Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 4/15 pp. 3-7
  • Guji ‘Ayyukan Banza’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Guji ‘Ayyukan Banza’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Ka Guji Allolin Ƙarya
  • Kada Ka Bari Sha’awa ta Jiki ta Zama Allahnka
  • Ka Mai da Hankali da Kalaman Banza
  • Yadda Za a Guji Kalaman Banza
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 4/15 pp. 3-7

Guji ‘Ayyukan Banza’

“Wauta ce a ɓatar da lokaci a kan ayyukan banza.”—MIS. 12:11, LITTAFI MAI TSARKI.

1. Ka lissafa abubuwa masu tamani da muke da su, kuma a wance hanya ce ya dace a yi amfani da su?

MU KIRISTOCI muna da abubuwa masu tamani dabam dabam. Waɗannan sun ƙunshi ƙoshin lafiya, kuzari, fahimi, ko kuma arziki. Domin muna ƙaunar Jehobah, muna farin cikin yin amfani da waɗannan abubuwa a bautarsa kuma muna yin abin da nassi ya ce: “Ka girmama Ubangiji da wadatanka.”—Mis. 3:9.

2. Wane gargaɗi ne Littafi Mai Tsarki ya yi game da ayyukan banza, kuma menene ma’anar wannan gargaɗi a zahiri?

2 Akasarin haka, Littafi Mai Tsarki ya yi maganar ayyukan banza kuma ya yi gargaɗi game da ɓata dukiyarmu wajen yin su. Game da wannan ka yi la’akari da kalmomin Misalai 12:11: “Manomin da ke aiki ƙwarai yana da isasshen abinci. Wauta ce a ɓatar da lokaci a aikin banza.” Ba shi da wuya a fahimci ma’anar wannan ƙarin magana a zahiri. Idan mutum ya ɓatar da lokacinsa da kuma kuzarinsa wajen aiki sosai, zai iya yin tanadin bukatun iyalinsa, zai iya samun ɗan kwanciyar hankali. (1 Tim. 5:8) Amma idan ya ɓata lokacinsa wajen yin aikin banza, yana nuna “wauta” wato rashin hankali da sanin ya kamata. Mai yiwuwa wannan mutumin zai sami kansa cikin bukata.

3. Ta yaya gargaɗin Littafi Mai Tsarki game da ayyukan banza ya shafi bautar mu?

3 To, idan muka yi amfani da mizanan wannan ƙarin magana ga bautarmu kuma fa? Za mu ga cewa Kirista da ya bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya da kuma bangaskiya zai mori kwanciyar hankali na gaske. Ya tabbata zai sami albarkar Allah a yanzu kuma da bege mai ƙarfi game da nan gaba. (Mat. 6:33; 1 Tim. 4:10) Amma kuma, Kirista da aikin banza ya ja hankalinsa yana saka dangantakarsa da Jehobah da kuma begensa na rai madawwami cikin haɗari. Ta yaya za mu guje wa haka? Dole ne mu fahimci abubuwa da ayyukan “banza” ne a rayuwarmu kuma mu ƙudiri aniyar guje musu.—Ka karanta Titus 2:11, 12.

4. Menene ayyukan banza?

4 To, menene ayyukan banza? Yana iya kasancewa dukan wani abu da zai janye hankalinmu daga bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Suna iya haɗawa da nishaɗi iri dabam dabam. Hakika, nishaɗi yana da muhimmanci idan aka yi sa da ka’ida. Amma idan muka ɓatar da lokaci mai yawa a kan ayyukan “nishaɗi” kuma muka ƙyale ayyukan bautarmu, to nishaɗi zai kasance aikin banza, wanda yake shafan ruhaniyarmu sosai. (M. Wa. 2:24; 4:6) Domin ya guje wa haka, Kirista yana bukatar ya daidaita al’amura, ya kula da kyau yadda yake ɓatar da lokacinsa mai tamani. (Ka karanta Kolossiyawa 4:5.) Akwai wasu ayyukan banza da suka fi nishaɗi muni ƙwarai. A cikin waɗannan sune allolin ƙarya.

Ka Guji Allolin Ƙarya

5. Ta yaya Littafi Mai Tsarki sau da yawa ya yi amfani da kalmar nan “gumaka”?

5 Abin sha’awa ne a fahimci cewa a yawancin ayoyin Littafi Mai Tsarki inda kalmar nan “gumaka” ta fito, tana nuni ne ga allolin ƙarya. Alal misali, Jehobah ya ce wa Isra’ila: “Ba za ku yi ma kanku gumaka, ba kuwa za ku gina kowace sassaƙaƙen sifa, ko umudi; ba kuwa za ku kafa kowane dutse wanda aka yi masa sifa ba a cikin ƙasarku, wanda za ku yi sujada a gabansa.” (Lev. 26:1) Sarki Dauda ya rubuta: “Gama mai-girma ne Ubangiji, abin yabo ne ƙwarai: Abin tsoro ne shi gaba da dukan alloli. Gama dukan alloli na dangogi gumaka ne kawai: Amma Ubangiji ya yi sammai.”—1 Laba. 16:25, 26.

6. Me ya sa allolin ƙarya ba su da amfani?

6 Kamar yadda Dauda ya nuna, muna kewaye da tabbacin da ya nuna girman Jehobah. (Zab. 139:14; 148:1-10) Gata ce Isra’ilawa sun yi alkawari na dangantaka da Jehobah. Wauta ce su kauce masa su bauta wa gunki da aka ƙera da kuma al’amudi. A lokacin wahala, allolinsu na ƙarya sun zama banza, saboda ba sa iya kāre kansu balle a ce masu bauta musu.—Alƙa. 10:14, 15; Isha. 46:5-7.

7, 8. Ta yaya ne ‘Dukiya’ za ta iya zama kamar allah?

7 A ƙasashe da yawa a yau, mutane har yanzu suna yi wa siffofi sujada, kuma waɗannan allolin ba su da amfani a yau kamar yadda ba su da amfani a dā. (1 Yoh. 5:21) Amma, Littafi Mai Tsarki ya kira waɗansu abubuwa alloli ban da gumaka. Alal misali, ka yi la’akari da waɗannan kalaman Yesu: “Ba wanda ke da iko shi bauta ma ubangiji biyu: gama ko shi ƙi ɗayan, shi ƙaunaci ɗayan: ko kuwa shi lizimci ɗayan, shi rena ɗayan. Ba ku da iko ku bauta ma Allah da [dukiya] ba.”—Mat. 6:24.

8 Yaya ne ‘Dukiya’ za ta iya zama kamar alla? Alal misali, ka yi tunanin dutsen da ke fage a ƙasar Isra’ila ta dā. Za a iya amfani da wannan dutse a gina gida ko kuma ganuwa. A wani ɓangare kuma, idan aka yi amfani da shi aka gina ‘al’amudi,’ ko kuma ‘siffa,’ sai ya kasance cikas ga mutanen Jehobah. (Lev. 26:1) Hakazalika, kuɗi suna da amfani. Muna bukatarsu don mu rayu, kuma muna iya yin amfani da su da kyau a hidimar Jehobah. (M. Wa. 7:12; Luk 16:9) Amma idan muka sa neman kuɗi gaba da hidimarmu ta Kirista, kuɗi za su zama allahnmu. (Ka karanta 1 Timothawus 6:9, 10.) A wannan duniya, da neman kuɗi yake da muhimmanci ga mutane, dole ne mu kasance da ra’ayin da ya dace game da wannan batun.—1 Tim. 6:17-19.

9, 10. (a) Yaya ne Kirista yake ɗaukan ilimi? (b) Wane hadari ne ƙarin ilimi yake kawo?

9 Wani abu mai muhimmanci da zai iya kasancewa abu marar amfani shi ne ilimi. Muna son yaranmu su sami ilimi don su biya bukatarsu a rayuwa. Abu mafi muhimmanci shi ne, Kirista da ke da ilimi sosai zai iya karanta Littafi Mai Tsarki da fahimi, banda wata matsala, ya amince, kuma ya koyar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki sosai don ya motsa zuciyar mutane. Samun ilimi yana ɗaukan lokaci, amma yana da muhimmanci.

10 Ƙarin ilimi da ake samu a kwaleji ko kuma jami’a fa? Ana ɗaukan wannan abu ne mai muhimmanci domin a yi nasara. Duk da haka, mutane da yawa da suka biɗi irin wannan ilimi a ƙarshe sai a cika zuciyarsu da hikima ta duniya. Irin wannan ilimi yakan lalata shekaru masu muhimmanci na ƙuruciya da za a iya yin amfani da su a hidimar Jehobah. (M. Wa. 12:1) Ba abin mamaki ba ne a ƙasashen da mutane da yawa suke da irin wannan ilimin, mutane da yawa ba su yarda da Allah ba. Maimakon mu dogara ga ilimi na wannan zamani don mu sami kāriya, ya kamata Kiristoci su dogara ga Jehobah.—Mis. 3:5.

Kada Ka Bari Sha’awa ta Jiki ta Zama Allahnka

11, 12. Me ya sa Bulus ya ce da wasu: ‘Allahnsu cikinsu ne’?

11 A wasiƙarsa zuwa ga Filibbiyawa, manzo Bulus ya ambata wani abu da zai iya zama allah. Ya yi magana game da wasu ’yan’uwa ya ce: ‘Mutane dayawa suna tafiya, na kuwa faɗa maku labarinsu dayawa, ina kuwa faɗa maku yanzu har da hawaye, maƙiyan gicciyen Kristi ne: waɗannan ƙarshensu halaka ne, allahnsu ciki ne, . . . suna tattalin alamuran duniya.’ (Filib. 3:18, 19) Ta yaya ne cikin mutum zai iya zama allahnsa?

12 Wataƙila ga abokanan Bulus, sha’awa ta jiki ta zama abu mafi muhimmanci fiye da su bauta wa Jehobah tare da Bulus. Wataƙila wasu sun zama masu zarin ci ko kuma masu maye. (Mis. 23:20, 21; ka gwada da Kubawar Shari’a 21:18-21.) Wasu kuma ƙila sun yi amfani da zarafin da suke da shi a duniya a ƙarni na farko kuma hakan ya rinjaye su daga hidimar Jehobah. Kada mu bari sha’awar rayuwa da ake gani wai tana da kyau ta sa mu yi sanyin gwiwa a hidimarmu ta Jehobah da muke yi da zuciya ɗaya.—Kol. 3:23, 24.

13. (a) Menene kwaɗayi, kuma yaya Bulus ya kwatanta shi? (b) Ta yaya za mu iya guje wa kwaɗayi?

13 Bulus kuma ya ambaci wani bangare na bauta ta ƙarya. Ya rubuta: “Saboda haka sai ku kashe zukatanku ga sha’awace-sha’awacen duniya, wato fasikanci, da aikin lalata, da muguwar sha’awa, da mummunan buri, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.” (Kol. 3:5; Littafi Mai Tsarki.) Kwaɗayi sha’awa ne mai ƙarfi na abin da ba mu da shi. Wataƙila na abin duniya. Wannan zai iya haɗawa da sha’awar jima’i. (Fit. 20:17) Fahimtar cewa irin wannan sha’awa daidai take da bautar gumaka, ya kamata ya sa mu yi tunani. Yesu ya yi amfani da kwatanci don ya nuna muhimmancin kame kai daga irin wannan muguwar sha’awar.—Ka karanta Markus 9:47; 1 Yohanna 2:16.

Ka Mai da Hankali da Kalaman Banza

14, 15. (a) Wane “aikin wofi” ne ya sa mutane na zamanin Irmiya suka yi zunubi? (b) Me ya sa kalaman Musa suna da amfani?

14 Abubuwan banza suna iya haɗawa da kalamai. Alal misali, Jehobah ya ce wa Irmiya: ‘Annabawa suna annabcin ƙarya da sunana: ban aike su ba, ban kuwa umurce su ba, ban kuwa yi masu magana ba: suna yi maku annabci da ru’ya ta ƙarya, da dubawa, da aikin wofi, da ruɗamin zuciyassu.’ (Irm. 14:14) Waɗannan annabawan ƙarya suna da’awar cewa suna magana cikin sunan Jehobah ne, amma suna ɗaukaka ra’ayinsu ne da kuma hikimarsu. Duk da haka, kalamansu sun zama “wofi.” Ba su da amfani kuma haɗari ne ga ruhaniya. A shekara ta 607 K.Z., mutane da yawa waɗanda suka maida hankali ga kalaman banza sun mutu a hannun sojojin Babila tun lokacinsu bai kai ba.

15 Akasin haka, Musa ya ce wa Isra’ilawa: “Ku ƙallafa zuciyarku a kan dukan zantattukan da na shaida muku yau; . . . Gama ba abin banza ya ke a gareku ba: gama ranku ne, ta wurin wannan abu kuma za ku tsawanta kwanakinku a cikin ƙasan, wadda ku ke ƙetaren Urdun garin ku ci mulkinta.” (K. Sha 32:46, 47) Hakika, kalaman Musa hurarru ne daga Allah. Saboda haka, suna da amfani, hakika da muhimmanci ƙwarai don rayuwar al’umma. Waɗanda suka yi biyayya da su, sun more tsawo rai da wadata. Bari mu ci gaba da guje wa kalaman banza kuma mu manne wa kalaman gaskiya masu amfani.

16. Yaya muke ɗaukan furcin ’yan kimiyya da suka saɓawa Kalmar Allah?

16 A yau muna ji ana furta kalaman banza kuwa? E. Alal misali, wasu ’yan kimiyya sun ce hasashe na ra’ayin bayyanuwa da kuma bincike-binciken ’yan kimiyya a wasu fannonin ilimi sun nuna cewa a yau babu amfani a yi imani da Allah, domin za a iya bayyana yadda dukan abubuwa suke aukuwa. Ya kamata irin waɗannan furcin fahariya su dame mu ne? Ko kaɗan! Domin hikimar ’yan adam ta bambanta da ta Allah. (1 Kor. 2:6, 7) Amma, mun sani cewa sa’ad da hikimar ’yan adam ta saɓawa hikimar Allah, a koyaushe hikimar ’yan adam ce ba daidai ba. (Ka karanta Romawa 3:4.) Duk da ci gaba na ’yan kimiyya a wasu fannonin ilimi, abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da hikimar ’yan adam ya ci gaba da kasancewa gaskiya: “Hikimar wannan duniya wauta ce ga Allah.” Idan aka kwatanta da hikimar Allah marar iyaka, hikimar ’yan adam banza ne. —1 Kor. 3:18-20.

17. Yaya ya kamata mu ɗauki kalaman shugabannin Kiristendam da na ’yan ridda?

17 Wani misali kuma na kalaman banza shi ne abubuwan da shugabannin addini na Kiristendam suke furtawa. Waɗannan suna da’awar cewa suna magana a cikin sunan Allah, amma yawancin abubuwan da suke furtawa ba su jitu da Nassi ba, kuma abin da suke cewa banza ne. ’Yan ridda ma suna furta kalaman banza, suna da’awar cewa suna da hikima sosai fiye da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” da aka naɗa. (Mat. 24:45-47) Amma, ’yan ridda suna furta na su hikimar, kuma kalamansu duk banza ne, suna hana wasu sauraro. (Luk 17:1, 2) Ta yaya za mu guje wa rinjayar su?

Yadda Za a Guji Kalaman Banza

18. Ta yaya za mu iya amfani da abin da ke 1 Yoh. 4:1?

18 Manzo Yohanna ya ba da shawara mai kyau game da wannan batu. (Ka karanta 1 Yohanna 4:1.) Bisa ga shawarar Yohanna, muna ƙarfafa waɗanda muke wa wa’azi su gwada abin da suka koya da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan ka’ida ma zai iya taimakonmu. Idan muka ji wata baƙar magana game da gaskiya ko kuma da ta ɓata sunan ikilisiya ko dattawa, ko kuma wani ɗan’uwanmu, kada mu yarda da abin da aka ce ba tare da yin bincike ba. Maimakon haka, ya kamata mu tambayi kanmu: “Mutumin da yake yaɗa wannan labarin yana yin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce? Irin waɗannan labaran ko zargin suna ɗaukaka nufin Jehobah ne? Suna kawo salama a cikin ikilisiya ne?” Duk abin da muka ji da zai rushe yan’uwancinmu maimakon ya gina su, banza ne.—2 Kor. 13:10, 11.

19. Ta yaya ne dattawa suke mai da hankali don kada kalamansu su kasance banza?

19 Idan ya zo ga kalaman banza, dattawa ma sun koyi darussa masu muhimmanci. A duk lokacin da za su ba da gargaɗi, su tuna kasawarsu kuma kada su ba da gargaɗi kawai daga ilimi da suke da shi. Amma su yi amfani da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Manzo Bulus ya yi gargaɗi sa’ad da ya ce: “Kada a zarce abin da an rubuta.” (1 Kor. 4:6) Dattawa ba sa zarce abin da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki. Kuma ba sa zarce shawarar da bawan nan mai aminci mai hikima ya rubuta a cikin littattafan da ke bisa Littafi Mai Tsarki.

20. A waɗanne hanyoyi ne ake taimakonmu mu guje wa ayyukan banza?

20 Abubuwan banza ko “allahn” ƙarya ne, ko kalamai, ko kuma wasu abubuwa duka suna da la’ani ƙwarai. Saboda haka, a koyaushe ya kamata mu yi addu’a mu roƙi Jehobah ya taimake mu don mu gane waɗannan ayyukan banza, ya kuma nuna mana yadda za mu guje su. Idan muka yi haka, za mu kasance da irin wannan ra’ayi kamar na mai zabura: “Ka kawasda idanuna ga barin duban abin banza, Kuma ka rayadda ni cikin tafarkunka.” (Zab. 119:37) A talifi na gaba, za mu tattauna muhimmancin yin amfani da shawarar Jehobah.

Za Ka Iya Bayani?

• Waɗanne ‘ayyukan banza’ ne ya kamata mu guje su?

• Ta yaya za mu guji barin kuɗi ya zama allahnmu?

• Ta yaya ne sha’awar abubuwa na jiki za ta iya zama bautar gunki?

• Ta yaya za mu guji kalaman banza?

[Hoto a shafi na 3]

An ƙarfafa Isra’ilawa su ‘nome gonarsu,’ kada su biɗi abubuwan banza

[Hoto a shafi na 5]

Kada ka bari sha’awar abin duniya ta sa ka yi sanyi a hidimar Jehobah

[Hoto a shafi na 6]

Kalaman dattawa za su iya taimako sosai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba