Ka Kasance Mai Sauƙin Hali A hanyar Da Ta Dace
‘Ka tuna musu . . . su kasance masu [sauƙin] hali.’—TITUS 3:1, 2.
1, 2. Menene Nassosi ya ce game da sauƙin hali, kuma me ya sa hakan ya dace?
JEHOBAH, Ubanmu mai ƙauna na samaniya, yana da hikima sosai. Muna bukatar ja-gorarsa a rayuwarmu domin shi ne Mahaliccinmu. (Zab. 48:14) Almajiri Yaƙub ya gaya mana cewa “hikima mai-fitowa daga bisa tsatsarka ce dafari, bayan wannan mai-salama ce, mai-sauƙin hali, mai-siyasa, cike da jinƙai da kyawawan ’ya’ya, mara-kokanto, mara-riya ce.”—Yaƙ. 3:17.
2 “Ku bari jimrewarku [“sauƙin hali”] ta sanu ga dukan mutane,” in ji manzo Bulus.a (Filib. 4:5) Yesu Kristi shi ne Ubangiji da kuma Shugaban ikilisiyar Kirista. (Afis. 5:23) Yana da muhimmanci kowanenmu ya kasance da sauƙin hali, mu zama masu bin ja-gorar Kristi kuma mu zama masu nuna sanin ya kamata a yadda muke bi da sauran mutane!
3, 4. (a) Ka kwatanta amfanin da za mu samu idan muka nuna sauƙin hali. (b) Menene za mu tattauna?
3 Za mu amfana idan muka nuna sauƙin hali yadda ya kamata. Alal misali: Bayan da aka gano wata maƙarƙashiyar da ’yan ta’adda suka ƙulla a ƙasar Britaniya, dukan fasinjojin da suke son su shiga jirgin sama sun bi umurnin da aka bayar na hana shiga cikin jirgi da kayan da ake bari a shiga da su a dā. Sa’ad da muke tuƙa mota, mu kan ƙyale wasu direbobi su wuce, musamman a rawul, don guje wa haɗari da kuma cunkushewar motoci.
4 Ga yawancinmu, nuna sauƙin hali ba shi da sauƙi. Don samun taimako, bari mu tattauna fasaloli guda uku na nuna sauƙin hali, wato, a tunaninmu, a halinmu ga masu iko, da kuma yawan sauƙin halin da za mu iya nunawa.
Me Ya Sa Ya Kamata Mu Zama Masu Sauƙin Hali?
5. A ƙarƙashin Dokar Musa, mecece za ta motsa bawa ya ci gaba da zama da ubangidansa?
5 Wani misalin da aka ɗauko kafin lokacin Kiristoci ya mai da hankali a kan kasancewa mai sauƙin hali da ra’ayin da ya dace. A ƙarƙashin Dokar Musa, ana ’yanta Ibraniyawan da suka zama bayi a shekararsu ta bakwai na yin bauta ko kuwa a shekarar ’Yanci. Amma bawan yana iya zaɓan cewa zai ci gaba da zama bawa. (Ka karanta Fitowa 21:5, 6.) Menene zai sa bawa ya yi hakan? Ƙauna ce ta motsa bawan ya ci gaba da kasancewa cikin irin wannan yanayin, wato, a ƙarƙashin ikon ubangidansa mai sanin ya kamata.
6. Ta yaya ne ƙauna za ta motsa mu mu nuna sauƙin hali?
6 Hakazalika, ƙaunar da muke yi wa Jehobah ce ta motsa mu mu keɓe masa rayuwarmu kuma mu yi rayuwar da ta jitu da keɓewar da muka yi. (Rom. 14:7, 8) “Gama ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba,” in ji manzo Yohanna. (1 Yoh. 5:3) Wannan ƙaunar ba ta biɗar abin kanta. (1 Kor. 13:4, 5) Sa’ad da muke hulɗa da mutane, ƙaunar da muke musu za ta motsa mu mu nuna sauƙin hali kuma mu saka bukatunsu a gaban namu. Maimakon mu nuna son kai, za mu saka bukatun wasu a gaban namu.—Filib. 2:2, 3.
7. Menene kasancewa masu sauƙin hali zai sa mu yi a hidimarmu?
7 Bai kamata furcinmu da halayenmu su sa wasu tuntuɓe ba. (Afis. 4:29) Hakika, ƙauna za ta motsa mu mu guje wa yin duk wani abin da zai hana mutane daga ko’ina su bauta wa Jehobah ba. Hakan ya ƙunshi kasancewa da sauƙin hali. Alal misali, ’yan’uwa mata masu wa’azi a ƙasashen waje da suka saba yin ado sosai ba za su nace ba cewa za su yi hakan a wuraren da hakan zai iya sa a ɗauke su ’yan iska kuma su sa mutane tuntuɓe.—1 Kor. 10:31-33.
8. Ta yaya ne ƙaunar da muke yi wa Allah za ta taimaka mana mu ɗauki kanmu a matsayin ‘ƙanƙanana’?
8 Ƙaunar da muke yi wa Jehobah tana taimaka mana mu guji yin fahariya. Bayan almajiransa sun yi gardamar wanda ya fi matsayi a cikinsu, Yesu ya kawo wani ɗan ƙaramin yaro ya tsayar da shi a tsakaninsu. Sai ya ce: “Dukan wanda ya karɓi ɗan ƙaramin yaron nan a cikin sunana, ni ya ke karɓa: kuma dukan wanda ya karɓe ni, yana karɓan wanda ya aiko ni: gama wanda shi ke ƙanƙani a cikinku duka, shi ne babba.” (Luka 9:48; Mar. 9:36) Ɗaukan kanmu a matsayin ‘ƙanƙanana’ zai iya yi mana wuya. Ajizancin da muka gāda da kuma son yin fahariya zai iya sa mu nemi matsayi, amma tawali’u zai taimaka mana mu nuna sauƙin hali kuma mu daraja wasu.—Rom. 12:10.
9. Menene ya kamata mu sani don mu kasance masu sauƙin hali?
9 Idan muna son mu zama masu sauƙin hali, dole ne mu yi la’akari da ikon waɗanda Allah ya naɗa. Dukan Kiristoci na gaskiya sun san mizani mai muhimmanci na shugabanci. Manzo Bulus ya bayyana hakan dalla-dalla ga Korinthiyawa: “Ina so ku sani, kan kowane namiji Kristi ne; kan mace kuma namiji ne; kan Kristi kuma Allah ne.”—1 Kor. 11:3.
10. Miƙa wuya ga ikon Jehobah zai nuna menene?
10 Yin biyayya ga ikon Allah zai nuna cewa mun dogara gare shi a matsayin Ubanmu mai ƙauna. Yana sane da dukan abubuwan da ke faruwa kuma zai albarkace mu yadda ya kamata. Sanin hakan zai taimaka mana a lokacin da mutane suka ƙi daraja mu ko kuwa a lokacin da suka yi fushi sosai. Bulus ya rubuta: “Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku.” Bulus ya nanata muhimmancin wannan shawarar da waɗannan batutuwan da ke gaba: “Kada ku ɗauka ma kanku fansa, ƙaunatattu, amma ku kauce ma fushi: gama an rubuta, Ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.”—Rom. 12:18, 19.
11. Ta yaya za mu nuna cewa muna bin shugabancin Kristi?
11 Wani abu kuma da za mu daraja shi ne hurarren ikon da ke cikin ikilisiyar Kirista. Ru’ya ta Yohanna sura ta ɗaya ta kwatanta cewa Yesu Kristi yana riƙe da “taurari” na ikilisiya a hannunsa na dama. (R. Yoh. 1:16, 20) Gabaki ɗaya, waɗannan ‘taurarin’ suna wakiltan rukunin dattawa, ko kuwa masu kula da ke cikin ikilisiyoyi. Waɗannan masu kula da aka naɗa suna bin shugabancin Kristi kuma suna yin koyi da hanya mai kyau da yake bi da mutane. Dukan waɗanda suke cikin ikilisiya suna bin tsarin da Yesu ya kafa na yin tanadin abinci na ruhaniya a kan kari ta hanyar “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Mat. 24:45-47) A yau, son yin nazari da kuma yin amfani da abubuwan da aka rubuta a cikin waɗannan littattafan zai nuna cewa kowannenmu na miƙa wuya ga shugabancin Kristi, kuma hakan zai sa a ƙara samun salama da haɗin kai.—Rom. 14:13, 19.
Menene Yawan Sauƙin Halin da Za Mu Nuna?
12. Me ya sa kasancewa da sauƙin hali yana da iyaka?
12 Nuna sauƙin hali ba ya nufin cewa za mu ƙarya bangaskiyarmu ko mizanan Allah. Wane mataki ne Kiristoci na ƙarni na farko suka ɗauka sa’ad da shugabannin addinai suka umurce su su daina koyarwa bisa sunan Yesu? Bitrus da sauran manzannin suka ce da gaba gaɗi: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.” (A. M. 4:18-20; 5:28, 29) Shi ya sa a yau, sa’ad da hukumomi suka nemi su tilasta mana mu daina yin wa’azin bishara, ba ma dainawa, ko da yake muna iya canja salon yin wa’azin don mu bi da yanayin cikin dabara. Idan aka hana yin wa’azi na gida-gida, muna iya neman wasu hanyoyin tattaunawa da masu gida kuma mu ci gaba da bin umurnin da Allah ya ba mu. Hakazalika, sa’ad da “mahukunta” suka hana mu yin taro, muna taruwa a ɓoye a ƙananan rukunoni.—Rom. 13:1; Ibran. 10:24, 25.
13. Menene Yesu ya ce game da nuna sauƙin hali ga masu iko?
13 A Huɗubarsa Bisa Dutse, Yesu ya ambata muhimmancin nuna sauƙin hali ga masu iko: “Idan kuma wani yana so ya kai ka shari’a, shi karɓe maka rigarka, bar masa mayafinka kuma. Kuma dukan wanda ya tilasta maka tafiya mile ɗaya, tafi tare da shi har biyu.” (Mat. 5:40, 41)b Nuna kula ga mutane da son taimaka masu zai motsa mu mu yi musu fiye da abin da suke bukata.—1 Kor. 13:5; Tit. 3:1, 2.
14. Me ya sa ba za mu nuna sauƙin hali ga ’yan ridda ba?
14 Kada mu yarda ra’ayinmu na son kasancewa masu sauƙin hali ya sa mu amince da ’yan ridda. Muna bukatar mu ɗauki wannan matakin don kāre gaskiya da kuma haɗin kan ikilisiya. Game da ‘’yan’uwan ƙarya,’ Bulus ya rubuta: “Mu kuwa ba mu zauɗa masu ba, ba mu yi biyayya da su ba, ko da sa’a ɗaya; domin gaskiyar bishara ta wanzu a wurinku.” (Gal. 2:4, 5) Idan ma wasu suka zama ’yan ridda, Kiristoci na gaskiya za su manne wa gaskiya.
