Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 8/1 pp. 17-21
  • Jehobah Ya Ƙidaye “Gashin Kanku”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ya Ƙidaye “Gashin Kanku”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Kada Ku Ji Tsoro”—Me Ya Sa?
  • Tamanin Gwara
  • “Kana Riƙe da Lissafin Yawan Hawayena”
  • Zama Abokin Allah na Kud da Kud
  • Mai Lura da Ya San Tamaninmu Luka 12:6, 7
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Babu Abin da Zai Iya “Raba Mu da Ƙaunar Allah”
    Ka Kusaci Jehobah
  • “Allah Ƙauna Ne”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Hakika Rayuwa Tana da Amfani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 8/1 pp. 17-21

Jehobah Ya Ƙidaye “Gashin Kanku”

“Ba kuwa ɗayarsu [gwara] da za ta mutu, ba da yardar Ubanku ba. Ai, ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake.”—MATIYU 10:29, 30.

1, 2. (a) Me ya sa Ayuba ya ji Allah ya ƙyale shi? (b) Furcin Ayuba yana nufi ne cewa ya juya wa Jehobah baya? Ka ba da bayani.

“NA YI kira gare ka, ya Allah, amma ba ka amsa mini ba, na yi addu’a kuma, amma ba ka kula da ni ba. Ka zama mugu a gare ni, da ƙarfin dantsenka ka tsananta mini.” Mutumin da ya faɗi wannan yana cikin tsananin wahala, kuma ba abin mamaki ba ne! Ya yi hasarar dukiyarsa, wani irin bala’i ya halaka ’ya’yansa, kuma a yanzu wata irin cuta mai ƙuna tana damunsa. Sunan mutumin Ayuba ne, kuma labarin wahalarsa na rubuce cikin Littafi Mai Tsarki domin amfaninmu.—Ayuba 30:20, 21.

2 Furcin Ayuba kamar dai ya juya wa Allah baya, amma ba haka ba ne. Ayuba yana magana ne daga zuciyarsa. (Ayuba 6:2, 3) Bai sani ba cewa Shaiɗan ne tushen gwajinsa, saboda haka cikin kuskure ya kammala cewa Allah ya yi watsi da shi. A wani lokaci, Ayuba ya ce wa Jehobah: “Me ya sa kake guduna? Me ya sa ka maishe ni kamar maƙiyi?”a—Ayuba 13:24.

3. Sa’ad da masifa ta faɗo, menene zai faɗo zuciyarmu?

3 A yau, bayin Jehobah da yawa suna wahala ƙwarai domin yaƙe-yaƙe, domin rikicin siyasa ko kuma tashin hankali, bala’i, tsufa, ciwo, talauci, da hani na gwamnati. Wataƙila kai ma kana fuskantar wani gwaji. Za ka yi tunani a wani lokaci cewa Jehobah yana gudunka. Ka san kalmomin Yahaya 3:16 ƙwarai: “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa.” Duk da haka, sa’ad da kake wahala kuma babu alamar sauƙi, za ka yi tunani: ‘Da gaske Allah yana ƙauna ta? Yana ganin wahala da nake ciki kuwa? Yana damuwa da ni kuwa?’

4. Wane yanayi ne ya zama dole Bulus ya jimre wa, kuma a waɗanne hanyoyi ne irin wannan yanayin zai iya shafanmu?

4 Ka yi la’akari da abin da ya faru da manzo Bulus. “Aka saka mini wata cuta, wadda ta zamar mini ƙaya, jakadan Shaiɗan, don yā riƙa wahalshe ni,” ya rubuta: “Sau uku nake roƙon Ubangiji kan wannan abu ya rabu da ni.” Jehobah ya saurari kukansa. Duk da haka, ya nuna wa Bulus cewa ba zai magance masa wannan ba ta wajen mu’ujiza. Maimakon haka, Bulus dole ne ya dogara bisa ikon Allah domin taimaka masa ya jimre da wannan “ƙaya.”b (2 Korantiyawa 12:7-9) Kamar Bulus, wataƙila kai ma kana fuskantar gwaji. Wataƙila kana mamaki, ‘Shin da yake ya bayyana babu abin da Jehobah yake yi game da gwajina ya nuna cewa bai san abin da yake damuna ba ne ko kuma dai bai damu ba ne kawai?’ Amsar a’a ce da babbar murya! Damuwar Jehobah game da bayinsa masu aminci ta bayyana cikin abin da Yesu ya gaya wa manzanninsa kafin ya zaɓe su. Bari mu ga yadda kalmominsa za su ƙarfafa mu a yau.

“Kada Ku Ji Tsoro”—Me Ya Sa?

5, 6. (a) Ta yaya Yesu ya taimaki manzanninsa kada su ji tsoron abin da ke zuwa a gaba? (b) Ta yaya Bulus ya nuna tabbaci a ƙaunar da Jehobah yake masa?

5 Manzannin sun sami iko ƙwarai daga wurin Yesu, har da “ikon fitar da baƙaƙen aljannu, su warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.” Hakika, wannan ba yana nufin cewa rayuwarsu za ta kasance marar gwaji da wahala. Akasarin haka, Yesu ya kwatanta dalla-dalla wasu abubuwa da za su faru da su. Amma kuma ya aririce su: “Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da ke da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta.”—Matiyu 10:1, 16-22, 28.

6 Domin ya taimaki manzannin su fahimci abin da ya sa bai kamata su ji tsoro ba, Yesu ya ba da misalai guda biyu. Ya gaya musu: “Ba gwara biyu ne kobo ba? Ba kuwa ɗayarsu da za ta mutu, ba da yardar Ubanku ba. Ai, ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake. Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.” (Matiyu 10:29-31) Ka lura cewa Yesu ya haɗa rashin tsoro a lokacin da aka fuskanci matsala da kasancewa da tabbaci cewa Jehobah ya damu da mu. A bayyane yake cewa manzo Bulus yana da irin wannan tabbaci. Ya rubuta: “Da ya ke Allah na goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai ba mu kome tare da shi hannu sake ba?” (Romawa 8:31, 32) Kowane irin ƙalubale kake fuskanta, ka tabbata cewa Jehobah ya damu da kai idan ka ci gaba da kasancewa da aminci a gare shi. Hakan zai bayyana ƙwarai sa’ad da muka bincika shawarar da Yesu ya bai wa manzanninsa.

Tamanin Gwara

7, 8. (a) Yaya ake ɗaukan gwarare a zamanin Yesu? (b) Me ya sa Matiyu 10:29 ta yi amfani da kalmar Helenanci na ƙanƙanci ta kwatanta “gwara”?

7 Kwatancin Yesu sun nuna yadda Jehobah ya damu da bayinsa. Da farko ku yi la’akari da batun gwara. A zamanin Yesu, ana yin abinci da gwara, amma domin suna yi wa gonaki ɓarna, ana ɗaukansu kamar ƙwari. Domin yawansu da kuma araharsu ana sayar da biyu ƙasa da naira biyar a kuɗin yau. Naira goma zai sayi gwarare biyar maimakon huɗu, ana ba da gyaran gwarar ɗaya kamar dai ba ta da wani muhimmanci!—Luka 12:6.

8 Ka yi la’akari kuma da girman wannan tsuntsuwar. In aka gwada ta da wasu tsuntsaye masu yawa, gwara da ta riƙa ma ƙanƙanuwa ce. Duk da haka, kalmar Hellenanci da aka fassara “gwara” a Matiyu 10:29 musamman tana nuni ne da ƙaramar gwara. Wataƙila Yesu yana son manzanninsa su yi tunanin tsuntsu ne mai ƙanƙanin tamani. Kamar yadda wani bincike ya nuna, “Yesu ya ambaci ƙaramar tsuntsuwa ce kuma a hakan ma ya yi amfani da ƙanƙanci!”

9. Wane darasi ne mai muhimmanci kwatancin Yesu ya koyar game da gwara?

9 Kwatanta gwara ta ba da darasi mai kyau: Abar kamar ba ta da tamani ga mutane amma tana da muhimmanci ga Jehobah Allah. Yesu ya nanata wannan gaskiyar ta wajen daɗa cewa ƙaramar gwara ‘ba ta faɗuwa ƙasa’ sai da sanin Jehobah.c Darasin a bayyane yake. Idan Jehobah Allah yana kula da ƙaramar tsuntsuwa marar tamani, hakika zai damu da wahalar ’yan adam waɗanda suka zaɓi su bauta masa!

10. Menene ma’anar furcin nan: “Gashin kanku ma duk a ƙidaye yake”?

10 Ƙari ga kwatancinsa na gwara, Yesu ya ce: “Gashin kanku ma duk a ƙidaye yake.” (Matiyu 10:30) Wannan gajeriyar magana ta nanata muhimmancin kwatancin Yesu game da gwara. Duba: Matsakaicin kan mutum yana ɗauke da ƙwayoyin gashi wajen 100,000. Kowane gashi ya yi kama da sauran, saboda haka, kamar dai babu wani ƙwaya guda da ya cancanci mu mai da masa hankali. Duk da haka, Jehobah Allah yana kula da kowane kuma ya ƙidaye shi. Tun da haka ne, akwai wani abu game da mu da Jehobah ba zai sani ba? Hakika, Jehobah ya san yadda muke ɗaiɗai. Hakika, “yakan dubi zuciya.”—1 Sama’ila 16:7.

11. Ta yaya Dauda ya furta tabbacinsa ga yadda Jehobah ya damu da shi?

11 Dauda wanda ya ga wahala, ya tabbata cewa Jehobah yana kula da shi. Ya rubuta: “Ya Ubangiji, ka jarraba ni, ka san ni. Ka san dukan abin da nake yi, tun daga can nesa ka gane dukan tunanina.” (Zabura 139:1, 2) Kai ma za ka iya tabbata cewa Jehobah ya san ka. (Irmiya 17:10) Kada ka yi saurin tunanin cewa ba ka da wani tamani da Jehobah zai lura da kai!

“Kana Riƙe da Lissafin Yawan Hawayena”

12. Ta yaya muka sani cewa Jehobah yana sane da wahalar da mutanensa suke sha?

12 Jehobah ya san kowane cikin bayinsa kuma yana sane da wahalar da suke sha. Alal misali, sa’ad da ake tirsasa wa Isra’ilawa da suke bauta, Jehobah ya gaya wa Musa: “Na ga wahalar jama’ata waɗanda ke a Masar, na kuma ji kukansu da suke yi a kan shugabanninsu. Na san wahalarsu.” (Fitowa 3:7) Tana sanyaya mana zuciya mu fahimci cewa sa’ad da muke wahala, Jehobah yana ganin abin da yake faruwa kuma yana sauraron kukanmu! Hakika wahalarmu tana damunsa.

13. Menene ya nuna cewa Jehobah da gaske yana damuwa da bayinsa?

13 Mun ƙara fahimtar yadda Jehobah yake kula da waɗanda suke yin dangantaka da shi daga yadda ya ji game da Isra’ilawa. Ko da yake wahalarsu sau da yawa domin taurin kansu ne, Ishaya ya rubuta game da Jehobah: “Cikin dukan ƙuncinsu ya ƙuntata.” (Ishaya 63:9; Litafi Mai-Tsarki) Da yake kai bawan Jehobah ne mai aminci, ka tabbata cewa sa’ad da ka ƙuntata Jehobah ma ya ƙuntata. Wannan bai motsa ka ka fuskanci wahala babu tsoro kuma ka ci gaba da yin iyaka ƙoƙarinka ka bauta masa ba?—1 Bitrus 5:6, 7.

14. A wane yanayi aka rubuta Zabura ta 56?

14 Tabbacin Sarki Dauda cewa Jehobah yana kula da shi kuma yana damuwa da shi ya bayyana a cikin Zabura ta 56, wadda Dauda ya rubuta sa’ad da yake guje wa Sarki Saul mai kisa. Dauda ya gudu zuwa Gat, amma sai ya tsorata za a kama shi sa’ad da Filistiyawa suka gane shi. Ya rubuta: “Dukan yini maƙiyana suna tasar mini, waɗanda suke faɗa da ni sun cika yawa.” Domin yana cikin haɗari, Dauda ya juya ga Jehobah. “Maƙiyana suke ta wahalshe ni dukan yini,” ya ce. “A kan kowane abu da nake yi, kullum suna ta tunanin yadda za su cuce ni!”—Zabura 56:2, 5.

15. (a) Menene Dauda yake nufi sa’ad da ya roƙi Jehobah ya lissafa hawayensa ko kuma ya rubuta su cikin littafi? (b) Sa’ad da muke fuskantar yanayi na ƙalubale, menene za mu tabbata?

15 Kamar yadda aka rubuta a Zabura ta 56:8, Dauda ya furta wannan furci mai ban sha’awa: “Ka san irin wahalar da nake sha, kana riƙe da lissafin yawan hawayena. Ashe, ba a rubuce suke a littafinka ba?” Lalle kwatanci ne na kulawar Jehobah! Sa’ad da muke wahala, muna yi wa Jehobah kuka da hawaye. Yesu kamiltaccen mutum ma ya yi haka. (Ibraniyawa 5:7) Dauda ya tabbata cewa Jehobah ya lura da shi kuma zai tuna da wahalarsa, kamar dai ya lissafa yawan hawayensa ne ko kuma ya rubuta su cikin littafi. Wataƙila ka ji cewa hawayenka lissafinsu na da yawa ko kuma za su cika shafuffukan littafi da yawa. Idan haka kake ji, zuciyarka ta sanyaya. Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbaci: “Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai, yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.”—Zabura 34:18.

Zama Abokin Allah na Kud da Kud

16, 17. (a) Ta yaya muka sani cewa Jehobah ya damu da matsalolin da mutanensa suke fuskanta? (b) Menene Jehobah ya yi ya ƙyale mutane su more dangantaka ta kusa da shi?

16 Hakikancin ƙidaye ‘gashin kanmu’ da Jehobah ya yi ya nuna mana irin Allah da muka sami gatar yi wa bauta. Ko da yake dole ne mu jira sabuwar duniya da aka yi alkawarinta domin dukan wahala da azaba su shuɗe, Jehobah yana wani abin ban sha’awa ga mutanensa a yanzu. Dauda ya rubuta: “Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, yakan koya musu alkawarinsa.”—Zabura 25:14.

17 ‘Amincewa Jehobah.’ Hakika, wannan ya wuce gaban a gwada ga mutane ajizai! Duk da haka, Jehobah ya gayyaci waɗanda suke tsoronsa su zo cikin tantinsa. (Zabura 15:1-5) Kuma menene Jehobah yake yi ga baƙinsa? Yana sanar da su alkawarinsa, in ji Dauda. Jehobah yana sanar da su sirri, yana sanar da sirrinsa ga annabawa domin su san nufe-nufensa da kuma abubuwan da za su yi domin su rayu cikin jituwa da su.—Amos 3:7.

18. Ta yaya muka sani cewa Jehobah yana so mu kasance da dangantaka ta kusa da shi?

18 Hakika, abin farin ciki ne mu sani cewa mu mutane ajizai za mu iya samun dangantaka ta kusa da Jehobah Allah Maɗaukakin Sarki. Babu shakka ya aririce mu mu yi haka. “Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku,” In ji Littafi Mai Tsarki. (Yakubu 4:8) Jehobah yana so mu kasance da dangantaka ta kusa da shi. Hakika, ya riga ya ɗauki mataki ya sa wannan dangantaka ta kasance. Hadayar fansa ta Yesu ta buɗe mana ƙofa saboda mu yi abota da Allah Mai Iko Duka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Muna ƙauna, domin shi ne ya fara ƙaunarmu.”—1 Yahaya 4:19.

19. Ta yaya jimiri zai inganta dangantakarmu da Jehobah?

19 Irin wannan dangantakar ta kusa tana inganta idan muka jimre cikin yanayi mai tsanani. Almajiri Yakubu ya rubuta: “Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da kome ba.” (Yakubu 1:4) Wane “aiki” ake cim ma wa ta wajen jimre wa wahala? Ka tuna da “ƙaya” da ke jikin Bulus. Menene jimiri ya cim ma a wannan? Bulus ya faɗi haka game da wahalarsa: “Saboda haka sai ma in ƙara yin taƙama da raunanata, domin ikon Almasihu ya zauna tare da ni. Saboda haka ina murna da raunanata, da cin mutuncin da ake mini, da shan wuya, da shan tsanani, da masifu saboda Almasihu, don sa’ad da nake rarrauna, a sa’an nan ne nake da ƙarfi.” (2 Korantiyawa 12:9, 10) Abin da Bulus ya fuskanta shi ne cewa Jehobah zai ba shi ƙarfi da yake bukata, “mafificin ikon” idan ya wajaba, saboda ya jimre. Hakan kuma ya sa ya kusaci Kristi da Jehobah Allah.—2 Korantiyawa 4:7; Filibiyawa 4:11-13.

20. Ta yaya za mu tabbata cewa Jehobah zai taimake mu kuma ya sanyaya mana zuciya sa’ad da muke fuskantar wahala?

20 Wataƙila Jehobah ya ƙyale gwajinka ya ci gaba. Idan haka ne, ka tuna alkawarinsa ga waɗanda suke tsoronsa: “Ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.” (Ibraniyawa 13:5) Za ka iya samun taimako da kuma sanyayar zuciya. Jehobah ya ƙidaye “gashin kanku.” Yana ganin jimirinku. Yana ƙuntata domin azabarku. Da gaske yana kula da ku. Kuma ba zai manta “da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa” da kuka yi ba.—Ibraniyawa 6:10.

[Hasiya]

a Dauda mai adalci da ’ya’yan Kora masu aminci ma sun yi irin wannan furci.—Zabura 10:1; 44:24.

b Littafi Mai Tsarki bai faɗi ko menene “ƙaya” da ke jikin Bulus ba. Wataƙila ciwo ne na jiki, irin su ciwon ido. Ko kuma kalmar nan “ƙaya” tana iya kasancewa manzannin ƙarya da suke ƙalubalantar manzancin Bulus da kuma hidimarsa.—2 Korantiyawa 11:6, 13-15; Galatiyawa 4:15; 6:11.

c Wasu malamai sun ce faɗuwar gwarar ƙasa ta wuce mutuwarta kawai. Sun ce a furcin asali hakan na nufin saukar tsuntsuwar ƙasa domin abinci. Idan haka ne, yana nufin cewa Allah yana lura kuma yana kula da tsuntsuwar a ayyukanta na yau da kullum, ba kawai lokacin da ta mutu ba.—Matiyu 6:26.

Ka Tuna?

• Waɗanne abubuwa ne za su iya sa mutum ya ji Allah ya yi watsi da shi?

• Wane darassi muka koya daga kwatancin Yesu na gwara da kuma ƙidaye gashin kanmu?

• Menene yake nufi da Jehobah ya “lissafa” hawayen mutum ko kuma ya rubuta shi cikin “littafi”?

• Ta yaya za mu sami ‘amincewar Jehobah’?

[Hoto a shafi na 18]

Me ya sa Jehobah bai cire “ƙaya” da take jikin Bulus ba?

[Hoto a shafi na 19]

Menene za mu koya daga kwatancin Yesu na gwara?

[Inda aka Dauko]

© J. Heidecker/VIREO

[Hoto a shafi na 21]

Ta wajen karatun Littafi Mai Tsarki a kai a kai, za mu sami tabbacin cewa Jehobah yana kula da mu ɗaiɗai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba