Manufar Talifofin Nazari
Talifofin Nazari na 1, 2 SHAFUFFUKA NA 3-11
Waɗannan talifofin guda biyu sun taimakemu mu fahimci ‘ayyukan banza’ da za su iya rinjayar mu daga bautar Jehobah. Sun nanata abubuwan da za su iya rinjayar mu, kuma sun ba mu dalilai da suka sa ya kamata mu dogara ga Jehobah a dukan abubuwa.
Talifofin Nazari na 3, 4 SHAFUFFUKA NA 12-20
Talifi na farko a cikin waɗannan talifofi ya nuna yadda Littafi Mai Tsarki yake taimakon matasa sa’ad da za su ɗauki mataki da zai shafi rayuwarsu. Na biyun ya ba matasa shawara mai ƙarfi daga Nassi game da abubuwan da ya kamata su sa a zuciya sa’ad suke shirin aure.
Talifin Nazari na 5 SHAFUFFUKA NA 21-25
Talifi na ƙarshe yana ɗauke da bayanai masu sa tunani game da littafin Mai-wa’azi. Ya nanata abubuwan da ake yi a wannan duniya da abubuwan da suke da muhimmanci a rayuwa.