Masu Kula Suna Bukatar Su Kasance Masu Sauƙin Hali
15. Ta wace hanya ce Kiristoci masu kula za su iya nuna sauƙin hali a lokacin da suke taro?
15 Ɗaya a cikin abubuwan da ke sa mutum ya cancanci yin hidima a matsayin mai kula shi ne kasancewa mai sauƙin hali. Bulus ya rubuta: “Mai kula da ikilisiya yā zama . . . salihi [“mai sauƙin hali”].” (1 Tim. 3:2, 3) Wannan na da muhimmanci musamman sa’ad da mazan da aka naɗa suka taru don su tattauna batutuwan da suka shafi ikilisiya. Kafin a yanke shawara, dukan waɗanda suka taru suna da ’yancin faɗin ra’ayinsu, ko da yake ba dole ba ne dukan dattawan su yi kalami ba. A lokacin da suke tattaunawa, ra’ayin mutum na iya canjawa a lokacin da sauran suka ambata mizanan da ke cikin Nassi da suka shafi batun. Maimakon ya manne wa nasa ra’ayin, ƙwararren dattijo zai nuna sauƙin hali. Sa’ad da suka soma tattaunawa, wataƙila kowannensu na da nasa ra’ayin, amma yin tunani tare da addu’a zai ɗaukaka haɗin kai a tsakanin dattawa masu filako da sauƙin hali.—1 Kor. 1:10; Ka karanta Afisawa 4:1-3.
16. Wane irin hali ne Kirista mai kula zai nuna?
16 A dukan ayyukansa, dole ne dattijo Kirista ya manne wa tsarin Allah. Ya kamata wannan halin ya bayyana har ma a lokacin da yake kula da tumaki, wanda hakan zai taimaka masa ya nuna sanin ya kamata kuma ya bi da mutane a hankali. “Ku yi kiwon garken Allah wanda ke wurinku,” in ji Bitrus, “kuna yin shugabanci, ba kamar na tilas ba, amma da yardan rai, bisa ga nufin Allah; ba kuwa domin riba mai-ƙazanta, amma da karsashin zuciya.”—1 Bit. 5:2.
17. Ta yaya ne dukan waɗanda suke cikin ikilisiya za su iya nuna sauƙin hali wajen bi da mutane?
17 Tsofaffin da ke cikin ikilisiya suna yaba wa taimakon da matasa suke yi kuma suna daraja su. Su ma matasa suna daraja tsofaffin da suka daɗe suna bauta wa Jehobah. (1 Tim. 5:1, 2) Dattawa Kiristoci suna neman mazan da suka ƙware waɗanda za su iya ba hakkoki, kuma suna koyar da su don su kula da tumakin Allah. (2 Tim. 2:1, 2) Kowane Kirista yana bukatar ya ɗauki hurarriyar shawarar Bulus da muhimmanci: “Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabannanku, ku sarayadda kanku garesu [“nuna sauƙin hali”]: gama suna yin tsaro sabili da rayukanku, kamar waɗanda za su amsa tambaya; su yi shi da farinciki, ba da baƙinciki ba: gama wannan mara-anfani ne gareku.”—Ibran. 13:17.
Nuna Sauƙin Hali a Cikin Iyali
18. Me ya sa nuna sauƙin hali yake da muhimmanci a cikin iyali?
18 Iyali tana bukatar ta nuna sauƙin hali. (Ka karanta Kolossiyawa 3:18-21.) Littafi Mai Tsarki ya ambata matsayin dukan waɗanda suke cikin iyalin Kirista. Uba shi ne shugaban matarsa kuma shi ne ke da ainihin hakkin yi wa yaransa ja-gora. Matar tana bukatar ta yi iyaka ƙoƙarinta ta amince da ikon mijinta, su ma yara suna bukatar su yi iya ƙoƙarinsu su yi biyayya, wannan shi ne tafarkin da Ubangiji yake so. Dukan waɗanda suke cikin iyali suna iya daɗa haɗin kai da salamar da ke cikin iyali ta wajen nuna sauƙin hali yadda ya kamata. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da wasu misalan da za su taimaka wajen kwatanta wannan bayanin.
19, 20. (a) Ka nuna bambancin da ke tsakanin Eli da Jehobah game da nuna sauƙin hali. (b) Waɗanne darussa ne iyaye za su iya koya daga waɗannan misalan?
