin Buddhism ne ba su san Littafi Mai Tsarki ba. Na yi nazari da wani mai aiki a gidan waya a harshen Khorat. Mun tattauna game da Ibrahim uban iyali. Sa’ad da mutumin ya ji sunan Abraham sai ya kaɗa kansa. Ba da daɗewa ba sai na fahimci cewa ba Abraham da ya sani ba ne muke tattaunawa a kansa ba. Mutumin yana tsammanin Abraham Lincoln ne, shugaban ƙasar Amirka a dā.

Muna farin cikin koyar da mutanen Thai masu zuciyar kirki Littafi Mai Tsarki, mutanen kuma sun koya mana yadda za mu yi farin ciki ta yin rayuwa mai sauƙi. Hakan yana da muhimmanci sosai, saboda a mazauni na masu wa’azi na ƙasashen waje da ke Khorat, babu wutan lantarki ko kuma ruwan fanfo. A irin wannan aikin mun ‘fayace mu . . . yalwata mu yi fatara.’ Kamar manzo Bulus, mun fuskanci abin da ake nufi da “yin abu duka a cikin wannan da ya ke ƙarfafa” mu.—Filib. 4:12, 13.

Sabon Abokin Aiki da Sabon Aiki

A shekara ta 1945, na je ziyara a Landan. A lokacin ne na je ma’adanar kayayyakin tarihi na Britaniya tare da wasu majagaba da kuma wasu da suke hidima a Bethel. Ɗaya cikinsu shi ne Allan Coville, wanda bayan ziyarata ya je makarantar Gilead aji na 11. An aike shi zuwa Faransa sannan ya je Belgium.b Daga baya, sa’ad da nake hidima na masu wa’azi na ƙasashen waje a Thailand, ya tambaye ni ko zan aure shi, sai na yarda.

Mun yi aure a ranar 9 ga Yuli shekara ta 1955 a Brussels Belgium. Ina sha’awar zuwa Faris bayan aurena, sai Allan ya shirya cewa mako guda bayan aurenmu mu halarci babban taro a wajen. Amma, da muka kai wajen, sai aka ce Allan ya taimaka ya zama mai fassara a taron. Kowace rana, yana barin gida da sassafe, kuma ya dawo da daddare. Na je Faris bayan aurena kamar yadda nake so, amma ina ganin Allan daga nesa a kan dakalin magana. Duk da haka, na yi farin cikin ganin ana amfani da mijina don a taimaki ’yan’uwa, hakan ya nuna cewa idan muka sa Jehobah a aurenmu, za mu yi farin ciki sosai.

Aure ya kai ni sabon yankin yin wa’azi, wato, ƙasar Belguim. Abin da na sani game da Belgium shi ne cewa ƙasa ce da aka yi yaƙe-yaƙe, amma ba da daɗewa ba na fahimci cewa ainihin mutanen Belgium masu son zaman lafiya ne. Aikin wa’azi ya sa na koyi yaren Faransa da ake yi a kudancin ƙasan.

A shekara ta 1955 masu shela 4,500 ne suke Belgium. A kusan shekara 49, ni da Allan mun yi hidima a Bethel da kuma hidima na masu kula masu ziyara. A farkon shekaru biyu da rabi muna zuwa wurare a bisa keke, muna hawan duwatsu, ko ana ruwan sama ko rana. A waɗannan shekarun, mun zauna a gidaje fiye da 2,000 na ’yan’uwa Shaidu. Sau da yawa ina haɗuwa da ’yan’uwa da ba su da ƙarfin jiki amma suna bauta wa Jehobah da dukan ƙarfinsu. Misalinsu ya ƙarfafa ni kada in yi sanyin gwiwa a hidimata. A ƙarshen kowane mako da muka ziyarci wata ikilisiya, muna samun ƙarfafawa sosai. (Rom. 1:11, 12) Allan abokin aure ne na gaske. Kalaman Mai Wa’azi 4:9, 10: ta kasance gaskiya: “Gwamma biyu da ɗaya . . . Gama idan sun fāɗi, ɗaya za ya ɗaga ɗan’uwansa.”

Albarka Daga Rayuwa ta Bauta wa ‘Jehobah da Ƙarfi’

A shekaru masu yawa, ni da Allan mun fuskanci abubuwa masu ƙarfafawa a wajen taimaka wa mutane su bauta wa Jehobah. Alal misali, a shekara ta 1983 mun ziyarci wata ikilisiya da ake yin yaren Faransa a birnin Antwerp, inda muka zauna da wasu iyali da Benjamin Bandiwila wani matashi daga Zaire (yanzu dimokuraɗiyya na Kongo) ya zauna tare da su. Benjamin ya zo Belgium ne don ya shiga babban makaranta. Ya ce mana, “Ina sha’awar rayuwar da kuke yi, na sadaukar da kai ga hidimar Jehobah.” Allan ya ce: “Ka ce kana sha’awarmu; amma kana biɗan abin duniya. Ba ka tunanin cewa hakan ba gaskiya ba ne”? Wannan furcin ya sa Benjamin ya yi tunanin rayuwarsa. Da ya koma Zaire, ya soma hidima na majagaba, yanzu yana ɗaya daga cikin Kwamitin Reshe.

A shekara ta 1999, an yi mini aiki a maƙogwaro. Tun daga lokacin nauyi na ya koma 30. Ainihi ni mace ce marar ƙarfi kamar ‘tukunyar ƙasa.’ Hakika, na yi farin ciki sosai da Jehobah ya ba ni “mafificin” ƙarfi. Bayan da aka yi mini aiki, Jehobah ya ba ni ƙarfin jiki har na soma bin Allan zuwa hidima na masu kula masu ziyara. (2 Kor. 4:7) A shekara ta 2004, Allan ya yi barci bai tashi ba. Na yi kewarsa sosai, amma sanin cewa Jehobah zai tuna da shi yana ƙarfafa ni.

A yau, ina shekara 83, na yi shekara 63 a hidima na cikakken lokaci. Ina hidima har yanzu, ina yin nazarin Littafi Mai Tsarki a gida kuma ina yin amfani da zarafi a kowace rana in yi magana game da alkawuran Jehobah. Wani lokaci, ina tunani, ‘Da ban soma hidima ta majagaba a shekara ta 1945 ba, da yaya rayuwata za ta kasance?’ A dā, rashin lafiya da nake yi ya ba da dalili cewa ba zai yiwu ba in yi hidima. Na yi farin ciki da na soma hidima na majagaba sa’ad da nake matashiya. Na shaida cewa idan muka sa Jehobah farko a rayuwarmu, zai ƙarfafa mu.

[Hasiya]

a An buga littafin nan salvation a shekara ta 1939. An daina bugawa yanzu.

b Labarin rayuwar Ɗan’uwa Coville ya fito a Hasumiyar Tsaro na 15 ga Mayu shekara ta 1961.

[Hoto a shafi na 18]

Ni da Astrid Anderson abokiyar wa’azina na ƙasashen waje (a dama)

[Hoto a shafi na 18]

Ni da maigidana a hidima na masu kula masu ziyara, a shekara ta 1956

[Hoto a shafi na 20]

Ni da Allan a shekara ta 2000

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba