Manufar Talifofin Nazari
Talifofin Nazari na 1, 2 SHAFUFFUKA NA 3-11
Akasin ra’ayi da halayen yawancin mutane, Kiristoci suna da dalilai masu kyau da zai sa su ci gaba da kasancewa masu sauƙin hali. Menene waɗannan dalilan? Kuma ta yaya za ka iya nuna sauƙin hali a aurenka?
Talifin Nazari na 3 SHAFUFFUKA NA 12-16
Me ya sa za mu tabbata cewa Jehobah yana ji addu’armu kuma yana damuwa sa’ad da muka kai kukanmu a gare shi? Wannan talifin ya amsa wannan tambayar kuma ya nuna yadda za mu iya jimre jarrabbobi.
Talifofin Nazari na 4, 5 SHAFUFFUKA NA 21-29
Waɗannan talifofin guda biyu za su taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da mutane, kuma mu guji kasancewa masu sūka. Kuma za mu ga bambancin da ke tsakanin wanda yake da hikima da gaske da kuma marar hikima.