19 Eli ne babban firist ɗin Isra’ila sa’ad da Sama’ila yake ɗan ƙaramin yaro. Amma yaran Eli, Hophni da Finehas “ba su da kirki” kuma “ba su kula da Ubangiji ba.” Eli ya ji labarai marar kyau game da abubuwan da suke yi, har da lalatar da suke yi da matan da suke hidima a ƙofar tantin taro. Menene ya yi? Eli ya gaya masu cewa idan Jehobah ne suka yi wa zunubi, babu wanda zai yi musu addu’a. Amma ya ƙi ya daidaita su da kuma horanta su. A sakamakon haka, ’ya’yan Eli suka ci gaba da yin zunubi. A ƙarshe, Jehobah ya yanke hukunci cewa sun cancanci su mutu. Sa’ad da ya ji labarin mutuwarsu, sai Eli ya faɗi ya mutu. Wannan sakamako ne marar kyau! Babu shakka, sauƙin halin da Eli ya nuna domin ayyukan muguntar da suke yi bai dace ba, domin ya ƙyale su su ci gaba da yin zunubi.—1 Sam. 2:12-17, 22-25, 34, 35; 4:17, 18.
20 Akasarin haka, yi la’akari da yadda Allah ya bi da ’ya’yansa mala’iku. Annabi Mikaiya ya ga wani wahayi mai ban sha’awa na taron Jehobah da mala’ikunsa. Jehobah ya tambayi mala’ikun ko akwai wani a cikinsu da zai iya ruɗar Sarki Ahab na Isra’ila don wannan mugun sarkin ya mutu. Jehobah ya saurari shawarwari dabam dabam na ’ya’yansa na ruhu. Sai wani cikin mala’ikun ya ce zai iya. Jehobah ya tambaye shi abin da zai yi. Da ya gamsu, Jehobah ya umurci mala’ikan ya je ya cika aikin. (1 Sar. 22:19-23) Ya kamata waɗanda suke cikin iyali su koyi nuna sauƙin hali daga wannan labarin. Zai dace maigida Kirista kuma uba ya yi la’akari da ra’ayoyi da kuma shawarwarin matarsa da yaransa. Su kuma mata da yara suna bukatar su san cewa idan suka faɗi ra’ayinsu ko kuwa abin da suka fi so, suna bukatar su nuna sauƙin hali ta wajen bin shawarar da maigida ya yanke domin shi ne Nassi ya ba ikon yin hakan.
21. Menene za a tattauna a talifi na gaba?
21 Muna godiya sosai domin waɗannan tunasarwa na Jehobah da suke cike da ƙauna da hikima game da nuna sauƙin hali! (Zab. 119:99) Talifinmu na gaba zai tattauna yadda nuna sauƙin hali yadda ya dace zai sa a sami farin ciki a cikin aure.
[Hasiya]
a Kalmar da manzo Bulus ya yi amfani da ita a nan an fassara ta “laushin hali [“sauƙin hali”]” a cikin Littafi Mai-Tsarki. Amma wata majiya ta ce: “Sauƙin hali ya ƙunshi nuna sanin ya kamata da haƙuri ga mutane da kuma ƙin nace wa ’yancinmu.” Saboda haka, kalmar tana nufin nuna sauƙin kai da sanin ya kamata, ban da nacewa wajen bin doka ko kuwa neman hakkinmu.
b Ka duba talifin nan “If You Are Impressed Into Service,” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu, 2005, shafuffuka na 23-26 na Turanci.
Mecece Amsarka?
• Wane sakamako mai kyau ne nuna sauƙin hali zai kawo?
• Ta yaya ne masu kula za su nuna sauƙin hali?
• Me ya sa nuna sauƙin hali yake da muhimmanci a cikin rayuwar iyali?
[Hoto a shafi na 4]
Dattawa ku bi misalin Kristi na yadda yake bi da mutane a hanya mai kyau
[Hoto a shafi na 6]
Sa’ad da dattawan ikilisiya suka taru, yin tunani da ke bisa addu’a da kuma nuna sauƙin hali zai ɗaukaka haɗin kai