Hawaye a Cikin Gora
MATASHIN maguji ne. Ya rikice, yana baƙin ciki, idanunsa kuma cike da hawaye, sai ya roƙi Allahnsa Jehobah, ya nuna masa alheri kuma ya yi juyayinsa, ya ce: “Ka sa hawayena cikin gorarka.” (Zabura 56:8) Wannan mutumi Dauda ne, wanda daga baya ya zama sarkin Isra’ila. Amma mecece gorar da Dauda ya ambata kuma ta yaya Allah yake saka hawayen mu a cikinta?
Dauda ya san gora. Gora ce da ake saka ruwa, mai, ruwan anab, ko kuma man shanu a ciki. Har ila, makiyaya a hamada, kamar buzaye, suna amfani da goruna da aka yi da fatar akuya ko rago. Waɗannan goruna suna iya riƙe ruwa mai yawa, bisa ga girman dabban. An san waɗannan gorunan fata da iya riƙe ruwan sanyi har ma a lokacin zafin rana na hamada. A dā, ana rataye gorar fata a bisa jaki ko raƙumi. A yau, kana iya ganinsa a gaban babban mota!
Kalmomin Dauda masu motsa zuciya game da gora suna iya zama da ma’ana a gare mu. Ta yaya? Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Shaiɗan ne ke iko da duniya kuma yana da “hasala mai girma” a zamaninmu. A sakamakon haka, duniya tana fuskantar kaito masu tsanani. (Ru’ya ta Yohanna 12:12) Saboda haka, da mutane da yawa kamar Dauda da suke fuskantar matsaloli da suka shafi motsin zuci, hankali ko kuma wahala ta zahiri, musamman ma waɗanda suke iya ƙoƙarinsu su faranta wa Allah rai. Kana cikin waɗannan? Da gaba gaɗi, har da “kuka,” waɗannan amintattun mutane sun ci gaba da kasancewa da aminci. (Zabura 126:6) Suna iya kasancewa da tabbacin sanin cewa Ubansu na samaniya yana sane da gwajin da suke fuskanta da kuma yadda hakan ke shafan su. Yana sane da azabar da bayinsa suke sha kuma yana tuna hawayensu da wahalolinsu, wato a alamance yana saka su cikin gorarsa.