Na Fahimci Cewa RAI YANA DA TAMANI
A SAFIYA RANAR 16, GA AFRILU 2007, yayin da nake hawa na uku na benen ofishin Norris Hall na jami’ar Virginia Polytechnic Institute and State University, ko kuma Virginia Tech, an sake tuna mini cewa muna bukatar mu yi godiya kowance rana da muka kasance da rai.
Ina ofishina, ina shirin sauka bene na biyu domin in karɓi wasiƙata. Wani Farfesa ya zo ya kira ni in je ofishinsa in taimaka in gyara masa kwamfutarsa. Da za mu shiga ofishinsa muka dinga jin harɓin bindiga a hawa na biyu na benen. Da yake ba mu san abin da yake faruwa ba, muka yi hanzari muka shiga ofishin, muka kulle ƙofa, da far gaba mu jira abin da zai faru da mu. Na laɓe a wani lungu ina ta yin addu’a ga Jehobah, na roƙi ja-gorancinsa domin in fuskanci dukan wani abin da zai faru.
Sa’ad da muke jira sai na tuna da wani abin da ya faru shekara 15 da suka gabata. Ina aikin kanikanci a wani shagon da ake gyaran motoci. Sai wani ƙaramin kwano ɗauke da man fetur a hanun abokin aikina ya kama da wuta. A firgice sai ya wasa min man mai wuta a fuskata! Wutar ta ƙone ni ƙwarai da gaske, daga fuska har zuwa kirji. Sai aka kwashe ni cikin helikafta aka kai ni asibitin da ya ƙware wajen kula da ƙuna, na yi wata uku da rabi rai a hannun Allah. Bayan na yi wata biyar a asibitin, na koma gida, kuma na yi godiya domin ina cikin masu rai. Wannan abin da ya faru ya koya mani in ɗauki kowace rana da nake da rai da tamani. Ya sāke ƙarfafa ƙudurina na yi amfani da ran a hidimar wanda ya ba ni wannan rai, wato Jehobah Allah a matsayin Mashaidinsa.—Zabura 90:12; Ishaya 43:10.
Domin na ji ciwo sosai, na ƙasa aikin kanikanci, sai na koyi aikin kwamfuta kuma Virginia Tech suka ɗauke ni a aiki. Dalilin da ya sa ke nan nake Norris Hall a wannan ranar.
Da ƙarar bindigar ta ci gaba, ba mu yi tsamanin cewa harbi mafi muni a tarihin Amirka yana aukuwa a hawan benen da ke ƙarkashinmu ba. Kisan ya tsaya ne bayan mai harbin ya kashe kansa bayan da ya riga ya kashe mutane 32 da ba su ci ba su sha ba. Bayan minti 20, da fara harbin muka ji muroyin ’yan sanda. Muka kira su suka raka mu waje.
Wannan abin baƙin cikin da ya faru ya koya mani cewa rai ba shi da tabbas a duniya ta yau. (Yaƙub 4:14) Lallai yana da muhammanci mu dogara da Mai ba da rai, Jehobah Allah kuma mu ɗauki kowace rana kyauta ce mai tamani daga wajensa.—Zabura 23:4; 91:2.
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 31]
AP Photo/The Roanoke Times, Alan Kim